Mr & Mrs fawaz

5 1 0
                                    

Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0

By Ayshart sani

79.

Yace Abu guda daya yake damuna Wanda har a yanxu Bai hakura dashi ba bayan kadarorinmu, naanna tace meye shi ban fahimci abinda kake nufi ba yace dukiyar wani bawan Allah ce a gurina yace watarana munje wata unguwa Tarauni munyi gaisuwa muna tafiya Sai mukaga wani Mai kifi nayi shaawa nace mu siya Usman yace Kar mu siya na nuna masa nikam Zan siya Dan nayi shaawa ko ba komai ma kaiwa iyalanmu haka na karasa gurin Mai kifin na siya na fara tafiya Sai ya tsinci sisin gwal a cikin wani kifi da yake kokarin yankawa naji an kwala min Kira bawan Allah na juya ganin ni yake nufi Sai na koma bayan na koma gurin Sai ya nuna min wannan gwal din yace yaji har cikin ransa ya yarda Dani Dan haka Yana bukatar Dana siya in bashi dubu dari biyu,inata mamakin Dama ance masu kifi suna arziki in Allah yasa suna da rabo suna tsintar gwala gwalai,Ina wannan tunanin naji kalmar dubu dari biyu nace me zaiyi da dubu dari biyu Sai na bukaci da ya fadamin ganin dai na nuna mamaki Sai yace min yanaso ya siyi gidansu na gado ne nace Masa ai in dai siyar da wannan gwal din zaiyi a wannan lokacin da gwal yake da Dan kudi zaiyi dubu dari biyar Dan ba karamin gwal bane babbane Kuma yanayin sisi ne dashi Amma Mai kauri Kuma Yana da girma kyallinsa Kamar diamond yace to shi ya siyarmin akan naira dubu dari biyu da hamsin in basa kudin nace Masa aa a yanxu dai bani da kudinnan a hannuna Amma insha Allah ya ajje zanzo na karba na bude mota Naga Ina da dubu dari kasan cewar bana tafiya ba Yan kudi a aljihuna ko a cikin mota.

Haka na bashi dubu darin nace ya rike gold din in na ciko ragowar Zan karba yace aa shi ya bani duk sanda kudin Suka samu na kawo Masa in muna da Rai ya yarda Dani dari bisa dari ya nuna min gidansa inda yake xaune da matarsa da Kuma yarsa daya tilo ya Kuma Sanar dani sunansa malam daga gefe aka karasa malam aminu Mai kifi da sauri abbu ya kalleta yace ya akayi Kika sani tana kuka tace mahaifina ne shine mahaifina da Allah yayi Masa rasuwa gaba daya falon kallo ya koma kanta tace har abbana ya rasu Bai manta da Kai ba shekara ta goma da doriya da rasuwarsa,duk lokacin daya tunaka Sai yace yasan Allah ne Bai nufeka da dawowa ba akwai abinda ya faru ko Kuma Allah ya maka rasuwa,wannan kudin shine dalilin daina sanaar kifinsa Yake kaiwa wani kamfani suna yin na gwangwani ya zuba kudin a matsayin hannun jari,wata ranar laraba muna zaune a gida akayi Masa waya Akan ana nemansa a company y tashi ya tafi Akan hanyarsa yayi hatsari Allah yayi Masa rasuwa.

Gaba daya dakin aka hau fadin innalillahi wainna ilaihir rajiun Allah ubangiji yajikanka ya gafarta masa tace ameeen ya Allah abbu ya Dade Bai Kara cewa komai ba Dan yaji mutuwar malam aminu sosai,Sai can ya numfasa yace to Wannan gold din Usman yakeyiwa Dan a yanxu gold din zaiyi kimanin miliyoyin kudi Dan ba karami bane to Wannan ne musabbabin komai Dan n sanar da usman ba hakkina bane dole Zan nemi malam aminu in bashi kudinsa Amma nafison Sai na tambaya naji zaiyi nawa tukunna in bashi kwana 3 tsakani tafiya ta Abuja ya tashi lokacin safiyya Bata tare dani shiyasa bata da masaniya Dan ba dan sisin gwal din Nan ba Usman bazai min haka ba  wannan shine abinda ya faru Dani.

Ayshart sani.

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now