Mr&Mrs Fawaz

22 5 0
                                    

Mr & Mrs Fawaz
❣️❣️❣️❣️❣️
https://my.w.tt/vEDm5wvXQ9

By Ayshart sani

48.

Kallon Azeema saadatu tayi tace ni yanxu bansan makomar aurena ba,ni dai nasan banason sa Amma tunda ya kasance miji a gareni dole nayi masa biyayya,amma ya kamata ace ko sannin wadda aka aura masa yayi shi auren ma kamar baya gabansa,murmushi Azeema tayi tace ko wane Dan Adam akwai kaddarar da Allah ya Dora masa taku kaddarar hka take zance siyayya Kuma ai ta Kare kowane Dan Adam da kike gani daga lokacin da aka daura aurensu akwai wata bishiyar siyayya da ubangiji ya ke dasa musu hade da Kaunar juna da tausayi su ma'auratan ne zasu taimaka gurin yaduwar wannan bishiya Wanda kuma Ina da yakinin Zaki taimaka gurin koyawa Fawaz maanar siyayya Dan baisanta ba kallon Azeema saadatu tayi tace nima ai bansanta ba zaki gane manufata anan gaba kowace da yadda Allah ya yi ta kar ki damu.

Yauwa in kinshiga ki fadawa umma dady yace Zaki tare karshen watannan kar ta siya Miki ko chokali ya Riga yayi Miki komai to kawai saadatu tace Dan ita kam an sata a duhu fita tayi daga motar ta Shiga gida biyo bayanta Azeema tayi tace umma gata na dawo Miki da ita to umma tace angode saadatu ga sakonki inji maigidanki yace a Baki kamar bazata karba ba sai Kuma ta Mika hannu ta karba tare da shigewa daki abinta fita Azeema tayi bayan ta sanar da umma sakon dady.

Ba karamin gyara umma tasa akayiwa saadatu ba Wanda in ka ganta in ba Wai ka Santa bane bazaka ganeta ba Yan gurin aikinsu suyi ta tsokanarta su Dr deen sunso ayi ko Yar dinner ne Amma Fawaz yace shidai aa suyi musu addua kawai Amma duk da haka sai da Fahad ya hadamusu Yar walima suka gayyato abokansu Fawaz yaji haushi sosai kamar kar ya tsaya dai Kuma ya tsaya,umma ma tayi yini a gidanta baa karamin kudi aka kashe ba su Dr Fahad anyi kokarin Dan lemuka da ruwa duk na roba suka kawo wa umma abinci ma sawa akayi akayi aka kaiwa umma haka Yan uwa suka xo aka Sha biki.

Su Dr deen aka xo daukar amarya mutane sunyiwa umma Kara sosai bayan an shigar da saadatu gurin mama an danka Mata Amana sai cewa tayi Amana ai mijin yarinya ita dai kawai yarinya tayi biyayya.

By Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now