Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG018.
Tun bayan mutuwar mahaifinsu saadatu a yan uwansa ba wanda ya dakko ko kwayar shinkafa ya kawo da sunan ga shi a dafa a bawa yayan marigayin amma duk da haka Allah bai hana su anincin da zasuci ba dan a rana suna cin abinci sau biyu sau uku sutura ma umma ladidi na kokarin dinkawa yayanta gudun kar su dinga kwadayin na mutane a shekara sai ta dinka musu sau Biyar ko ma fiye da hakan wannan halinda saadatu taga mahaifiyarta a ciki shi ya hanata kula samari kwata kwata wannan dalilin ne yasa kawunta bello yake mata lakabi da mai kashi tsiya wannan shine takaitaccen tarihin saadatu Aminu.
Ba saadatu ta farka ba sai wajan sha biyu na rana a washe garin ranar ta farka lokacin gaba dayansu suna falon azeema a zaune suna mamakin rashin farfadowar ta jin motsi suka yi alamar ta tashi kenan da sauri azeema ta shiga dakin kallon kallo akayi tsakanin azeema da saadatu nan take saadatu ta tuno da halinda take ciki bigeta akayi da mota tace likita ina ne kafin ma ta karasa murmushi azeema tayi tace sannu sis saada yanxu dai kiyi wanka kiyi brush ki kuma yi alwala ki rama sallolin da ake binki in kika ci abinci tukunna sai in yi miki bayannin abinda ya faru dake,gysda kai kawai tayi dan jin ta takeyi wata iri gashi kuma jikinta gaba daya ciwo yakeyi,amma dai bazanyi wanka ba bara nayi sallah tukunna bandakin ta Shiga ta dauro alwala ta yi sallar laasar tana idarwa ta kalli agogon dakin ganin sha biyu sai gabanta ya fadi ta yi magriba da ishai tana tunanin ya ummanta zataji gashi har dare ya tsala bata tafi gida ba tana wannan tunanin azeema ta shigo da abincin tace likita naga sha biyu na dare har tayi murmushi azeema tayi tace sis saada sha biyu na rana ne ba na dare ba kiyi sallar asuba tukunna ga abinci kici sai muyi a nan na kwana kenan ta tambaya banza azeema tayi mata ganin ba zata amsa ba yasa ta tada sallar asuba amma ta kasa cin abincin wanka azeema tasa ta tayi ta kuma bata abaya ja tasaka.
Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh
YOU ARE READING
Mr&Mrs Fawaz
Romantikthis story is about 5goods friends that can sacrifices their happiness for there beloving once.