Mr &Mrs Fawaz

16 2 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

43.

Dakinsa suka shiga direct a zaune suka samesa da waya a hannunsa abdullahi yace aa Mai nagge ai na dauka zanxo na sameka a sume a daki yace saboda me fa dariya Deen yayi yace saboda anyi maka aure haderai yayi yace koma wacece ai ita ta kawo kanta Dan haka haka zatayi hakuri da duk wani abu da zata gani a gidannan kuwa,Fahad yace yanxu dai tsaida gininmu zamuyi a gama naka tukunna tunda Kai ka Riga da kayi auren ma maka masa hannu Fawaz yayi a cinya yace dady mantawa yayi tare mukaxo duniya shiyasa yayi min aure ni kadai duk dariya suka sa,zeema ya aka Kare da case din auren yarinyar can naga kamar an daura auren ko dariya abdullahi yayi yace ana maganar aurenka kana maganar auren wata can harararsa Fawaz yayi tare da mai da kallonsa gurin Azeema Yana jiran amsa eh an daura Amma badashi waccan din ba da wani ne daban wallahi ta bani tausayi sosai tana ganin mu'ujizozi iri iri.

Wane irin wan mahaifi ne da ita Mara Imani a zuciyarsa cewar Fawaz ai da ganinsa tun mahaifinta na raye ma bashi da mutunci abdullahi yace Wai akan was kuke magana nan Azeema ta basu labarin abinda ya faru ohh ke kika Kira daddy kenan cewar Fahad eh mana ai yanda naga Fawaz yana haki nasan zaa aikata ba dai dai ba ni kuwa ba iya tsayar dashi zanyi ba shiyasa na kirasa sai gashi kafinma ya karaso har kawun Bata yasha Mari dariya suka saka Amma bakada mutunci wlh Mai nagge cewar Deen ai ya bani haushi ne ita mahaifiyarta na kokarin Kare yarta shi Kuma a dole sai an fadi mummunar kalmar a kan yar shiyasa nayi hukunci nan dai sukayi Mata fatan alkhairi da fatan Allah yasa hakan ne yafi Zama alkhairi a rayuwarta.

Umma meyasa kika Bari aka aura min mutumin da bashi da kirki duk Yan uwansa sunfi sa mutunci fa Kuma sai ta kasa karasa maganar da tayi niyyar fada kallonta umman tayi tace ki karasa Mana mutumin da ya ceci rayuwarki daga halaka ai ba abin yarwa bane kafin ma umman ta karasa fadar abinda zata fada saadatu ta Mike ta shige daki taci kukanta ta gode Allah.

By Ayshart sani.
Wattpad @ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now