Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9By Ayshart sani
30.
Cikin zuciyar dady baya fahimtar abinda suke fada ya dai amsa musu ne kawai dan suma suna son lafiyar Fawaz din,tun ana mintuna har aka tafi awanni saadatu taga abin ma karewa bane duk da ranar tana da off a asibiti bata da aiki amma duk da haka ta kasa Zama saboda ummanta ta Kira wayarta Kuma a kashe,matsawa tayi kusa da Azeema tace likita ni Zan tafi gida dare ya fara yi tara ta wuce.
Azeema tace ki bari a fito dashi sai a kaiki gida kinji murmushi saadatu tayi tace don't worry likita I can manage Dr deen ya matso yace bara inyi dropping dinki ,Azeema tace shikenan ma dr Deen zai Kai ki nan y matsa y karbi key suka fita.A mota ba Wanda ya iya yin magana sai da sukai tafiya mai nisa tukunna ta iya bude baki tace likita dama haka yake suffering da heart failure yace eh saadatu haka yake fama Amma shi kullum in zaka basa shawara sai ya nuna maka ba haka bane shi lafiyrsa kalau Amma duk lokacin da aka bata masa rai to fa sai ciwon sa ya tashi haka zaiyi ta fama da mamaki tace to me ya faru dashi har ciwon nan ya sameshi rashin mahaifiyarsu shine amsar da Dr deen ya Bata,shiru ta danyi sai Kuma daga baya tace Amma ni Ina ganin rashin mahaifa bazaisa Dan Adam kamuwa da irin wannan ciwon ba,na yarda rashin iyaye Yana da illa a rayuwa sosai amma rashinsu wani darasi ne na rayuwa Wanda ba kowane zai fahimci hakan ba sai Wanda abin ya faru a kansa dariya Dr deen yayi yace saadatu bazaki gane binda nake nufi ba Amma ki sani cuta Allah ne yake jarabtar bawansa da ita Amma komai Yana da sanadi to shi Fawaz sanadin tasa cutar mahaifiyarsu ce shiru saadatu tayi ta kasa cewa komai.
By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

YOU ARE READING
Mr&Mrs Fawaz
Romancethis story is about 5goods friends that can sacrifices their happiness for there beloving once.