Mr & Mrs Fawaz

19 2 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

69.

A haka muke rayuwa cikin soyayyar juna da Kaunar juna duk bayan kwana 2 Ina zuwa gidansu umma Dan bamu da wadanda suka fisu bayan kamar wata shida a tareda su Inna mukayi munga canjin rayuwa da dama munyi karatu arabi da boko Amma akwai banbanci karatunmu na can da na nan Dan haka muka Koma makaranta dan mu Kara wayewa akan harkokin rayuwa na lokacin bayan mun gane yanayin rayuwar sai mukayi sharawa da aliyu akan ya kamata mu siyar da wasu daga shannunmu mu zuba jarin kanmu a kasuwa nayi naam da shawararsa amma na fada masa muyi shawara da su umma tukunna bayan tattaunawa dasu suma sunyi naam da hakan sun kuma goya Mana baya akan hakan bamu siyar ba sai da sallah taxo lokacin sunyi tsada muka siyar da goma Sha daya muka bar guda biyar a ciki domin kanmu zamu cigaba da kiwonsu.

Haka muka siyar da shanu guda  takwas mun samu kudi miliyan daya da kusan dubu dari takwas haka muka dawo gida bayan nan aliyu ya dauki guda 1 ya bawa su umma domin halaccinsu garemu su alhaji Usman ma ya dauki shanuwa daya ya basu su raba suyi layyar sallah da ita,a haka ya samu ubangidansu na kasuwa shi ya Kara nuna masa hanyoyin kasuwanci haka muka fara da miliyan daya da dubu dari biyar miliyan daya da rabi kenan kafin kace me alh.aliyu mai nagge ya bunkasa ya Zama attajiri na bugawa a jarida domin Allah ya sawa kasuwancin albarka haka ya dawo nan Jan bulo ya siyi filaye guda 2 ya ajje shida mukhtar suke komai a lokacin ne Kuma mukhtar da alh Usman zasuyi aure a lokaci guda bayan aure duk sun tare a gurare daban daban a lokacin Kuma arziki kamar me Allah ya basu bayan gama gini da aliyu yayi muka Koma a nan mukhtar ya kama haya shima nan aka kawo matansu shida alh.usman Dan duk a tareda mu suke zaune bayan kamar wata biyar muna tare dukanmu a wannan lokacin alh.nura da alh.mahmoud suma suka dawo kusa damu wannan shine tushen komai a lokacin Kuma Allah ya azurtamu da cikin da sai daya Kai wata biyar tukunna nasan dashi Wanda ya kasance dukanmu muna dauke da juna biyu Banda maryam matar da mukhtar da alh.usman Yan biyu sun bawa shamsu wata biyu inda shamsu ya bawa abdullahi wata daya duk kusan tare muka haihu Amma har a lokacin maryam Bata haihu ba wadda take ganin kamar ni na hànata haihuwar hakan yasa bama zaman lafiya tareda ita gashi wadanda zasuyi Mana tsakani da ita Allah ya yi musu rasuwa sanadin hatsarin mota zuwa garinsu su umma Allah ya karbi abinsa.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now