Kainuwa....37

5.9K 475 48
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*37*

Sun isa asibiti Doctor Jamil wanda ya kasance director ne a wannan asibiti, matsayi da girmansa yasa mutane suke karramashi dayawa, sannan ga kokarin yin aiki da kyautatama wanda bashi dashi.
Kafin su isa dama Sarki ya sanar dashi komai hakan yasa suna isa wani yaransa yazo ya kaisu wani d'aki, wanda yasa aka kamashi domin su.
D'aki ne babba gani matsayi da mukamin wanda zai zauna a d'akin, Dr Jamil da kansa yazo, bayan sun gaisane ya nemi keb'ewa da Abu Turab, hakan yasa Basira da Lantana suka koma gida tunda akwai masu kula dashi.
Dr Jamil ne ya kalli Abu Turab yace " Yarima ni kaina nayi mamakin jin abinda ya faru, dan mun taba had'uwa dakai lokacin bakafi shekara 13 ba, sosai na d'auka baka gani."
Abu Turab ya d'an murmusa yace " ya fad'ama komai kenan?"

Murmushi yai sannan ya matso tare da nad'o wani abu kamar kyale yace " sry fa zaka zama makaho na kwana biyu."
Ban fahimta ba?
" zamu kula da kai zuwa gobe, sai muce an maka aikin gobe, sannan mu rufe idanuwanka na zummar mun maka aiki, zamu jira zuwa awa 24 sannan mu duba muga ko an samu cigaba, kaga a kalla xamu kai zuwa kwana biyu saboda kar mutane su fahimta, in mun since sai kuma ka jira ko da kwana 3 zuwa hudu ne sannan mu sallameka."

Abu Turab ya jinjina kai sannan yace "Na fahimta na kuma gode sosai, Allah ya saka da alkairi."

Kafadarsa ya dafa sannan yace " Karka damu, d'a kake a gurina abinda zan maka banaji ma zan wa nawa 'ya'yan domin Abdussamad ya taimakeni dan shine silar zamana duk abinda na zama a yanzu."

Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Dr Jamil yace " duk abinda kake bukata ka fito ka sanar dani, kaji?"
Abu Turab yai murmushi sannan ya d'aga kai alamar to.

Zarya kawai take a cikin d'akinsu, hankalinta ya gaza kwanciya sam, ganin ba haza ga yamma tayi ta jawo hijab dinta ta fito da sauri.
Tana kokarin fita Mahaifiyarta na kawo kai.
Tsayawa tai, Ummanta ta kalleta tace " Khadija ina kuma zaki?"
Bakinta ta d'an motsa kamar zatai magana sai dai bata ce komai ba.

Kallanta ta karayi tace " dama fad'amiki xanyi yanzu mahaifinki ya dawo yace in sanar dake Saifullahi yazo yana gun Magajiya, nan kuma bayan Magrib zai shigo."

Gabanta ne ya fadi dan ita sam ta manta da wani Saif da ake san bata.
Ta kalli Umma tace " Umma nifa na d'auka an bar maganar nan."
Ambar maganar kamar ya kenan? Khadija wai me kika d'auki maganar mahaifinki ne?

Kasa tai dakai sannan tace " naji Umma kiyi hakuri amma dan Allah yanxo zan d'an fita kadan ba dadewa zanyi ba."

Ina zaki?
Yanzu zan dawo nan kasan layi zani.
Umma tace " kinga dai magrib ta kawo kai karki dade.

Da sauri ta wuce ta a tafe tana amsa wa da to.

*******

A bakin asibitin ta sauka ta fito ta shiga ciki, tsayawa tai tana tunani inda zata nufa, Allah ne ya taimaketa ta hango Garzali.

Da sauri ta karasa gunsa, shikuma lokacin yana kokarin komawa ne dan yaje gida d'auko wani sako da Abu Turab ya aikeshi.

Sai data kusa isa tad'an kwalla mai kira, juyowa yai yana ganin itace ya karaso da sauri sannan ya gaisheta.

Amsawa tai sannan ta d'ora da cewa " ina akwma kwantar da Yaya? Muje ka nunamin."

Garzali yace " to ranki ya dade."

Nan yai gaba ita kuma tana binshi .

Sunyi tafiya mai d'an tsawo kafin su isa d'akin.
Nan yai sallama ya shiga tare da ajiye mai ledar aiken, Abu Turab ya kalleshi zaiyi magana ya hangota tsaye a jikin kofa.

D'auke kansa yai daga inda take yace "Garzali kai ne? Har ka dawo?"

" Nadawo Ranka ya dade, sai dai bani kadai bace."

Zai sake magana Abu Turab yace " karka damu jeka."

Garzali ya fita daga d'akin.

Tana tsaye a kofar, gani tai ya koma ya kwanta.

A hankali tasa kafarta cikin d'akin, sai dataje kusa dashi ta bayansa ta kuramai ido cikin sanyin murya tace " Yaya ina wuni?"

Shiru yai baice komai ba, zama tai a kujerar dake jikin gadon da alama wani ne ya jawota ya zauna agun, kallansa tai bayan ta zauna ta sa hannunyenta kan gadon tana wasa da hannu a hankali ta ce " Yaya ina cikin wani hali, duk duniya kai kadai ne nakejin zan iya sanar mawa, na rasa yanda zanyi, ina tsoro abubuwa guda uku."

Shiru tai kafin tai ajiyar xuciya ta cigaba " ina tsoron Abbana da Umma Magajiya dan na tabbata ba tun yanzu ba suke aikata laifi, na biyu ina tsoron kar a cutar dakai."

Shiru tad'an sakeyi tad'an furzar da iska sannan tace " yaya, bansan ya zanyi ba da alama maganar Saif tananan, ni kuma......"

Kasa karasawa tai saboda zuciyarta dataji tayi rauni.

Abu Turab yana jinta har kuma zuciyarsa yakejin kalamanta.

Hawayen dayad'an ziraro mata ta goge, tai murmushi sannan tace " Yaya sai dai akwai wani abu da yake sani farin ciki, inajin dadi sosai da wannan aikin da za'ama, na rasa meyasa inaji a jikina lokacin ganinka yayi, sannan inhar kana gani ina ganin ba yanda su Abba zasuyi."

Murmushin yake ta sake yi tace " Kayi hakuri na takurama da nakeyi, na sani yanzu bakasan kula ni."
Ta mike jiki a sanyaye tace " Yaya inaso kasa abu d'aya a ranka, wlh wlh ni bazan taba cutar dakai ba bama kaiba, bana fata in cutar da kowani mutum a duniya, ko da kuwa a rashin sani ne."

Juyawa tai xata tafi, dan dama wannan amsar itace wacce ta dade tanasan ta bashi, tayaya yaya zai dubeta yace mata wai itama tana da tabbas din bazata cuce shi ba?"

Sai datakai kofa ta juyo tace " Allah ya baka lafiya Yaya."

Nan ta juya tai gaba, juyowa yai da sauri ya kalleta, bayanta ya kalla lokacin data rufe kofar.
Idanunsa ya runtse sannan yad'an had'a lab'ansa.

Ba shakka sai ya jure sosai, dan a lokacin datake magana jiyai kamar ya juyo ya lalasheta, Saif? Saifullahi? Wa kenan?"

Tunowa yai da abinda Mahaifinta ya musu, kwafa yai sannan ya juya.

Itakam tana fita ana kiran sallar magrib.

A can gida kuwa sai nemanta akeyi dan kuwa Saif kafin ai sallah ya iso,anan sukai sallar Magriba, sai dai shiru ba Khadija.

Hankalin Waziri da Mahaifiyarta ya tashi sosai.

Nan yasa aka fito dan nemanta.

Saifullahi yaro ne ga Senate Kassim, 'yan siyasa ne sannan bayan siyasa sun gaji kudi.

******,*

Mairo kuwa da yamma itama ta shirya fes dan zuwa gun Abu Turab saboda shi yace mata tazo akwai maganar da zasuyi.

Ta fito zata fito ta gami dashi a zaune a ciki motarsa a kofar gidansu.

Yi tai kamar bata ganshi ba xata wuce, Abdulmajid ya fito daga motar xai nufota, da sauri ta koma ciki.

Komawa yai ya xauna a saman mota dan jiranta, Mairo kam tana shiga ciki ta dafa kirjinta tace " nikam wannan akwai dan masifa, na tabbata kuma tsabar rainin hankali ne ke damunsa wlh ba so ba, wannan wani irin rainin hankali ne.

Itakam tsoronta d'aya shine karta fita tana mai magana Mahaifinta ko wani ya gansu a sanar mai.

Dole ta koma ciki fitar da batai ba kenan.



*ABU TURAB TEAM🤝🏻*

KAINUWA....Where stories live. Discover now