Hibba
A gurguje na karaso bakin gate, chief security officer na gidan Mr John yazo ya tare ni ganin na karaso cikin sauri, cike da damuwa ya tambayeni "Madam are you going somewhere?"
Na gyada mishi kai "please I want to quickly get something outside"
"Kona ha'da ki da wasu daga cikin security su rakaki? It's Mr Sooraj order"
Cikin sauri na girgiza masa kaina nace "no Mr John, ba sai an rakani ba yanzu zanje na dawo bazan jima ba"
Shiru yayi yana nazari kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ba don yaso ba yace mun toh shikenan yasa aka bude mun gate, ina sa kafana a waje naji wani irin sanyi ya ratsani tsigar jikina duk suka mimike amma still ban karaya ba na soma tafiya cikin sauri sauri, sai faman dialing number da Ammar ya turo mun da sako nakeyi amma bata shiga hankalina ya kuma tashi, nayi tunanin ko na kira Hassan na fa'da mishi sai kuma na canza mind dina, bansan wani hali Ammar yake ciki ba in har zai ce mun kar na sanar da kowa na taho ni kadai, kirjina sai faman bugawa da karfi yakeyi ina addu'a Allah yasa yana lafiya. Har can kasan layin na karasa da kafa tukuna na samu abun hawa na tsayar da nace mishi ya kaini bakin gate. Within 6 minutes na sauka a bakin gate na tsayar da kananan motoci masu tafiya, ya tambayeni ina zanje nace mishi Ijora yace na hau mu tafi, ina shiga ciki na sake ciro waya ina cigaba da dialing still bata tafiya, nayi saurin rubuta mishi text nace mishi ya jira gani nan zuwa, can naga ya sake turo mun da sako yace idan na isa Ijora bustop na shigo layin Fatai Irawo, kaina ya daure meyasa baya daukan wayata sai dai ya turo mun text? Wata zuciyar tace dani kilan yana cikin mutane ne yana kafa kafa baya son a sani.
Tafiyar 15 mins mukayi daga Ikoyi zuwa 3rd mainland, Munata tafiya dai har muka sauko daga kan gadan da zai sada mu da Iddo, yamma ya gabato sosai na duba lokaci naga ana neman shida da rabi, gari ya soma duhu, daidai Ijora bustop driver ya kaini yace mun iso nace mishi mu karasa Fatai Irawo, yace bai san wurin ba amma sai dai a tambaya, wasu mutane masu wucewa ya tsayar yana tamabayarsu layin suka mishi kwatance yayi musu godiya sa'anan ya tada mota muka shiga cikin unguwar, can kasa ya kaimu, unguwar sai a hankali hanyar duk babu kyau ga wari dake tashi saboda shara da ake zubarwa kota ina, har wani jiri nake gani amma haka na jure na toshe hancina muka karasa ciki, daidai bakin wani lungu ya ajiyeni yace nan ne Fatai Irawo, na kalli lungun babu mutane, wani irin faduwar gaba ne ya ziyarce ni, kirjina na harbawa na tambayeshi nawa ne kudinsa yace mun dubu daya nace toh nasa hannu cikin jaka na mika masa sa'anan na fito jikina na bari na soma rubuta text na turawa Ammar nace masa gani nan na iso yana ina, shiru banji an mun reply ba hankalina ya kara tashi, jikina sai kyarma yakeyi ina sake da warwara cikin zuciyata. Nafi 5 minutes ina tsaye a wajen har zan sake tura wani text naga wata mota ta saho kai tazo tayi parking daidai bakin lungun, kafun kace me naga mutum ya fito daga cikin motar kamar walkiya yazo ya tsaya a gabana, freeze nayi don in my wildest dreams ban ta'ba tunanin zan sake daura idanuna a kansa ba, numfashina ya tsaya cak na huccin gadi, a gigice nake binsa da kallo don ganin abun nake kamar a mafarki ganinsa tsaye a gabana, mutumin da har duniya ta na'de bana fata ko mafarkin Allah ya sake ha'dani dashi, koda da tsautsayi, mutumin daya ci mutuncina yaci zarafina tun ina karama, mutumin da........
Wani irin tafarfasa naji zuciyata kemun, a hankali ya soma takowa bai karaso inda nake yaja ya tsaya "wow Hibbata kenan, ashe da rabon zan sake daura idanuna kan wanan kyakyawar fuskar taki, kinga yanda kika kara kyau kuwa" ya fada yana bin jikina da kallo yana lashe lips dinsa.
Baya baya na soma yi zuciyata na bugawa kamar zata fasa kirjina ta fito nace "karka kuskura ka matso kusa dani macuci kawai azalumi! Ina Ammar yake?!"
Cak ya tsaya yana bina da kallo na yan sekoni daga bisani ya bushe da wata irin dariya kamar wani mai tabon hankali sai da yayi mai isansa tukuna ya soma girgiza kai "Hibba Hibbatullah kenan.... har yanzu da sauran ki, wato a tunaninki Ammar ne ya turo miki wanan text din shiyasa kika zo da ba'rin jiki? Daman na sani, nasan ta wanan hanyar ne kadai zan iya samu kizo gareni, kowa yasan irin son da kike yiwa Ammar, akansa zaki iya yin komai, you can risk anything, toh ba Ammar bane ni ne nan nake nemanki"
Zaro ido nayi jin abunda ya fadi, sai a lokacin na fahimci abunda yake nufi, innalillahi wa ina illahi raji'un, wato shi ya turo mun da text din yayi pretending kamar Ammar? Ina ya samu numberta? Ya akayi yasan inda nake? Tambayoyin da suka shiga mun yawo aka kenan ban samu ansa ba, sai yanzu nayi realizing wautana tana fito kai tsaye daga gida ba tare da na tsaya nayi tunani ba, I've made a big mistake. Maganarsa ne ya katse mun tunani inda yake fadin "kina tunanin bayan wanan shekarun da aka dauka zan iya mantawa dake ne? No it's not possible Hibba, ke tawace har abada, har duniya ta na'de bazan ta'ba barinki kiyi rayuwa babu ni ba, yanzu kuma lokaci yayi daya kamata ki dawo gareni, kizo Hibba mu koma Maiduguri ki zauna tare dani, zan baki duk wata kulawa da kike bukata, zan baki ingantacen rayuwa fiye ga wanan da kike ciki kinji" ya fada maganar cikin sigar rarashi yana kokarin karasowa inda nake.
"Na gaya maka karka matso kusa dani! Babu inda zan bika, ka kyaleni, ka fita daga rayuwata!" Na fada a tsawace na juya a kidime ina neman hanyar guduwa naji ya karaso cikin sauri zai kamoni, haba kafun ya kai hannunsa jikina na juyo a zuciye da dukan karfina na kai mishi naushi a gefen fuska, wayar da nake rike da ita a hannu ta sameshi a fuska, baya baya yayi yana neman faduwa don ba karamin impact wayar tayi masa a fuska ba, dafe gefen fuskar yayi yana zundumo ashar daga bakinsa, don baiyi expecting hakan daga gareni ba, kafun kace me na karawa kafata wuta, gudu nake sosai da dukan karfina har ina tuntube saboda duwatsu dake hanyar lungun, har na kawo daidai karshen lungun zanyi kwana naji an fizgoni ta baya, na bude baki zansa ihu yasa tafin hannunsa ya toshe bakina, kokuwa na soma yi dashi kamar wata zarariya ina kokarin kwace kaina, duk inda hannuna yaci karo dashi ina kokarin na yaga da farcena, ganin inata faman masa gardama za'a iya bullowa a ganmu yasa ya kara matseni a jikinsa, unexpectedly naji saukan naushi daya sa numfashina kakegwa wani irin duhu ne ya ziyarceni lokaci guda na fadi a wajen, wayata da nake rike da ita ta silale daga hannuna, wani irin zafin radadi naji yan ratsa fuskata, kaina ya soma juyawa na soma ganin dishi dishi ina kwance a wajen, nasan idan banyi kokarin nayi clearing kaina ba komai zai iya faruwa dani a wajen tunda babu mai kawo mun doki, lungun shiru babu mai giftawa, da kyar nasa hannu na soma kokarin lalubar wayata naji muryarsa yana fa'din "wai meyasa kikeda taurin kai ne haka Hibba? Zuwa fa nayi na dauke ki mu koma gida salin alin kike mun wanan gadammar, kinsan yanda nayi missing dinki kuwa?"
Rintse idanuna nayi ina kokarin forcing kaina yayi clearing, cikin sa'a kuwa nayi na samu na bude idanuna na hango wayar tawa kwance a can a gefe, cikin sauri na mike na rarafa naje na dauko ba tare da ba'ta lokaci ba na soma lalubar number Hassan, zan dana dialing kenan naji yasa kafa yayi kicking wayar daga hannuna, yar kara na sake hawaye zuka ciciko mun idanu, "wayyo Allahna..Hassan...Hassan" na fada ina sheshekar kuka, shi kadai nakeda sa ran zai iya zuwa ya ceceni a wanan wajen.
Ba tare da ba'ta lokaci ba naji an fizgoni daga kasan da nake kwance, yasa wani tsuma ya toshe mun bakina da hanci, kokuwa na soma yi ina kokarin nayi numfashi at the same time ina kokarin na kwace kaina daga hannunsa, sai dai duk yanda nayi na kasa don kawu Abu yayi kusan ukuna a girma inma bai fi ba don yanada jiki. Tsuman dayasa ya toshe hancina wani irin warin chemical yakeyi, a hankali senses dina ya soma barin jikina, jikina ya soma weak, ina kokarin fighting amma inaaa, abunda nake shaka cikin wanan tsumar yasa nayi weak sosai nan take na soma jin wani irin bacci mai nauyi na neman fizgata duk yanda nayi na farka naji na kasa. Haka ina ji ina gani na kasa koda kwakwaran motsi a hannunsa, ban sake sanin inda kaina yake ba.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Roman d'amourHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...