Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9By Ayshart sani
70.
Matar Usman mahaifiyar Azeema Bata haihu ba sai da suka shekara hudu tukunna kasancewarsa maza hakan yasa suke sonta suka Koma komai ma tare sukeyi kusan tare aka haifi Azeema da momi Dan ku kuka rada Mata sunan Dan asalin sunanta afrah ne kuke ce mata momi tun safiyya na dukanku har ta hakura itama ta maida sunan nata haka Dan mukhtar yace a barta a momi din haka kuke rayuwa yau kuna nan gidan gobe kuna can bayan kusan shekara biyu lokacin Ina da tsohon cikin fu'ad a lokacin aka fara blackmailing Dina a farko nayi burus da maganar Dan ban dauki maganar da gaske ba, abinda aka cemin kuwa shine in rabu da yayana da mijina hakan yasa nayi watsi da abin sai Naga duk abinda wannan blackmailer din ya fada min Yana tabbata hakan yasa na fara gasgata maganar da domin kuwa ya gargadeni akan mijina zaiyi hatsari in har ban rabu dashi ba Kuma hakan ya faru dake akwai kwanansa a gaba haka Allah ya bashi lafiya bayan komawarsa kasuwa baa jima ba ya Kuma gargadata akan zaa damfari mijina sai gashi an danfari aliyu kudin bar naira miliyan biyu bayan nan ya sanar dani xai kashe mijina da yayana da duk Wanda xai bashi matsala gurin aiwatar da kudirinsa Jin haka yasa na amince akan Zan barku Amma idan na haihu bazan iya tafiya da ciki ba bansani ba ko Zan rayu hakan yasa na cigaba da Zama har na haifi fu'ad Wanda bayan haihuwarsa ma ban tafi ba sai daya dawo ya Kuma tsiratar Dani da hada Mana gobarar da dakyar muka tsira..
Hakan yasa bayan komai ya lafa na siyi gida a nan cikin tarauni ba tareda sanin aliyun ba sai dai na sanar da mukhtar daga baya Amma da sharadin tareda alkawarin bazai sanar da kowa ba da farko yaki amincewa sai dana sanar dashi dalilina na hakan daga baya a amince kafin na bar gidan sai Dana tabbatar da aliyu yayi min signing duk wani documents da makudan kudade da wasu abubuwansa yayi signing akan ya mallakawa yayansa Yan biyu da kuma fu'ad tukunna na bar gidan nan Wanda dukiyarku ce nake juyawa nake yi muku duk wasu abubuwan rayuwar domin duk wani motsinku Ina sane dashi nasan komai dakuke ciki Wanda mukhtar ke sanar dani har lokacin da Allah yayiwa mijina rasuwa.
By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

YOU ARE READING
Mr&Mrs Fawaz
Romancethis story is about 5goods friends that can sacrifices their happiness for there beloving once.