Mr & Mrs Fawaz

18 6 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

40.

Ganin ba abinda ya Sami saadatu sai kujewa a kafa da hannu yasa ta dauketa ta sata a mota asibiti ta kaita aka dudduba ta akayi Mata dressing haka matar ta dakko ta tare da tambayarta inda zata ganin Bata dawo dai dai ba yasa t kaita gidanta dan ta huta bayan allurar da akyiwa saadatu ta saketa ta tambayeta meya fito da ita haka har zata Yi Mata karya sai Kuma ta fada Mata gaskiyar abinda ke faruwa shiru matar tayi tace kyalesu kiyi zamanki anan nima nini kadai ce daga ni sai Dana guda daya fu'ad.

Bayan azahar sai yan daurin aure suka garzayo lokacin Azeema da Fawaz suna tare da umma da mai unguwa da wasu manyan mutane a layin wadanda umma ta sanar dasu abinda ke faruwa bayan kawu Bello ya shigo cikin gidan kallonsa me unguwa yayi cikin takaici yace to malam Bello ai sai ka zauna muyi magana Dan yarinya dai Bata gidannan ta bar gidan cikin isa yace ko tana nan ko Bata nan aure sai an daura shi text Azeema tayi wa daddy tare da tura masa address din gidan mintuna da basu wuce goma ba dady ya shigo layin kasancewar Azeema tayi masa bayanin kadan daga abinda ke faruwa Yana zuwa ganin yanda Fawaz yake huci yasa yakamasa ya sashi a mota sannan y dawo gidan Dan Fawaz har Marin kawu Bello yayi saboda Yana fadawa umma magana bayan dawowar dady Azeema ta fada masa shi kansa yayi mamaki sosai Dan haka ya Kira mai unguwa gefe yace shi Yana so a bawa dansa auren saadatu idan har sun amince.

Mai unguwa yayi murna Amma yace dole sai da amincewar mahaifiyarta tukunna umma ta amince d maganar Dan da a daura yarta sagir gwanda Koma waye a aura Mata bare wannan da ya nuna ita din uwa ce Dan haka ta yarda da kaddara haka Allah ya kaddara musu bayan kawu Bello yaji maganar masifa ya hauyi shi bai amince ba sai dai suje can gida su zabi wata ai tana da kanne sai da daddy ya tsawatar tukunna Dan har Yan sanda aka kawo ana daura auren kuwa ya Mike yace ba ruwansa dasu sun cire au daga cikinsu suje su nemi wasu Yan uwan Amma basu ba.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now