Kainuwa.......5

7K 524 26
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂*

_Alhamdulila an gama *Nayi Nadama* da *Hamal* Allah ya kara Baseera (Ameen) ni da ragowa 'yan kungiyar Haske na muku bangajiya, Allah ya kare mana ku😍_

*5*

Ganin yanda takeyi yasa Magajiya tace a maidata b'angarenta, nan kowa ya mike ya fita sakamakon sallamarsu da tai.

Suna fita ta aika a kira mata yayanta Hisham, bai dade ba ya shigo nan ta sanar dashi komai sannan ta d'aura da cewa " yanzu in Mai Martaba ya tambayeta ta fadamai tirsasata nai zaiyi zargin wani abu kasan halinsa sarai."

Hisham yai shiru sannan ya ce " bari na kira mai magani ya dubata."

Wani mugun kallo ta bugamai wanda yasa yace " tuba nake ashe fa babu namijin da ya isa shiga b'angaren matan sarki ba tare da izini ba ko an sanshi ba."

Kanta ta d'auke daga inda yake tace " Ka fad'ama Turaki ya tambayar mana kaninsa ko akwai maganin da zai warkar da ciwon tunda naga kanin nasa yasan kan magani."

Nan ya amsa da to sannan ta kara kallansa zatai magana yai saurin cewa "na fahimci komai kinaso kice shi Turakin ya rike maganar a sirri."

Murmusawa tai kad'an sannan ta juya kai.

Hisham ya mike ya fito yana fita waje yai d'an kwafa tare da kallan inda ya fito sannan yai gaba.

Basira kam kwanciya tai ta shiga bargo saboda sanyin dake ratsata itakam batasan gidan nan sam ita duk rayuwarma ba dadi take mata ba inta itace har gwara can inda ta fara zama akan nan dan a kalla a can gidan bayi insuna hira suna sata dariya amma nan kam tanaji tunda ta shigo haryau batai dariya ba.

Tana nan kwance aka aiko mata da magani, ko kallan maganin batai ba dan itakam ta sab ciwonta inta kwana washe gari zai baje.

Bayan tayi isha'i ne wasu bayi suka shigo suka tsaya a inda take, babbar cikinsu wacce suka zauna da ita a can ne, ta matso kusa da Basira tace "Ranki ya dade wanka zaki tashi kiyi."

Basira batai musu ba ta mike saboda a can an sanar da ita yin musu laifi ne kuma yana jawo a rage ganin girmanta.

Ban d'aki ta wuce, ruwan zafi ne aka saka a katan baho an saka abubuwan kanshi kala kala, kina shiga b'an d'aki wani dadad'an kamshi ne zai bugeki, nan ta sata a ruwan zafin.

Bayan sun gama wankan ne suka bata wasu kaya masu kyaubta saka sannan wannan matar ta miko mata wani ruwa a kofi ba musu ta amsa ta shanyi, maganin ba dadi bata koma san dame akayishi ba sai dai tasan akwai zuma a ciki.

Tana gama shiryawa wata mata ta shigo mai d'an jiki haka, tana shigowa suka gaisheta jin suna cewa Jakadiya yasa ta fahimci wacece.

Jakadiya ta kalleta sannan ta gaisheta tace "Ranki ya dade muje ko?"

Basira batai musu ha tabi bayanta.

Sun d'anyi tafiya kad'an kafin su shiga wani b'angare, sosai an tsara b'angaren gashi kato ita da tana tunanin b'angaren Magajiya yafi kyau sai dai yau ta gane wannan yafi, ga girma ga kyau,kofar wani d'aki suka isa sannan Jakadiya ta kwankwasa, daga ciki akace shigo.

Jakadiya ta kalli Basira nan Basira ta shiga dan ta gane hakan ake nufi.

Katon d'aki ne sosai ganinsa yasa tai saurin maida kanta kasa, murmushi ya saki sannan yace " Amarya karaso mana."

A hankali Basira ta karasa inda yake ta tsugunna nesa dashi sannan tace "Barka da dare."

Alama ya mata da hannu akan ta matso kusa dashi, idanu ta d'an zaro kad'an tana tsoron kar ta matsa ya kula da bakinta da ya ke ciki da kuraje har kan d'an leb'enta.

KAINUWA....Where stories live. Discover now