Mr & Mrs Fawaz

15 6 1
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

60.

Sosai saadatu tayi murnar ganin na'anna rungumeta tayi tace Ina ta missing dinki dariya tayi tace ai gashi kinganni ko,hmm abinda fu'ad yace kenan Wai ni haka zaku dinga zalinta ta kenan in kun hadu kallonsa saadatu tayi kishi kake dani kenan kyaleshi yata halinsa kenan in ya ganni da mutane harararsa saadatu tayi tace to bakin Hali kenan babba da Kai kana bakin Hali anji kunya fa ni dai ai na gama da Kai in fada maka,ni dai ba wannan ba ga guri ki zauna Zama tayi tace ni Ina ga nan Zan dawo kawai saboda shi Kuma mijin naki bashi da aikinyi ko murmushi tayi tace hmm haka dai kake gani na'anna tace eh daki naji dadi sosai ko wata ai kwayi min murmushi tayi tace yace anjima in yaxo daukata zai shigo ku gaisa to shikenan Allah ya kawo shi,Ashe Zaki gane gidan tace ah haba zuwana biyu fa ai ni ko sau daya naje guri Ina ganewa Dan ace kina saurin gane abubuwa ko tace kaji dashi ni ba Dan Kai naxo ba shima murmushi yayi nan suka barke da hira girki ma tre suka Yi shi ranar shima fu'ad ya makale a gida ya kasa fita saboda tsokana.

Hudu da quater Fawaz yayi Mata waya akan yaxo su tafi fu'ad na'anna tasa ya shigo dashi har dake gate man ya bude Masa ya Shiga cikin gidan tunda ya Shiga gabansa yake faduwa,gabansa bai tsananta faduwa ba sai da suka hada ido da fu'ad Yana Masa kallon sani bayan sun gaisa yace muje ko Jin muryarsa ma ya kuma kada Masa tunani a take a gurin yace abbu,kallonsa fu'ad yayi yace naam yace who are you yace ni Dan gidan ne ance in shigo da Kai ne bin bayansa Fawaz yayi har cikin falon tafiya sukeyi kowanne da abinda yake sakawa a ransa fu'ad ma ganin Fawaz yasa jikinsa yin sanyi kalau ya nuna masa guri yace bara na kirasu Kai kadai Fawaz ya iya gyadawa,Shiga fu'ad yayi Yana falo yace gabana ne yaketa faduwa na'anna itama tunda aka bude gate nata gaban yake faduwa Amma sai tayi murmushin karfin Hali tace dauki drinks k Kai Masa gamu nan dauka yayi tare da fita hannun saadatu taja suka shiga daki ta bata duk wasu abubuwan bukata tace muje to daga nan sai mu gaisa ba kyau shanya miji mikewa sukayi suna fitowa har kofar main falo nan gaban duka su biyun bugunsa ya tsananta saadatu tace nayi mantuwa murmushi naana tayi tace jeki dauka bara na shiga ni mu gaisa kafin ki dawo tace okay toh shiga tayi da sallama fu'ad ke kallon kofa tace Ina Dan nawa juyowa yayi da niyyar gaisheta mikewa tsaye yayi yace ke.....ke.......Ke ..........

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now