Hibba
Dariya da naketa ji ana mun cikin kunne ne ya farkar dani daga baccin da nakeyi hade da iska ana hura mun a fuska, duk da ban gama bude idauna ba, already nasan wanda yake mun wanan aika aikan, inda sabo na rigada na saba yanzu da irin tashina daga naccin da akeyi.
Murmushi na sake ina kokarin bude idanuna nace "Faheema..."
"Anty Hibba ina kwana" ta fa'da tana dariya cike da jin dadin ganin ta samu nasarar farkar dani.
"Anty Hibba ki tashi! Kin manta daddy zai fita damu yau! Wayyo I'm so excited! Please wake up!"
Sai faman murna take tana mun tsalle akan gado. Daman tun ran dana fara shigowa gidan nan bacci ne kawai ke raba mu da Faheema, wani sa'in har sneaking takeyi ta shigo dakin mu kwana tare, sai dai na farka cikin dare naga ta kudundune kuda dani tana sharan baccinta.
Na tuna ranar da muka dawo gidan bayan dramar dana yiwa Hassan akan hanya, muna barin hall din straight gida muka taho, a ranar wani irin tarba na musaman na samu wurin Faheema wanda ba ta'ba mun ba a rayuwa. Muna tsaye a bakin kofa na shiga cikin mansion din ina kallon yanda Hassan yake rungume da diyarsa, yana sumbatar cute face dinta, ban ta'ba ganinsa cikin irin wanan yanayin ba so carefree, idan yana tare da Faheema gabadaya canzawa yakeyi kamar bashi ba, his expressions is always filled with love, loyalty and deep affection for her. Ina tsaye ina kallonsu har ta gama masa oyoyo sa'anan ta dawo da hankalinta gareni tana dubana, sai data tabbatar da ni din ce tsaye a gabanta naga ta kwaso a guje tazo ta fa'da a jikina, rungumeni tsam tayi a jikinta tamkar taga uwarta data ba'ta.
A lokacin naji zuciyata tayi mun wani irin dumm...hade da dan bugawa da karfi karfi, ban san sanda nima na kara janyota jikina ba na rungumeta tsam ina ajiyar numfashi, zuciyata tayi relax, na lumshe ido ina rungume da ita kamar karna saketa nakeji a wanan lokacin. Ban ta'ba jin yaro ya shiga raina faral da'ya haka ba, don tunda nake babu wani yaron daya ta'ba kusanci dani haka, kilan shiyasa naji Faheema ta shige mun faral da'ya.
A hankali ta da'go sai faman kyalkyalewa da dariya take cike da murna tana fa'din "oyoyo Anty Hibba, finally Daddy ya kawo mun ke gida! I'm so happy...."
A hankali ta juyo tana duban Daddyn nata dake tsaye a gefe yana kallon mu tace dashi "nagode Daddy!"
Murmushi ya sakar mata cike da so da kauna yace "you're welcome sweetheart" yanda suke exchanging kallo shi da diyarsa tamkar ni wata sabuwar kyauta ce da aka kawo mata cikin leda.
Ba tare da ba'ta lokaci ba naji ta kamo hannuna cikin yan mitsi mitsin nata tana jana "taho muje Anty Hibba... yau zamu dafa biscuit da miyan nan da kika ta'ba turo mun, shi zamu ci a dinner yau"
Yanda take jana har ina neman losing balance din nayi saurin kama kaina ga magunanta guda biyu Alfan da Kian na biye damu a baya. Cikin sauri na juyo ina duban Hassan hankalina a tashe ina neman doki daga garesa amma shi ko ajikinsa murmushi kawai naga ya sakar mun yana kallonmu har Faheema ta jani muka shige ciki, na fara bin ko ina da kallo, gida tamkar aljannah duniya, na soma tuna ranar dana fara shigowa gidan da irin tsoro da farga dana shigo da ciki. Ina wanan tunanin Faheema na jana har muka shigo cikin main Parlour, wani irin sanyayen kamshi ne ke tashi daga ko ina,
"Faheema ina kika sa....." sauran maganar ne ya mutu a bakin mai maganar muka juyo cikin sauri nida Faheema muka ga Maryam tsaye sanye cikin atamfa riga da skirt, tayi kyau sosai fuskarta tasha makeup, doguwa ce, jikinta dan daidai fatar jikinta brown kana ganinta kasan tana kula da kanta sosai. Kallonmu kawai takeyi da mamaki rubuce karara a fuskarta, ta kalleni ta kalli Faheema. Nan take naga ta ba'ta fuska. A hankali ta soma takowa har inda muke tana bina da kallo sama da kasa ta yatsine fuska kamar taga kashi, nan take nasha jinin jikina, daman tun farkon haduwarmu jikina ya bani wanan matar ba sona takeyi ba, bata kaunata.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...