Mr & Mrs Fawaz

36 4 0
                                    

Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0

By Ayshart sani

20.

Tun daga kofar gidan zaka tabbatar da irin tashin hankalin da akeyi a gidan yadda kofar gidan ya dan cika ai azeema bata gama parking motar ba Saadatu ta fita da sauri dosar gidan tayi yara na ganinta suka ruga gidan suna ga saadatun nan ta dawo nan da nan hankalin mutanen gurin ya dawo kanta,shiga cikin gidan tayi su azeema ma na bin bayanta turus tayi a tsakar gidansu ganin kawunta bello da daya kanin mahaifin nasu suna fitowa da kayansu daga daki tsayawa tayi tana kare musu kallo daga baya tai karfin halin cewa umma meke faruwa.

Jin muryarta da sauri umman ta mike tace Saadatu ina kikaje tun jiya nake nemanki saboda rashin sanin in da kike ko bacci na Kasa yi,tana kuka tace umma mota ce ta bigeni sai da aka kaini asibiti tukunna katseta kawunta yayi dalla can rufe mana baki munafuka kin dai tafi yawon iskancinki sai yanxu zaki wani dawo kice mota ce ta bigeki to kuxo Ku bar gidannan tunda dama na gado ne aka barku kuke zaune tunda naga duk yawon iskancin naki baki Iya kin sai muku gurin zama ba, da kuka tace wlh kawu mota ce ta bigeni tsawa ya daka mata malama rufemin baki kun hada baki zaki wani yiwa mota karya, to daga yau zuwa gobe ki tabbatar da kun hada ina Ku ina Ku kun bar gidan nan dan sashi zanyi a kasuwa gwanda a siyar dashi kawai a raba gadon kowa ya huta  yana gama fadar haka ya juya ya fita shima kanin nasa ya bi bayansa.

Kuka Saadatu ta saka tace wlh umma banje ko ina ba mota ce ta bigeni kafin ma ta karasa saukar mari kawai taji a fuskar ta dafe kumatu tayi tana kuka azeema tace dan Allah umma kiyi hakuri wlh ni na bigeta cikin rashin sani  na dauketa na kaita asibiti aka rubuta magani da ruwa da allurai gashi bata cikin hayyacinta kuma ni bansan gidansu ba shiyasa ita kuma bata farka ba dan haka na wuce da ita gidan mu kawai ta nuna su fahad dake bayanta a tsaye tace tuni Dr deen yabi bayan su Kawu tun fitarsu dan yayi musu kallon yan tambayoyi.

By Ayshart sani
Wattpad@ Ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now