Mr & Mrs Fawaz

30 4 0
                                    

Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0

17.

                   Wacece saadatu
Saadatu yace a gurin malam Aminu da umma ladidi yace ta farko mai shekara Ashirin da doriya tun auren Aminu da ladidi yan uwan aminun basa so haka dai Allah ya kaddara sai Aminu ya auri ladidi tun daga lokacin bakakaen maganganu,hassada da mugayen fata ba Wanda ba aiwa ladidi ba haka dai suke zaune cikin rufin asirin Allah tana saida kayan miya tun tana amarya kasancewa malam Aminu kifi yake siyarwa Allah kuma ya rufa masa asiri abinci dai a gidansa sau uku ake samunsa har Allah ya azurtasu da samun cikin saadatu bayan sun kwashe shekara biyar suna nema dangi har sun fara kiran ladidi da juya har aka haifi saadatu dangin basa son ladidi.

Tsana suke nunawa saadatun tun tana karama har ta fara tasawa ta fahimci meke faruwa a rayuwarta har lokacin kuma Allah bai bawa ladidi wani cikin ba sai da saadatu ta shekara sha da watanni sanni Allah ya kara azurta ladidi da wani cikin,rainon ciki ladidi takeyi me laulayi har ya fara girma cikin nada wata bakwai da kwanaki akaiwa malam Aminu kiran gaggawa a gurin da yake saro kifi dan haka ya fita gabannin magriba dawowar da baiyi ba kenan da ransa dai gawa aka kawo gidan haka ladidi ta Shiva tsananin tashin hankali har Allah ya sauketa lafiya ta kuma haifar ya mace aka saka mata mariyatul adawiyya suke kiranta da Mariya yar da ko ragon suna baa yanka mata ba saboda tun da malam Aminu Allah yayi masa rasuwa ta Shiva tsananin tashin hankali da kyar ake samun abincin da zaa ci bare kuma ragon suna,haka dai suke rayuwa duk wata Sana'a ta cikin gida umma ladidi yinta takeyi har Allah ya kawosu lokacin da saadatu take tallafawa rayuwarsu kudin da gwamnati take biyanta na aikin da takeyi,karatun saadatun ma da kyar aka karasa sa dan Allah ya kawo musu me taimakon rayuwarsu.

Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now