Chapter 106

1K 59 0
                                    


Tun daga ranar da abun nan ya faru, Hibba bata sake jin duriyar Afrah ba, an shafi wata da'ya wata biyu har uku, ko labarinta bata kuma ji ba, har ta soma feeling relaxed but deep down she's still a bit worried, Hassan bai dauko mata batun ita kuma ba abun ta tambayeshi ba, haka suka cigaba da zamansu hankali kwance, ranar kwatsam sai ga Sadik nan yazo, hajiya ta aikoshi ya kawowa yayansa sako, bai tadda Hassan ba, haka ya jira..a anan ma yaci abincin rana, suna cikin hira da Hibba magana ke kawo magana har hiran nasu ya gangaro zuwa ga Afrah, nan ya shaida mata ai tana nan a killace, ashe tun a cikin satin da abun ya faru Hassan ya magance abun, ya aika su Ndagi special mission akan suje har gida su sami mahaifanta da duk wanda suka ci karo dashi a gidan su ja musu kunne idan ba haka ba, duk abunda faru da yar'su su kuka da kansu, a ranar dasu Ndagi suka dira a gidan, ba karamin girgiza yan gidan sukayi ba a tunaninsu yan' fashi ne, sunci sa'a kuwa suka tadda Alhaji a gida suka ja masa kunne ha'de da kashedi mai kyau ya kama yar'sa idan ba haka ba yana gab da rasata, sosai Alhaji ya girgiza da wanan kashedi da aka masa, shi daman all these while baisan wainar da ake toyawa da yar'sa ba, suna gamawa suka tafi.

Alhaji ya kasa tsaye ya kasa zaune, daga Afrah har uwarta sunga tashin hankali a ranar, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, gashi family dinsu Sooraj Marafa ba familyn daya isa ya jada bane, shi kanshi yana mugun mugun shakarsu musaman mahaifinsu Hassan, masifa ya shiga yi sosai yace wani irin tozarci suketa janyo masa da familyn, anyi na farko bata daddara ba an kuma yin na biyu? Toh da ranshi da lafiya baza'ayi na ukun ba, ya dinga blaming uwar nata yace duk laifinta ne, yar'tasu kwaya da'ya da Allah ya mallaka musu amma ta kasa bata tarbiyan da zata rike kanta cikin al'umma

Tun daga ranar yasa tsaro sosai a gidan nasa, Afrah bata fita, harta kofar dakinta yasa masu gadi suna dubata, gabadaya duk kayan shaye shayen da takeyi sai da Hajiya tabi duk ta kwashe kuma ta toshe hanyar da zatayi ta samu, dayake she's already addicted to it, tazo kamar zata zare abun har yana neman ya ta'ba mata kwakwalwa, a ranar da Alhaji ya gano Afrah tana shaye shaye sai da zuciyarsa ta kusan bugawa, ya girgiza sosai bai ta'ba kawowa a ransa tana cikin wanan halin ba, sai da yayi kuka da idanunsa don yasa buri sosai akan Afrah zata gaje shi, daya gano mahaifiyar nata na sane all these while akan halin da take ciki kuma tayi shiru taki cewa komai sai daya ha'da mata da saki da'ya.

Nan da nan yasa aka kaita special hospital na Rehabilitation, komai a sirrince aka dinga yi ba'aso yan'uwa su sani don abun kunya ne a garesu ace da mutuncinsa dakomai yar'sa na wurin rehabilitation, first 3 months da Afrah tayi spending a wajen ba karamin jin jiki tayi ba, ta rame tayi wani iri duk ta sauya kamani, duk yanda taso a bata abun shaye shayen aka ki, gashi abun yana cinta sosai kamar zata mutu.Har yanzu tana can ana kokarin nema mata lafiya.

Duk wanan labarin da Sadik yake bata Hibba tayi jugum tana sauraronsa jikinta yayi mugun sanyi, tana tunanin irin wanan rayuwar data jefa kanta ciki, ace mutum da hankalinsa da komai ya zabi yayi irin wanan rayuwar, Sadik ya ta'be baki "Afrah ce fa... abunda yafi wanan ma zatayi kindai gani da idanunki, so ki rabu da ita, tunda an gaya mata taki ji, duniya zata sanar da ita, ai gashi tun ba'a je ko ina ba ta soma ganin ishara daga ita har iyayen nata da suka daure mata gindi"

"Toh Allah ya kyauta... ni babu wanda nake tausayawa illa Faheema, she doesn't deserve to have a mother with a lifestyle like this, sam bata cancanci hakan ba"

Ajiyar zuciya Sadik ya sauke " Anty Hibba...babu wata uwar da Faheema take da wace ta wuce ki, please let's keep it that way, Afrah bata cikin rayuwarta kuma bazata ta'ba kasancewa cikin rayuwarta ba  har abada, kece komai nata yanzu, da ita da Faheam duk naki ne ki rike, ki daina ma kawo wanan tunanin a ranki please"

Ajiyar zuciya Hibba ta sauke tana sauraronsa cike da sanyin jiki.

***********************
Hibba

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now