Hassan
Yana tsaye ta fice ta bar masa dakin, ya tsaya galala yana kallo ya rasa ma mezai yi, don baiyi expecting wanan maganar data fada mishi ba, hannu yasa cikin lalausar sumar kansa ya rintsa idanunsa yana jin yanda zuciyarsa ke faman tafarfasa kamar zata harba ta fito, jikinsa har tsuma yakeyi, gabadaya tunaninsa a hargitse yake, Hibba ta caza masa kwakwalwa, meye ya hau kanta yau dinan? ta dage sai lallai ta koma, toh ta koma tayi me? So take ta koma ga wahala? He just doesn't understand her.
Indai kulawa ne a tunaninsa zai iya ba'ta ko wani kulawa a duniyar nan, ita kanta shaida ne, ba sai ta koma wanan wahalalen garin nan nasu ba, he can't even imagine leaving her ta koma, gari banza ma bai bari ta tafi ba ballantana yanzu da ta rigada ta zama mallakinsa, ga dan iskan kawun nan nata da Allah kadai yasan inda yake ya bazama yana nemanta, wani irin huccin numfashi ya furzar daga bakinsa, ya kasa tsaye ya kasa zaune, taya ma zai bullo wa wanan lamarin? gashi bazai iya falasa mata sirrinsa ba, dazun saura kadan yayi making mistake na furtawa, ya kasa gane irin wanan taurin kan nata dukda tasan zai iya mata komai a rayuwarnan amma ta daddage sai ta koma, wai tana so ta koma kan wani banzan aikin data bari a baya, bai taba coming across mace irinta ba, she's just different, bata ma damu da abun hannunsa ba tana so ta koma ta nemi na kanta, yasha haduwa da mata da dama da suke numa suna sonsa and it's either one of 3 things, zasu soshi ko dan kyaunsa, ko arzikinsa or his status in life, harta Afrah ma, lokacin da suka fara soyayya kafun ya aureta ya zata she's different sai daya aureta yaga ba haka ba, she's one of the most selfish, self centered person daya sani, bata damu da kowa ba sai kanta, kuma sai yanzu ya kara tabbatar wa kansa kudinsa na daya daga cikin abunda yasa Afrah ta aureshi. Hibba kuma ta zarce tunaninsa, wani irin mazauni na musamman ta samu cikin zuciyarsa yanzu, tun randa ta kwaso jiki daga Maiduguri tazo Lagos don tayi negotiating release din kaninta ya jinjina mata, abunda ya fara drawing dinsa gareta kenan, bravery dinta, zata ita yin komai don ta kare jininta, ba kowa bane zai iya yin abunda tayi ba and it awakened something in him.
Yana tsaye yana wanan tunanin kasa hakura yayi shima yabi bayanta, yana isa parlourn a wurin varenda ya hangota tsaye tana kallon waje, tayi zurfi cikin tunani, from time to time take sa hannu tana share hawayenta, nan take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi, sam baya iya juriyar ganinta cikin wani hali, a hankali ya soma takowa har ya tsaya dab da inda take ya kira sunanta a hankali "Hibba...."
A hankali ta waigo tana dubansa, kallonshi tayi for some seconds sa'anan ta juya ta cigaba da kallon waje,
"We need to talk... ya kamata mu zauna muyi magana" ya karasa maganar yana cigaba da takowa inda yake, tana ganin ya doso tayi saurin kaucewa ta shigo parlourn hannunta rungume bisa kirjinta tace "babu wata sauran magana da zamuyi, nidai na fada maka, zan koma Maiduguri"
"Hibba..." ya sake kira sunanta, bata saurareshi a fusace ta dauki hanya zata shige daki, kamar walkiya yayi taku daya biyu ya cafkota ya juyo da ita ta fada jikinsa, kafun tayi wani yunkuri ya rungumeta tsam a jikinsa yana ajiyar numfashi "karki ce zaki nesanta kanki daga gareni, idan kikayi haka kinyi violating contract din, ki tuna aikinki 24 hour service ne tare dani, taya kike expecting relationship dinmu yayi working idan kikayi nesa dani?"
Hura masa hanci tayi ha'de da watsa masa harara tace " wanan kuma ban sani ba, ai zaka iya zuwa ka gani a duk inda nake idan ta kama maka"
Murmushi ya dan sake yanda tayi maganar " I'm a busy man Hibba... kina tunanin inada lokacin yin irin wanan tafiyen ne?"
Shiru tayi batace dashi komai ba sai faman hucci takeyi, ganin batada niyan saukowa ne yasa ya cusa fuskarsa daidai saitin wuyanta yana shakar kamshinta hade da kai mata kiss a wajen, yasan wanan wurin yana daya daga cikin weak point din jikinta, da zaran ya mata hakan zata saduda ne, ai kuwa he's plan worked don yana kissing dinta a wajen yajibta sake wani irin wahalalen numfashi a hannunsa, jikinta yayi weak, a hankali ya cigaba da kai mata soft kisses yana lasarta ta ko ina a wuyanta har ya gangaro zuwa fuskarta, ya tsinci kansa da mata rada cikin kunne " kiyi hakuri ki daina wanan fushin dani, I'm sorry I made you upset.. I didn't mean to"
Ba Hibba ba harta shi karan kansa sai dayayi shock jin maganar da fito daga bakinsa unexpected, bai san sanda maganar ta kubuce masa ba, ya tsinci kansa da bata hakuri, abunda bai ta'ba yi ba kenan, wai ya tsaya yana bawa mace hakuri, kwakwalwarsa ta shiga cikin rudani, baisan ma meyasa yake yin wasu abubuwa makamancin haka akanta ba, kawai ya tsinci kansa da aikata hakan, yanzu he doesn't want to think about anything, he just wants to be with her don haka yayi kokarin kawar da tunanin ya cigaba da kissing dinta.
"Ki zauna tare dani ba sai kinyi wani aiki ba" ya fada mata in between kisses.
Saurin girgiza masa kanta tayi idanunta a lumshe tana jin yanda feelings dinsa ke ratsa mata ko wani lungu da saku na jiki. "I can't... I don't have anything here, inada rayuwa dana bari can baya, ga kuma kanina, I need to take care of both of us"
"You have me... ki fadi duk abunda kikeso zan miki, I'd do anything for you"
"Bazan iya ba Hassan... bayan bashin da kake binmu bazan iya kara maka wanan nauyin ba, I need a job to support myself and my brother"
Shiru yayi yana sauraronta, bai san meyasa takeda kafiya haka ba, amma gudun kar a sake tada wani rigima yasa yace "toh shikenan naji... tunda aiki kikeso za'a samo miki ko a Lagos ne idan mun koma but please ki ajiye maganar komawa Maiduguri, I need you with me" yanda ya karasa maganar cikin sigar rarashi yana shafarta yasa gabadaya duk jikinta yayi weak, ta kasa koda kwakwarar motsi tana manne a jikinsa.
A hakan ya cigaba da bata baki har ya karasa da ita cikin daki still tana manne a jikinsa suka karasa bakin gado ya zaunar da ita, ba tare da ba'ta lokaci ba ya manne bakinsu wuri da'ya ya soma kissing dinta, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana fitar da numfashi a hankali, tun safe yaketa wanan dokin, yazo ya jishi cikin warmth dinta, yayi kissing soft lips dinta. ga wani irin matsanancin sha'awarta da yake ji yana tasar masa, tunda ya shigo dakin ya kyalara idanunsa akanta yaji mazakutarsa ya motsa, hankalinsa ya tashi, bai ma san ta yanda zai bullo mata ba, gashi yanda yakeji idan har bai sameta ba hankalinsa bazai taba kwantawa ba, tun ba'a je ko ina ba ya soma realizing mistake dinsa na tunanin cewa zai iya having dinta so daya yaji ya gamsu, yanzu ji yake kamar hura masa sonta da sha'awarta ake cikin kogon zuciyarsa, Ko a meeting da sukayi yau da wani client dinsu, kasa barin masa kwakwalwa tayi, every minute every second tana mind dinsa yana imagining dinta, sai da yayi kissing dinta mai isarsa tukuna ya da'go ya ha'de goshinsu wuri da'ya yana ajiyar numfashi.
Not edited.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...