Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9By Ayshart sani
39.
Mikewa saadatu tayi tace aure Kuma kawu Dan Allah kayi hakuri kar kayi min aure kawu kallonta yayi yace ke har kinyi girman da Ina magana da uwarki kina sa min baki to ki maida hankalinki kanki aure ne ba fashi,kawu ka taimaka min bazan iya yin biyayya ga mutumin da banaso ba Dan Allah kar Allah yasa kiyi dukane zakisha kamar jaka Dan shima ba mutunci ne dashi ba wahala zaki Sha kallon mamaki umma tayi masa tare da hadiyan yawu tace waye mijin da zaka aura Mata,sagiru ne dan gidan malam audu mai kaba Kuma bazan fasa ba shi ba kallon mamaki umma tayi masa tace ka rasa Wanda zaka bawa auren yata sai yaron da bashi tarbiya bashi da ilimi ban isa in zabawa ita yar taki mijin aure bane kome kana da ikon zaba mata Amma ba irin wadannan mazan marasa tarbiya ba ni dai na gama magana Dan haka ku Zama cikin shiri bayan azahar.
Kuka saadatu tasa tace umma Dan Allah kar ki Bari ya aurar dani bazan iya ba wlh kallon tausayi umman tayi Mata tace dauki kayanki ki tafi gidan yakumbo in yaxo yaga bakya nan dole zai hakura ya kyaleki tunda bazaa daura aure da Babu ba Ina da Kaya a gidan umma to tashi maza ki tafi can Allah ya kiyaye daki ta shiga ta dau uniform da Yan abubuwan bukata ta fito wayarta ta dauka ta fita bayan sunyi sallama da umma sai a lokacin ta tuna waya take da saadatu tana danna wayar ga mamakin ta gani tayi har a lokacin baa kashe wayar ba hello shine abinda tace Azeema tace me ke faruwa sis saada wlh likita kawu na ne yakeson yayi min aure kafin Azeema ta Dora magana akai mota taxo ta make saadatu.
Da salati matar ta fito daga mota tana salati innalillahi wa'inna ilaihir rajiun shine abinda take ta maimaitawa gashi gurin ba kowa kana ganin matar kaga kyau Amma babbar macece ba yarinya ba.
By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

YOU ARE READING
Mr&Mrs Fawaz
Romancethis story is about 5goods friends that can sacrifices their happiness for there beloving once.