Mr Mrs Fawaz

20 4 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

66.

Sanyin asuba ne ya farkar da na'anna lokacin fu'ad ya fita masallaci dafe da kanta ya Mike toilet ta Shiga ba abinda ya canja har drawer din dakin dan ita tayi musu ordering kayan har kujerun daga China da sunan dady ne ya siya da murmushi ta shiga bandakin tayi alwala ta fito agogo ta kalla ta tabbatar da asuba ce yanxu Dan haka tayi sallolin da suke kanta tareda asubahi tana nan zaune tana addu'o'i taga flask din shayi dana abinci Dan haka ta zuba tasha tea din tana sha shigowar saadatu ne yasata daga kanta ta kalleta da murna saadatu tace kin farka tace na farka daughter har nayi sallah ma saadatu tace asuba ce yanxu tai murmushi tace sanyin asuba ai daban yake kowa Yana ganeshi gyada Kai saadatu tayi.

Shigowar Fawaz da fu'ad ya matukar bata mamaki kwata kwata Fawaz baiyi tunanin ganinta a zaune a falo ba saboda fu'ad yace Masa Bata farka ba shikansa yayi mamakin Jin hakan shiyasa yaxo Dan ya dubata ganinta yasa shi kokarin juyawa ya fita dakatar da shi tayi zan bar maka dakinka Zan Koma dakina kallon saadatu yayi tace haka tace min har zaiyi magana sai kuma yayi shiru tace sannan inason magana daku da safe in Allah ya kaimu k sanar da danuwanka zamuyi magana a main falo insha Allah ta juya ta fita daga dakin bedroom ya Shiga ya gyara gado ya haye abinsa,shigowa tayi da niyar Yi masa magana Amma ganin bacci zaiyi yasa ta kyaleshi kawai ta hau gyare gyareb dakin bayan ta gama kitchen tayi ta dade a kitchen din saboda aikin ranar yafi na kullum bayan ta gama dakin Fahad da suka Bata can ma taje ta gyara Masa abinsa.

Takwas da rabi ta dauki breakfast din su na'anna ta fito main falo a zaune ta tadda dady bayan sun gaisa ta tambayesa dakin na'anna nuna mata corridor din kusa dasu Fawaz yayi yace in ta shiga anan yake sosai take mamaki Dan tsawon zamanta a gidan tana yawan ganin ana gyarawa Amma bata taba kawowa Wai dakuna ne a gurin ba kofa ta biyu ta bude kamar dai dakinsu Fawaz shima wannan haka yake har yafi nasu Fawaz kyau da tsari suna zaune a falo ita da fu'ad suna Hira kamar yadda suka Saba gaisheta ta karayi fu'ad ne yace Ina kwana in-law tana dariya tace yau Kuma shima Yana dariya yace eh mana tunda matar yayana ce kinga ai dole a Baki respect tace naji ga break nan sai a karya sosai na'anna tayi farin ciki da samun suruka kamar saadatu tayi godiya dariya saadatu tayi tace Kai na'anna nikam kunya kike bani in kina min godiya wlh shikenan bara naje sai anjima din ta fada tareda fita daga dakin.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now