Mr &Mrs Fawaz

17 5 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

42.

Fahad Ina danuwan naka Yana daki ya bashi amsa kiramin shi samsu mikewa Dr deen yayi ya shiga dakin Dan Kiran Fawaz falon cike yake da mutane iyayensu maza da Mata,sai Kuma su kansu aminan juna fitowa sukayi gurin suka samu guri suka zauna kallon su yayi yace alhamdulillahi kamar yadda kukaga na Tara ku anan na taraku ne Dan in sanar daku hukuncin Dana yanke akan Fawaz ba tare da saninsa ba sai dai wasu daga cikin Yan uwana sun sani alh.usman, alh.Mahmoud, da alh.nura duk sun sani Fawaz cikin mamaki yake tunanin wane irin hukuncine aka yanke akansa haka da sai ya tara gaba daya mutane zai sanar dashi kallon Azeema yayi yai Mata Alamar ta San akan abinda ake magana cikin farinciki ta nuna masa aa ya dauke idonsa ne kawai badan ya yarda ba.

Kallonsa dady yayi yace Fawaz a yau na biya sadakin aurenka Kuma an daura maka aure Wanda nasan har abada bazanyi Dana sanin aurenka ba auren da zakayi alfahari dashi a gaba insha Allah,ai ba Fawaz da aka fadawa maganar ba har Dr deen sai da gabansa ya fadi juyawa Fahad yayi ya kallesa ganinsa yayi gaba daya lokaci daya ya canja jijiyoyin kansa gaba daya sun Mike,kafin dady ya Kara magana Fawaz ya tari numfashinsa cikin murya me abin tausayi yace dady Dan ka zaba min matar aure shine har sai ka sanar dani hakkin iyaye ne su zabawa yayansu abokan Zama na gari wadanda zasuyi alfahari da junansu,tun tasowarmu Kai ne ka Zame Mana jigo a rayuwarmu nagode da wannan aure da kayi mini Allah ubangiji ya bani ikon yin biyayya a gareka bamusan dadin kowa ba a rayuwarmu sai naka wadda ta haifemu ma ta gujemu Kai ka Zame Mana tsani madogoro nagode sosai da sosai mikewa yayi kawai ya Shiga daki jikinsu ne gaba daya yayi sanyi kallonsu dady yayi yace nayi hakan ne Dan ceto yayanmu daga hlaka da Kuma ceto har daga fadawa hannun gurbataccen mutum,Dr deen ne ya katse shi yace ni dai Dan Allah kar ayi min irin wannan auren Ina da wadda nakeso dama a cikinmu shine bashi da budurwa alh Usman yace to hanzarta sanar da Yan matan naku kema Azeema Yusuf ya sameni nace Kuma ya turo magabatansa kasa tayi da kanta Bata tanka ba nan dai aka sallami yara su Kuma iyayen suka cigaba da tattauna abubuwa masu mahimmanci.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now