Chapter 90

1.2K 70 0
                                    

Hibba

Ina kwance ina la'latsa wayata bayan mun gama waya da Hassan Ammar yayi sallama ya shigo, ya samu wuri kan kujera ya zauna yana fuskantata "kin tashi"

Na gyada masa kaina ina murmushi, at least na samu enough hutu sosai. Murmushi ya sakar mun "daman nazo ne na dubaki naga ya jikin, tunda gobe zan wuce"

Wani irin sinking feeling naji cikin kirjina danaji ya ambato komawarsa, sam bana so kanina yayi nesa dani nafiso na dinga ganinsa kullum kusa dani ina sa masa ido, amma dana tuno dalilin ma dayasa zai koma sai na dan' saki raina

Daya fuskanci yanayina yace "Kiyi hakuri Ya'Hibba nima da zanso kasancewarmu tare anan Lagos amma kinga dole na koma"

Murmushi na sakar masa, "karka damu Ammar zaka iya tafiya, kaje Allah ya bada sa'a kuma ya kara tsarewa, akaina karka samu wani damuwa, Hassan yana nan kuma inada tabbacin zai bani duk wani kulawa daya kamata, kaima ka gani he's capable"

Gyada mun kai yayi "na sani... sai dai har yanzu..."

"Har yanzu me?" Na tambayeshi ina dubansa

"Kawai har yanzu abun yana mun kamar a mafarki yanda abubuwa suka kasance, wai Mr Sooraj ne ya aureki, like da matsayinsa da komai still bai damu ba yace yana sonki, kinsan Allah Ya'Hibba ban ta'ba kawowa a raina haka abubuwa zasu tafi da zuwana Lagos da komai amma haka Allah ke abunsa nidai farin cikina da'ya shine you're in good hands, nasan zan tafi na barki hankalina kwance, cikin koshin lafiya Mr Sooraj zai kula mun dake yanda ya kamata, zaki samu kulawa sosai, kema ki daure ki bishi sau da kafa kamar yanda Ummi ta bi Abba, ki kyautata masa kamar yanda yake kokarin kyautata miki, kuma ki kara hakuri, na sanki da hakuri amma ki kara akan wanda kike dashi saboda yanzu yanayin da zaki soma tafiyar da rayuwarki zai sauya Ya' Hibba, ba yanda muka taso ciki ba saboda yanayin tsarin rayuwarsu daban take da wanda muka taso ciki amma with time you'll get used to it, Allah ya baku zaman lafiya Ya' Hibba, Allah ya raba lafiya ya kara muku donkon son juna"

Tunda Ammar ya fara magana hawaye suka soma zubo mun musamman sanda ya ambato Ummi da Abbanmu, naji gabadaya jikina ya kara sanyi, a hankali nake tuno abubuwa da dama yanda tun Ummi keda rai takeda burin taga ranar aurena, taga jikokinta..... lumshe idanuna nayi ina kokarin danne zuciyata a raina ina fa'din Allah ya jikan iyayenmu da rahama.

"Haka ne Ammar kanada gaskiya insha Allah zanyi yanda kace, Allah ya kara mana hakuri gabadayanmu, kaima idan kaje can ka kama kanka Ammar, karka bari wani abu ya janye maka hankali ya hannaka concentrating akan abunda ya kaika, kaga yanda su AK suketa yaba halayenka da nutsuwarka, dan Allah ka cigaba karka zuba musu kasa a ido, na sanka da kokari da hankali dan Allah ka cigaba da wanan kokarin, Allah ya bada sa'a..."

"Ameen Ameen ya' Hibba.... zanyi missing dinki sosai"

"Nima zanyi missing dinka Ammar...kuma ina fata idan kaje ka dawo komai yayi kyau Allah ya ha'daka da yarinya mai hankali wace zata soka sosai ku fahimci juna kaima...."

Ban karasa maganar ba naga yayi kicin kicin da fuska, nayi shiru ina dubansa ban san meyasa ba Ammar kwata kwata baya son ina dauko masa maganar aure ko zancen budurwa, ban ta'ba ganin ya nuna interest dinsa akan ko wace mace ba, dukda irin baiwar kyau da Allah yayi masa tun tasowar mu duk inda muka shiga sai ya janyo hankali garesa amma koda wasa bai ta'ba nuna mun yaga wata yana so ba. A raina nace ko don saboda rayuwar mu daban yake bamu taso cikin normal rayuwa ba shiyasa waenan abubuwan basu dame shi ba, Ammar is only focused on how to make life easy for me and him. Ajiyar zuciya na sauke ina dubansa, dayaga kallon nawa yayi yawa ya waske yana shafar sumar kansa yace "ina yar'ki bata dawo daga Islamiyah ba?"

"Hmm bata dawo ba amma ina jin suna kan hanya don daddynta yace zai biya ya daukota"

Dariya Ammar ya sake "nasan ai ba'a rabaku da ita shiyasa nake tambaya, yarinyar tana sonki sosai Ya'Hibba, ta mayar dake tamkar ke kika haifata, she's so close to you"

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now