Mr & Mrs Fawaz

26 5 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

24.

Dariya Yusuf din yayi yace Azeema sai yaushe zaki gane Ina sonki naga gaba daya hankalinki baya kaina kallonsa takeyi cikin mamaki zatayi magana taji Fahad yace chill bro in dai zeema ce tana sonka kawai dai tana bukatar time ne kallonsa yayi yace time fa kake fadi wani time Banda Wanda na bata Fawaz da baya bukatar yawan maganar Yusuf ne yace Azeema tana bukatar lokacine Dan ta duba taga wane irin decision xata dauka don't worry zamu taimaka gurin sanar da Kai da wuri kar ka damu, kallon su Azeema tayi tace so you choose Yusuf instead of me,murmushi Fawaz yayi ya bar gurin nan su Kuma suka cigaba da tattaunawa.

     Tafiyarsu Azeema ce ta bawa saadatu damar fitowa tsakar gida kusa da umma ta zauna tana bawa umma hakuri tare da Kara jaddadawa umma abinda ya faru ba tare da bata lokaci ba umma tayi mata fada tare da nasiha umma tace ya kamata mu bar gidan nan mariya dake zaune a gefe tace umma Ina zamuje murmushi umman tayi tace nima bansani ba auta Allah Yana tare damu da kawonku ya dawo ya Kara mana korar Kare gwanda mu yafi Koma Ina me to umma makaranta fa cewar auta shiru umman tayi saadatu Banda kuka ba abinda takeyi.

Wayarta ce ta hau ringing ta dauka number ce Dan haka sai da ta katse aka sake Kira tukunna ta dauka Azeema ce tace sis saada nice tace au Dr Azeema Ina yini ya kukaje gida nan dai suka Kara gaisawa tace yauwa dama Cha nayi karku daga hankalinku ku maida kayayyakinku in da suke ku cigaba da zamanku zamuyi magana da kawun naku cikin rashin fahimta tace to likita na gode.

Bayan ta sauke wayar ta sanar da umma abinda azeeman tace da mamki umma tace kar ta sa kanta a abinda xata cutu fa.

Ayshat sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now