Chapter 20

1.2K 78 4
                                    

Hibba

Gaban wata makeken kofa muka tsaya, ba tare da ba'ta lokaci ba Hassan ya danna kararawa, kofar ta budu, wani mutum muka gani tsaye sanye cikin suit, dogo ne sosai zasuyi kusan tsawo da'ya da Hassan, a hankali nake binsa da kallo zuciyata cikeda fargaba, kyakywa ne sosai fatar jikinsa chocolate color, na fara tunanin duk mutanen Hassan da muke haduwa da babu mumuna cikinsu, mazaje ne da suka ansa sunansu maza, buri da sha'awar duk wata lafiyayar ya'mace.

Kallonshi kawai nakeyi na kasa dauke idanuna akansa, murmushi ya sakar wa Hassan ya mika masa hannu suka soma gaisawa, a hankali ya dawo da dubansa gareni, wani irin yarr naji a game da idanunsa da suke yawo akaina, bance masa komai, munfi minti biyu a hakan yana faman bina da kallo daga bisani naga ya tuntsire da dariya.

"My God!...." ya fa'da yana matso da fuskarsa dab da nawa "lallai jini ba wasa, they look exactly alike, too bad you're taken" ya karasa yana murmushi

Hassan na jin haka yayi kicin kicin da fuska kamar bai ta'ba dariya "hands off Ak" ya fada masa cike da warning.

Daman wanan ne AK din? Na tambayi kaina, wanan ne mutumin da yake azabtar mun da Ammar? Yayi kama da masu irin wanan mugun halin, Wayo Allah kanina, na fa'da can kasan raina ina jin yanda bugun kirjina ke kara tsananta.

A hankali AK ya soma ja da baya yana fa'din "mayar da wukar kaima kasan I have my own taste there's no way I'm interested"

Hararar wasa Hassan ya sakar masa muka karasa ciki ina biye dashi a baya, muna shiga sai faman baza idanu nake ko Allah zaisa na ganshi, ai kuwa Hassan na matsawa idanuna suka hango mun shi zaune ta daga can gefe

"Ammar!!!" na fada da iyakacin karfina na ba'lla a guje naje na fa'da jikinsa ina rungumeshi tsam a jikina.

"Ya Hibba..." ya fa'da yana zaro ido, gabadaya a rikice yake ya kara rungumeni  "wayyo Ya' Hibba ashe kinzo"

Kuka na fashe dashi, jikina na wani irin kyarma na rikeshi gam, ina mikawa Allah godiya dayasa na sameshi cikin koshin laifiya, kuka Ammar shima yakeyi yana fa'din "ya Hibba I'm so sorry... kiyi hakuri ki yafe mun, sai da kika ce mun kar na taho amma na nace, gashi halin dana fada, ki yafeni Ya' Hibba nayi kuskure"

A hankali na da'go ina dubansa hawaye na zuba mun, Ammar ya fini tsawo sosai, siriri ne bashida jiki kamar ni, ina kallonsa tamkar ina kallon kaina a madubi don kamanin mu da'ya, wani idan bai kai hankali nesa ba zai iya cewa mu tagwaye ne, Ammar kyakyawan yarone, sanyi sanyi dashi bashida hayaniya ko kadan shiyasa mutane ke yawon taking advantage dinsa, kuka yakeyi sosai na ruko hannunsa a hankali ina fa'din "Shh...ya isa haka Ammar, koma meye ta rigada ta faru, ni daman fatana bai wuce nazo na sameka cikin koshin lafiya ba, tunda Allah ya rigada yasa na ganka koma meye zamu magance tare" na fada ina jan hannunsa muka nemi wuri muka zauna ina fuskantarsa, kasa rike kaina nayi don ina son nasan komai yanda akayi ya fa'da cikin wanan matsalar.

"Dan Allah ka sanar dani komai Ammar... karka boye mun komai"

Shiru Ammar yayi yana nazari, idanunsa cike da fargaba, kamar yana shakar ya fa'da mun, na sashi a gaba, idan bai fa'da mun matsalarsa ba wa zai fadawa? Tun yana karemi nake kula dashi har ya kawo haka, so bai kamata ya boye mun wani abu ba.

"Ammar?" Na sake kiran sunansa ina sauraron bayani.

Ta gefen idona ina iya hango Hassan da AK zaune can gefe suna hiransu sun kyalemu daga ni sai Ammar.

Dogon numfashi Ammar yaja ya fesar "I was so stupid Ya'Hibba... na zata zuwana Lagos zai bude mana hanya, zan samu na fitar da mu cikin talauci, musaman ke, banson ganinki kina wahala safe dare rana akan mu, nazo da burin na samu kudi dayawa na gina mana rayuwa ingantace, na siya miki duk abunda kikeso Ya'Hibba, daga nan ki samu ki bar wanan wahalalen aikin inda basu ganinki da daraja"

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now