Mr & Mrs Fawaz

45 5 0
                                    

Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0

By Ayshart sani

21.

Kallon tsaf umman tai musu sannan ta dauko tabarma ta shimfida musu tace bisimillah Ku zauna zama sukayi nan dai azeema ta kwashe kaf labarin ta fadawa ummansu Saadatu shiru umman ta danyi sannan tace Saadatu kallonta tayi ta yi tace naam umma tace ba wai dan ban yadda da abinda wannan baiwar Allah din ta fada ba Amma ina so ki san wani abu idan har kikai min karya bazan taba yafe miki ba dan banyi muku tarbiyar karya ba Saadatu tace eh umma baxan taba fada miki abinda nasan karya ne ba kafin umma tai magana Dr deen ya shigo gaisawa sukayi da umma yabi bayan yan uwansa ya zauna,umma ta kalleta tace kin tabbatar kadeki akayi ba wani gurin kika tafi ba saadatu tace eh wlh umma kadeni akayi ta rantse ta kuma rantsewa akan kadeta akayi nan umma ta Kada kai tace na yarda tashi ki shiga ciki.

Mikewa tayi ta shiga cikin dakinsu kallon azeema umman tayi tace ba wai dan ban yarda dake ba nayi mata wannan tambayar aa sai dan baa shaidar dan yau duk da nasan irin tarbiyar dana bawa yayana,banaso rashin mahaifinsu ya sasu shiga hanyar halaka na gode da irin taimakon da kukayi wa yata Allah ya biyaku nagode sosai suma godiyar suka yi tare da kara bawa umma hakuri sannan suka mike dan tafiya kiran Saadatu umma tayi tace kixo kuyi sallama zasu wuce fitowa tayi idonta duk ya kunbura alamar kuka sallama sukayi ta rakasu har kofar gida Amma ta Kasa ce musu komai saboda yadda muryarta take rawa haka sukayi sallama suka dau hanya tafiya sukeyi a mota Amma Ba Wanda yake yiwa dan uwansu magana sbd tausayin saadatu.

A garden din gidansu fawaz suka yada zango kowannensu jugum jugum saboda tsananin tausayin Saadatu da halinda suke ciki fawaz da ke dakinsa yana tunanjn meya zaunar dasu haka har yanxu ya fito dan ya leka gidansu azeema ko sun dawo suna can, a parking lot ya ga motar azeema hakan ya tabbatar masa da sun dawo suna garden,garden din ya nufa shima a zaune ya gansu jugum jugum.

By Ayshart sani
Wattpad@Ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now