Mr&Mrs Fawaz

19 6 1
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

44.

Kuka take Yi kamar ance Mata uwarta ta mutu ringing din wayarta ganin number din data kirata ne yasa ta dagawa,bayan sun gaisa tace meyasa kike kuka Kuma nan ta sanar da ita abinda ya faru itama nasiha tayi mata tare da nuna Mata hakan kaddararta ce ya kamata Kuma ta rungumi kaddararta da hannu biyu Koda da niyar cutar dake yayi wannan yunkurin to Allah bazai bashi dama ba tunda kikayiwa iyayenki biyayya nan dai tayi ta Mata nasiha kinga yayan naki ma Yana fushi dake Wai kin kwace masa fada daga zuwanki tana dariya tace ki bashi wayar karba yayi yace kin wani xo kin kwace min uwata ko tana dariya tace la ya fu'ad ai kaga Ina da farin jini daga haduwar da Bata wuce awa biyar ba tafi taku ta shekara da shekaru wooo nafika farin jini mikawa na'anna wayar yayi kawai baice Mata komai ba dariya na'anna tayi tace shikenan daughter Allah yasa hakan ne yafi alkhairi tace ameen na gode tare da ajje wayar.

Duniyar tunani ta fada Wai yau nice matar aure, auren ma Wanda nake tsoro yake Kuma bani tsoro akowane lokaci wayarta ce ta hau ringing tana dubawa taga Dr Azeema ce tadagawa tayi jikinta a sanyayye sannan ta gaishe ta kindawo gida kuwa a sanyayye saadatu tace eh na dawo ajiyar zuciya Azeema ta sauke tace nasan an sanar dake halin da ake ciki ko shiru saadatu tayi sai can tace game dame kenan,game da aurenki da Fawaz  eh an sanar Dani,yauwa to shine nace ya kamata ki tare a satinnan gobe zanzo zanyi wa umma bayani Dan munyi magana da daddy ma Amma meyasa ya Fawaz ya amince da aurena bayan kafin ta karasa Azeema ta katseta kinga saadatu Koma dai menene ki bar maganar nan aure dai an Riga an daura bazaa warwaresa ba gobe idan naxo zanyi wa umma bayanin komai kema ki kwantar da hankalinki kinji toh kawai saadatu tace sannan Azeema ta Dora shima Fawaz din baisan dawa aka daura masa aure ba Amma dai ya amince da hakan nan sukayi sallama ranar da kyar saadatu tayi bacci tana ta tunanin makomarta.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now