Mr & Mrs Fawaz

18 2 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

63.

Sosai mama take mamakin saadatu ganin yau ba tsoro a tareda ita take fada Mata magana Fahad dake tsaye ya kasa magana sbd firgici yace kaf duniya Mara Imani ne kadai xai iya yin abinda wannan matar tayi gwanda dai ki kufada Mata tunda ita ba abinda ta sani,murmushi saadatu tayi me ciwo tace uwa uwace Koda kuwa uwar Zina tayi ta haifi mutum dole yayi biyayya ko yaki ko yaso muryar fu'ad ce ta katseta Yana saadatu na'anna,juyawa tayi ta ganta a kwance kamar matacciya ba tareda wani tunani ba ta riko hannun Fawaz tace you have to do something kallonta yayi yace I cant help a heartless women daidai shigowar su Dr deen tace ya Deen help her pls nan dai ya duba ta yace a maida ita guri Mai Iska kayan amfanin Fawaz saadatu ta dakko suka gwadata yace jininta ne ya hau daki Fawaz kawai yayi ya barsu a gurin ruwa da allura ya rubuta yace a siyo sai a saka mata karba dady yayi yace bara n karbo aa daddy bara na karbo cewar Deen ciccibarta fu'ad yayi saadatu tace shigo da ita nan dakinsu suka shiga dai dai nan fu'ad ya sauketa shikuma Yana bude toilet kallonsu yayi kawai ya karasa gurin drawer.

Sosai saadatu Tasha mamakin ganin irin decoration din da aka kawata dakinsu dashi da balloons da abubuwan decoration daga dama an makala HBD wifey sai duk jikinta ya Kara sanyi Amma hakanan ta dake abinta,a zaune Fawaz ya taradda fu'ad a falo,yace and you Kai ma ka yarda da ita kenan kallonsa yayi yace ni da dady mu kadai mukasan gaskiyar abinda ke faruwa tunda kunfi yarda dashi sai kaje ka tambayesa Dan ni ba Wanda ya Isa nayiwa mahaifiyata rashin kunya ba kamar Kai da kake kallonta kake fada Mata ka tsaneta ba,Fahad dake bakin Koda ya shigo yace Kai dama baka San komai ba you are little lokacin da abin ya faru so ba zaka San komai ba Fawaz da maganganun fu'ad suka gama Bata masa rai matsowa yayi gurin da sauri Fahad ya rike Masa hannun yace let him bro he's your little bro so baisan komai ba sai abinda aka Dora da akai kawai,saadatu dake bakin kofa tace  ya Fahad.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now