Chapter 68

1K 68 10
                                    

Hibba

Ina kwance a wajen ina kallon Kawu Abu bayan ya gama ba'batunsa akan yanda yake sona da mahaifiyata. Har yanzu kokarin digesting abun nake cikin kwakwalwata, ina cikin wanan tunanin unexpectedly naji yayi pouncing akaina.

Bai tsaya ba'ta lokaci ba wajen ha'de bakina da nashi ya soma kissing dina,
Kara na sake a mugun firgice ina kokarin kwatar kaina, ya kara danneni akan gadon da iyakacin karfinsa, kokuwa na soma kokarin yi dashi, ya kamo hannuna duka biyu cikin nashi ya matse ta yanda bazan iya motsi ba, nayi nayi na kwace kaina naji na kasa, hawaye ne masu zafi suka gangaro mun, ya matso dab da kunnena ya zira harshensa ya lashe wurin sa'anan ya rada mun cikin kunne "dama ki daina wanan kokuwan da kikeyi kiyi relax don babu yanda za'ayi kiyi escaping daga hannuna, wanan ranar na jima ina jiranta, yau rana ce da zan kwashe garan dadi, Kawu Abu zai jiyar dake dadi irin wanda baki ta'ba jinta ba" sai faman shinshina wuyata yakeyi yana bi da hannunsa duk inda yaci karo a jikina, ina kwance a wurin jikina sai faman kyarma yakeyi hawaye na zuba mun, ganin yana kokarin rabani da kayan jikina naji wani irin sabon firgice ya ziyarce  na zaro ido cike da matsanancin tsoro ina dubansa na soma girgiza masa kaina, "Kwu Abu dan girman zatin Allah karka mun haka, karka ce zakayi wani abu dani ina rokonka da Allah da manzonsa, please..."
Murmushi ya sakar mun "relax Hibba, ke kanki zakiji dadi, ki bari Kawu Abu ya kula dake ya nuna miki irin son da yake miki"

Wani irin wahalalen numfashi naja na fezar ya kara danneni kan gadon, yasa hannu ya soma tuge igiyan dake gaban abayan jikina yana murmushi yana kallon fuskata, na rintse idanuna, ina rokon Allah ya dauki raina, don a ganina mutuwa ce kadai sauki gareni da akan wanan mumunar Abun da Kawu Abu yake shirin aikatawa gareni, ina jinsa ya gama kwance igiyan Abayan ya dagota ya cireta gabadaya daga jikina, na rage daga ni sai bra da pant sanye a jikina, wani irin kara na sake na soma jijiga gadon ina kokarin kwatar kaina daga gareshi "ka sake ni Kawu Abu!! Na tsaneka!! Ka daina mun abunda kakeyi!! Ka daina ta'bani bana so!!!"

Kuka na fashe dashi a wajen jin irin wanan tozarta da rashin mutunci da kawu Abu yake mun, na soma kokarin juyawa don na kare jikina amma yasa kafafunsa duka biyu ya danne, a hankali ya soma bin jikina da kallo idanunsa suka sauka kan kirjina nan take naga idanunsa sun bulluko, ya rikice ya rude, ya soma lashe lips dinsa tamkar wani tsohon maye, ina kwance a wurin sai faman kuka nake, a hankali ya dauke idanunsa daga kirjina zuwa kasan marata ya tsaya cak, nan take naga murmushin ya ba'ce daga fuskarsa, yana bin cikina da kallo tamkar yaga horo, a kidime naga ya kai hannunsa cikina ya soma ta'tabawa, ya danna da iyakacin karfinsa sai dana saki kara, "Bura'uba!" ya furta a kidime yana kokarin mikewa ya sake fincikoni garesa, bai tsaya ba'ta lokaci ba ya ware kafafuna ya tura hannunsa cikin pant dina, yatsansa naji ya ratsa cikin jikina, kara na sake ina kokarin kwatar kaina

"kam bala'i me zan gani?"

Wani irin wawan mari naji ya daukeni dashi a wajen, nan take naji kaina ya soma juyawa, kafun kwakwalta ta gama registering meke faruwa dani da kuma dalilin dayasa ya sakar mun mari haka, naji ya sake daukeni da wani marin,

Kara na sake jin zafin daya ratsa kwakwalwata lokaci guda, Kawu Abu ya dawo tamkar wani mahaukaci  a kaina, mari yaketa faman kaimun ta ko ina, kuka nake ina kokarin kwatar kaina daga dukan da yake mun" yar kutumar uba daman ciki gareki?! ciki Hibba? A gidan uban wa kika roro wanan cikin? Wani dan kutumar uban ne yayi miki wanan cikin? Ni zaki ciwa amana ni zaki yiwa haka??!!! Abunda na jima ina tanadi shine kika dauka kika bawa wani?"

A mugun zuciye naji ya sake kaimun naushi a gefen fuskata, ihu na sake, kafun Kwakwalawata ta gama registering abunda yake faruwa naji yasa hannu ya shakoni da iyakacin karfinsa "yau sai na aika dake lahira! Karuwar banza karuwar wofi kawai!! Har kinada mind din da zaki budewa wani kafafunki har yayi miki ciki? Toh wlh Hibba ki kuka da kanki, ni Abubakar yau zan kasheki da hannuna, kuma ina kashe banza in kashe wofi" sosai ya shake mun wuya, nasa hannuna duka biyu ina kokarin kwatar kaina gabadaya a firgice nake hankalina yayi mugun tashi, sai faman zaro ido nake saboda numfashine dake kokarin tsaya mun don ba karamin shaka ya kaimun a wuya ba yana hucci a kaina, jikina ne ya soma yin weak saboda restricted airflow, naji dakin ya soma juya mun, unexpectedly ya sake daukeni da wani marin ha'de da kaimun naushi kuma a fuska, nan take wuta ta dauke mun ban sake sanin inda kaina yake ba.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now