Kainuwa.......1

23.5K 1K 71
                                    

🕊 *KAINUWA* 🕊
_........Dashen Allah_

*Haske Writer's Association*

*Na Ayusher Muhd🤸🏻‍♂*

*Bismillahi Rahmani Rahim*

_All character and event in these novel are Fiction_
May Allah guide us through the right path (Ameen).

_Godiya ta musaman ga masoyana, ina godiya da alfahari daku nagode kwarai da gaske._

*1*

*Shekara ta 1970*

Gidan ya cika taf da mutane duk inda ka duba wasa ake yi, wasu na wasan dokuna wasu na wasan shad'i wasu busa suke yi, wasu waka suke yi, haka wasu wasan kidan kalangu sukeyi.

Hidima dai kala kala irin ta wasan ninmu na hausa na da, kowa ka gani fuskar nan tasa a washe take alamar tsantsan farin ciki.

Bayi sai murna sukeyi dan irin wannan sha'ani shi ke sa su su fito haka, maroka sai tasu hidimar suke yi.

Gidan sarauta na kasar zazzau kenan wato Zariya.

Zazzau na daya daga cikin manyan masarautu a Najeriya. Masarautar taci kasashe da dama da yaki, Girman kasar Zazzau ada ta kai har Suleja a Jahar Niger.

Masarautar Zazzau ita ce tafi kowace masarauta a yankin Afrika ta yamma yawan makarantun zamani da na addini, shiya sa ma ake mata taken Zazzau, birnin Ilimi.

Zazzau yana d'aya daga cikin Hausa bakwai wanda Bayajidda ya kafa, gari ne na sarauta.

A wannan shekara ta Alif dubu d'aya da d'ari tara da saba'in karni ne na sarautar Abdulsamad wanda ya kasance d'a ne ga sarki AbdulJalal wanda ya mulki kasar shima daga gun mahaifinsa.

Abdulsamad yana shekara 20 kacal aka daura shi akan mulki sakamakon rasuwar mahaifinsa, suna da yawa a gun mahaifinsu sai dai shine ya kasance d'an sarauniya Kubra sannan yaro ne mai hankali da ilimi hakan yasa mahaifinsa ya bada wasiyyar shi yakeso a nad'a.

An aura ma Abdulsamad mata a wannan lokacin wace ta kasance 'ya ce ga waziri wato " Safina" wacce ta kasance tun tana yar shekara uku mahaifinta ya bada umarni a koyar da ita tarbiya ta matan sarki, hakan yasa ta taso mace mai tsauri da tsananin jan aji, abinda zai baka mamaki ko Abdulsamad sai ya sara mata a gun ji da kai da mulki.

Safina ta auri Abdulsamad tana yar shekara 15, wacce aka nad'a a matsayin sarauniya, ta kuma bada umarnin a dinga kiranta da *MAGAJIYA*.

Yayanta Hisham shine ya gaji mahaifinsu, wanda aka nad'a sarautar waziri.

Auran Abdulsamad da Safina babu soyayya a ciki sam aurene na umarni, sai dai ita dama Magajiya sam babu soyayya a tsarin rayuwarta abu d'aya aka nuna mata ta auri sarki ta haifar masa d'a wanda zai gajeshi, itadai d'anta kuma jininta ya zama Sarki.

Wannan shine abinda iyayenta suka daura ta akai.

A wannan lokacin shekarar Sarki Abdulsamad da Magajiya 20 da aure sai dai har yanzu Allah bai azurtasu da haihuwa ba.

Sarki ya cike mata 4 sannan yana da kwarkwara 9 amma har yanzu ba labarin ko da batan wata.

Wannan abu na matukar damun Sarki da Magajiya, tayi magani harta gaji har yanzu babu labari.

Sai dai alwashi ne tasha babu mai haifar ma Abdulsamad magaji sai ita in har ba ita ba kuwa to lalai bataga wacce ta isa ba.

_Wannan kenan_

Kwatsam Magajiya ta fara abin laulayi haka kuma tace ai likita ya bata umarnin zama a d'aki ba tare da fita ba har sai ta sauka, sannan ya hana mijinta kusantarta saboda mahaifarta batada karfi.

KAINUWA....Where stories live. Discover now