Hibba
Jin dumin tafukan hannu a gefen fuskata ne ya farkar dani na bude idanuna a hankali suka saukan kan fuskar dana jera kwanaki ina mafarki, zaro ido nayi ina dubansa ina kokarin mikewa, yayi saurin dakatar dani ya daura hannunsa bisa kafadata alamun na koma na kwanta, rintsa idanuna nayi saboda zafi da ciwo da suke mun na bude su a hankali suka tsarku da nashi, zaune yake a gefen gadona dab dani yana kallona da narkakun idanunsa masu narkar mun da zuciya, ji nake kamar a mafarki yazo mun, sake lumshe idanuna nayi ina sake tsareshi da idanuna ko kyaftawa bana yi na zuba masa ido ina binsa da kallo, haka nan na tsinci kaina cikin zallar farin ciki, kasa hakura nayi sai dana sake mikewa na zauna muna fuskantar juna sosai, yayinda gwuiwowina ke ha'de da nashi, wani irin abu naji yana fuzgata gareshi da bazan iya cewa ko mene ba, zuwa yanzu zuciyata tayi sanyi sosai akanshi har ji nake zan iya cigaba da rayuwa dashi koma a yaya makomata zata kasance, zan daure na zauna dashi, idan ma baki daure ba ya zakiyi da rayuwarki? Wata zuciyar ta tamabeyni. Ajiyar zuciya na sauke ina cigaba da kallon cikin kwayar idanunsa cike da zullumi na kira sunansa a hankali "Hassan..."
"Na'am sweetheart"
"Kazo?" Na tambayeshi ina cigaba da kallonsa kamara mafarki
Gyda mun kansa yayi yana kallona, cikin kwayar idanunsa ina iya hango tsantsar so da kauna da yake mun a cikinsu, zuciyata ce ta kara yin sanyi, muryata kasa kasa nace "ina ka shiga? Tun ranar inata sa ido ko zaka zo amma shiru, ko kayi fushi ne dani"
Girgiza mun kansa yayi yana kara matsowa kusa dani "Ko kadan sweetheart, I thought you didn't want me around, na zata baki so ki kara ganina shiyasa na baki space, banso na takura miki, Da safen nan asibitin suka kirani suka shaida mun jikinki ya sake tashi? meyasa baki kirani kin sanar dani ba, ko text da kin turo mun, kema kinsan zan iya barin komai don nazo na kasance tare dake"
Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mun nayi saurin tarewa " ba haka bane kayi hakuri, nasan I've pushed you away these past few days because I was hurt, nasan it's not your fault hasalima you were only trying to protect me, I'm sorry for reacting that way, I just realized how important you are to me"
Farin ciki ne ya bayana a fuskarsa, ya sakar mun murmushi wanda yasa zuciyata melting, murmushi yake sosai wanda har saida dimples dinsa suka bayana, yasa hannunsa yana share mun hawaye " shh... it's okay sweetheart, you don't have to apologize, I understand, none of this is your fault, duk laifina ne, I should have been straightforward and honest with tun farko, Sai dai a lokacin ban ta'ba tunanin abubuwa zasu kai ga haka tsakanina dake ba, but I'm glad it did, you're worth everything to me Hibba, kwana biyun nan na shiga cikin mawuyacin hali a dalilin rashin jinki kusa dani, it made me realize how important you are to me, and I'm willing to do anything just to keep you by my side, kiyi hakuri ki daina wanan fushin dani Hibba, I need you by my side please, I've missed you so much" Ya karasa maganar ha'de da janyoni ya matse gam jikinsa yana ajiyar numfashi, kirjina ne ya shiga harbawa da matsanancin karfin gaske don unexpectedly na jini cikin jikinsa, sosai ya rungumeni har ina jin dumin jikinsa yana ratsani, a hankali yake furta mun kalamai masu tausasa zuciya, yana magana yana shafa mun bayana har na soma relax a hannunsa, a hankali nake fidda numfashi ina shakkar dadadden kamshin turaren jikinsa, gabadaya kamshinsa ya buwayi hancina, ji nake kamar mu kasance a yanda muke har abada tare dashi, shiru mukayi a tare muna musayar numfashin juna, a hankali na lumshe idanuna ina cigaba da sauraron bugun zukatan mu, munfi 10 mins a hakan sa'anan ya da'go yana dubana "so what do you say yanzu? Komai ya wuce?"
Ajiyar zuciya na sauke nace "komai ya wuce, nima kayi hakuri da abubuwan dana furta maka, banyi niyan treating dinka haka ba, ban san me ya hau kaina ba, nasan kayi mun komai kuma kamun hallaci a rayuwa, bakayi deserving haka daga gareni ba, insha Allah daga yau bazan sake nuna maka fushina ba, I regret my previous actions, I'm ready to be with you and to spend the rest of my life with you insha Allah... kuma kasan meye?" Na karasa maganar ina duban cikin kwayar idanunsa, a hankali ya girgiza mun kansa "a'a sai kin fad'i"
"Nima nayi missing dinka fiye ga yanda kake tunani, I missed you so much"
Wani abu ne naga yayi flashing cikin kwayar idanunsa "Da gaske?"
Nayi saurain gyada masa kaina ina kara lafewa a jikinsa, shiru yayi yana dubana with so much intensity in his beautiful eyes, yasa hannunsa duka biyu ya tallafo gefen fuskata yana shafa a hankali, munfi 5 mins muna kallon cikin kwayar idanun juna sa'anan naji ya furta a hankali "I love you soo much Hibbana, I love you with all my heart, daga yau na baki zuciyata, ni naki ne ke kadai, babu wani abun da zai kuma shiga tsakaninmu, insha Allah ke matata ce har abada" ya karasa maganar yana dukar da fuskarsa daidai dab da nawa muna musayar numfashi, hancinmu na gogan juna, wani irin kasala ne naji ya mamaye jikina nima a hankali na furta masa " nima take ce har abada, I love you too"
Lumshe idanunsa yayi cike da jin dadi yace "say it again.."
"I love you.." na sake furtawa a hankali
"Sake maimaitawa" ya fa'da muryarsa kasa kasa yana kara goga dogon karan hancinsa da nawa.
"I love yo...."
Ban karasa maganar naji saukar lips dinsa bisa nawa ya katse mun saran magana, ya soma kissing dina a hankali, wani irin yanayi na tsinci kaina na kasa koda kwakwaran motsi a hannunsa, na langwabe masa shi kuwa ya rikeni kamar kwai, idanunsa a lumshe ya cigaba da kissing lips dina yana kara manneni a jikinsa kamar za'a kwace masa ni, a hankali yake shafar fuskata yana tsotsan lips dina, gabaday duk wani tsiro na gashin dake kwance a jikina babu wanda bai mimike ba, sai faman ajiyar nunfashi nake ina kara jin wani irin sanyin dadi a raina.
Ban san iya tsawon lokacin da muka kasance dashi a hakan ba, sai da yayi kissing dina iya son ransa tukuna ya dago yana dubana da kyawawan idanunsa yana ajiyar numfashi.
Not edited
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...