Mr&Mrs Fawaz

19 3 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

53.

Tana idarwa azkar tayi yana zaune Yana kallonta har gari y Dan waye tukunna ta Mike mikewa yayi yayi hanyar toilet ganin haka ta fito falo tana gyarawa tana yin hanyar kitchen Yana fitowa cikin shirinsa tsaf kallonta yayi yace na Dan fita yanxu Zan dawo tace toh Ina tsintsiya nuna Mata inda yake ajjewa yayi sannan ya fita a falo ya tadda Fahad suka dunguma kofar gida acan suka tarar da sauran har Azeema suka dunguma training center suna Dan gudu Azeema tace Fawaz Ina amarya? Tana lafiya abdullahi yace anya kuwa Dan wannan kyallin goshin da Alamar tambaya Deen yace ku barsa hakanan in tayi tsami maji ganin suna San bata masa rai kawai ya kyalesu yayi gaba abinsa,bayan fitarsa tea saadatu ta dafa tare da soya chips da ta gani a cikin kitchen din ta gyara ko Ina da Ina turaren wutar d aka kawo Mata shima ta saka daki ko Ina ya dau kamshi sannan ta Koma bathroom tayi wanka tana cikin shirya wa ya shigo allah ya taimaketa tasa kayanta da sauri ta dau dankwalinta zata daura Yana shigowa idonsa akanta yace waya gyara dakinnan ya tambaya Yana karewa dakin kallo ganin yayi masa kyau ga kamshi sai tashi yake tace nice ya gyada Kai ganin tana kokarin daura dankwali yce shi gashin kazanta ce ta hana a gyarashi ake kokarin kulleshi ya fada tare da shigewarsa toilet falo t Koma ta zauna ya Dan jima kadan sannan y fito kallonsa tayi tace ga abinci sosai yake mamakin maganarta abinci Kuma da sassafe tace tea ne da chips nayi gyada Kai yayi yace okay.

Waya ya dauka ya Kira fahad shigo muyi break kafin ka wuce okay to kayi sauri kasan bazan jiraka ba ko tareda kashewa kallonta yayi yace kixo ki diba Mana aa na koshi me kikaci ya tambaya tace aa banason tea ne yace sai me? Tace Koko Amma shima tea din inaso kawai bana Sha da yawa ne kafin yayi magana wayarta ta fara ringing hakan yasa ta Mike Dan duba Wanda ya kirata sunan umma ne ya bayyana a jiki.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh.

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now