Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0By Ayshart sani
82.
Wata tarairaya ta musamman saadatu take samu daga fawaz Wanda ita yanxu Banda kunya babu abinda takeji duk inda su fawaz zasuje to fa har da saadatu zaaje gurin aiki Kam Dama tuni ta koma abinta ya nemi alfarmar a barta a permanent morning Kuma an karba Dan haka permanent morning kawai takeyi Dan Bai yarda ya katse Mata rayuwa ba.
Zaman lafiya saadatu wani irin son fawaz ne yake Kara cika Mata kirji Dan duk wani abinda zai Bata Mata Rai bayasonsa Dan haka itama Bata son bacin ransa kwata kwata,sabani dama dole ne Amma in itace take fada baya kulata haka itama in yanayi bata kulawa shiyasa suke kwanciyar abinsu ga wasu kayan Mata da naanna take dirka Mata na kayan gyara kullum Kara cika takeyi kullum a amarya yake jinta,Fahad ya fahimci fawaz da biyu yake Masa cin mutunci akan matarsa Dan haka ya bawa su daddy go ahead akan neman aurensa sukayi shawarar kawai a hada bikinsa Dana azeema da Yusuf.
Rayuwa ta sauya an yankewa alhaji Usman hukunci dai dai abinda ya aikata azeema tayi namijin kokarin gurfanar da mahaifinta da tayi a gaban kotu tareda bada shaida akan abinda ta sani alkali ya yanke Masa hukunci zaman yara na shekaru,an daura auren abbu da naanna,mama ta nemi gafarar su fawaz akan abubuwan da tayi musu Kuma duk sun yafe Mata abbu ya gina asibiti na kansa inda duk yayansa da wasu Manya Manyan likitoci suka aiki a cikinsa a inda Kuma anyi bikin azeema da Yusuf dinta shima Fahad da tasa sahibar.
Umma ma an zama hajiya domin kaf dinsu suka kwasa sukaje suka sauke farali saadatu hankalinta ya fara tashi ganin shekara daya d doriya bata samu ciki ba ta fito free tayiwa fawaz maganar cikin lallashi ya nuna Mata ba komai Allah ne Bai basuba Kuma Basu cire Rai ba hakuri ya bata bayan sun bincika komai normal Allah ne Bai Basu haihuwa ba.
Mariya an fara girma kanwar saadatu fuad tunda ya ganta yace yaga Mata Suka kulla zumunci Shida ita sosai suke nunawa juna kulawa,saadatu ta bar gidansu fawaz ta tare a nasu gidan ita da mijinta cikin soyayya da kulawar juna inda Yusuf ma basuda nisa dasu fawaz Fahad da dama su tare gaba dayansu aka siya musu fili gini komai da komai iri daya akayi musu Dr abdullahi da Dr Deen an Kai kudi ranar biki kawai ake jira.
Ayshart sani.
YOU ARE READING
Mr&Mrs Fawaz
Romancethis story is about 5goods friends that can sacrifices their happiness for there beloving once.