Mr & Mrs Fawaz

20 4 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

57.

A tsakiyar kanta taji tsawarsa kar ki kuskura ki fita daga dakin nan shine kalmar data dakatar da ita takowa yayi har gabanta Yana Mata wani mugun kallo Ina zakije?ya fada idansa a kanta ya fawaz we don't have any other option to follow dole muyi biyayya ga magabatanmu kayi hakuri Dan Allah tayi sauri ta fice bangaje shi tayi gaba a bangarenta tai ta sata aiki tun tanayi cikin dadin Rai har ta gaji tun karfe kusan goma na safe har biyar na yamma ita tayi Mata gyaran bangarenta tas har dakin momy da yasmeen girki gyaran kitchen komai da komai tun Fawaz na kallon time daya fita sallar azahar wucewa yayi ya dan zagaya gari a kafa shi kadai bai dawo ba sai pass 5 Yana Shiga daki ya fara Kiran sunanta Jin shiru abin ya bashi mamaki sosai,bangaren maman ya shiga abinda bai taba Yi ba Ina saadatu shine abinda ya fara fada,banza tayi Masa ganin bazata tanka Saba yasa ya fara kwala Mata Kira sai gata ta fito gaba dayanta ta canja yanayi abin tausayi,sosai ta bashi tausayi riko hannunta yayi yace duk Randa kika sake kika Kara shigowa bangaren nan sai ranki ya baci wallahi,me kake nufi bazata Mana aiki ba komai kallonta yayi yace Ina Yar aikin gidan take taje hutu shine amsar data bashi ohh ita Kuma waccan fa tayi maka kama da yar aiki ne ohh ita wannan din kama tayi Miki da yar aiki,eh mana baka gani ba bai tanka Mata Jan hannun saadatu yayi sukayi gaba sai da suka je kofar dakin sannan ya juyo yace wlh duk Randa kika sake kika Kara sata aiki a gidan haduwarmu bazatayi kyau ba to ubana ai sai ka tsinemin ko tunda nasa uwata aiki gaba yayi ya barta tana ta faman yaba bakar magana da maganganu marasa dadi.

Direct daki yayi da ita toilet ya nuna Mata shigewa tayi wanka tayi tasaka doguwar riga sosai takejin yunwa a cikinta Dan ta galabaita sosai baga dayanta ta rasa me ma zatayi fitowa tayi yana zaune ya buga uban tagumi kallonta yayi yace kinci abinci Kai ta girgiza tare da yin hanyar kitchen din Ina Kuma Zaki Zan dora abinci ne tsaki yayi yace hado tea ki zauna Kisha ba sai kinyi girki ba zansa Fahad ya taho dashi kawai samu kici wani abin dai akwai abubuwa ki duba.

By Ayshart sani
WattpadAyshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now