Mr&Mrs Fawaz

15 3 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

55.

Fitowa suka Yi daga kitchen rike da tea flask a hannunta ta riko yasmeen da dayan hannun Mika masa tayi tace gashi karba yayi yace tnx tare da kallon yasmeen yace kinga antin naki tace eh ya Fawaz Kuma Ina sonta tana da kyau yace ai Bata kaiki kyau ba ko tana dariya tace anty Wai haka daga kai saadatu tayi tace sosai kinfini kyau yasmeen ga sunanki suna mai dadi tana dariya tace yauwa ya Fawaz dazu mama tace  wai sai ta dinga musgunawa antinnan Kuma wai sai ta rabaku hade rai yayi yace yaushe ta fadamiki,dazu take fadawa anty momi Ina zaune shine suka koroni katseta saadatu tayi tace yasmeen bakyau mutum ya dinga gulma fa kinaso Allah ya Kona ki ne girgiza Kai tayi tana zaro ido to ki daina b kyau kinji gyada Kai kawai yasmeen tayi tace na daina anty yauwa kanwata ta kaina kallon Fawaz tayi taga ita yake kallo sunkuyar da kanta tayi sannan tace Dan Allah ka Ara min wayarka in Kira na'annan wayata ba kudi kallon mamaki yayi mata tareda faduwar gaba jin sunan da ta ambata yace no bara na tura miki kudin dai ki Kira tana zaune suka shigo tace nagode Allah ya Kara arxiki mai amfani yasa afi haka.

Kiran wayar na'annan tayi a ringing na biyu ta daga tace nayi fushi ba yini ba Kai amarya ko na'annan dariya tayi tace to ni ai bana Yar kunya da ke wake jin kunyar mamansa laaa to shikenan Zan shigo insha Allah in na fito Yana zaune Yana kallonta tana waya ganin tanayi cikin farin ciki abinda yake bashi mamaki Kuma maganarta ta karshe me take nufi da in ta fito bai gama magana ba sai kin anawa was kofar bugun masifa ko baiyi magana ba yasan wacece Amma mamakin sa shine wane tsautsayi ne ya kawota dakinsa har take wannan mummunan bugun katsewa saadatu tayi tare da mikewa daidai nan ya bude kofar fuskarsa a tamke bangajeshi maman tayi ta Shiga dakin.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now