Kainuwa.....58

6.9K 512 39
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*58*

Duk yanda Magajiya tai akan samun mafita ta kasa, da sassafe kuwa ta aika akan a kira mata Hisham.
Ko gaisuwarsa bata amsa ba tace " Yaya inaji fa yaran can yasan wani abu namu."
Gabansa ne ya fad'i kallanta yai sannan ya tuna kawo Khadija gida da yai, ba dai wani abu ta fada mai ba?
Daurewa yai yace " bangane ba? Me ya sani?"
Ta girgiza kai tace ban sani ba sai dai daga yanda yazomin da kuma yanayin kalamansa inada tabbacin yasan wani abu wanda yafi fyaden da akama Basira."
Hisham ya sauke ajiyar zuciya jin da alama ba Khadija bace yace " amma kinsan yaran nan shegen yaro ne anya ba dan karkiyima Mahaifiyarsa wani abu bane?"

Magajiya ta girgiza kai cikin yanayin tunani tace " Yaya bakaga idanun yaran nan ba alokacin, sannan cemin fa yai in fara hada kayan lefensa yaban zuwa sati biyu, kamar ni dan karamin yaron da ko uwarsa na girma yazomin da zancen rainin hankali irin wannan?"

Hisham shi kansa yayi mamakin jin haka yace " da kuma bakinsa ya fad'a miki hakan?"
Tace " anan gun kuwa, sannan harda cemin in sa Abdulmajid ya janye auren Mairo, umarni fa yazo ya bani wanda ko ubansa bai taba ban umarni akan abinda yasan ina duk wani abu na ganin na hana wannan abun."

Hisham yace " da alama yasan wani abun to amma ta yaya?"
Magajiya ta juya kai tace " wannan shine abinda ke damuna."
Shiru sukai kafin can ta kalleshi tace " Yaya"
Kallanta yai yace " ya zakiyi?"
Murmushi ta saki tace " kamar ni? Abinda yafi damuna kenan dan jiya ko baccin kirki ban samu ba, kamar ni Magajiya ace wannan yaran zai kalla ya bani umarni?"
Hisham a ransa yace " an tabo Masifa."
Magajiya ta kalleshi cikin iza tace " zanyi abinda yace bayan na tabbatar da akwai sirri na a hannunsa, zanyi lefe zan kuma sa a sa rana, zan nuna ma jama'a Turab ma d'anane."
Hisham cikin tsananin tsoro ya kalleta dan ya tabbata wank mugun abun zata fada daga karshen abin arzikin datai, dan yasanta haka take in har aka bata mata rai sai ta nuna bakomai Sai kuma tayi abinda baki bazai fadu ba.

Magajiya ta kara wani murmushin jin dadi tace "Aure? Auren Bilkisu?" sai kuma ta sa dariya tace " lalai nayi gangancin barinka da rai."
Hisham ya kalleta yace " me kike tunanin yi?"
Kallansa tai sannan ta wani juya ido tace " sai muga ranar auransa waye zai je gun, mai makon kaga ai aure da shi a d'aura da Abdulmajid sannan su gama d'aura aure suzo su tadda angon da aka shirya za'ai dashi a kwance ba numfashi."

Hisham ya kalleta yace " ban fahimceki ba....."
Tace "Zaka fahimceni, dan kuwa kaine zakasa a kamashi a hanyarsa ta zuwa d'aurin auran, sannan musa abokinsa dole ya sanar akan bazai samu zuwa ba dan shi ba auran yake so ba, kaga ran Sarki zai b'aci matuka ya aura ma Abdulmajid Bilkisu sannan mai makon mu sakeshi lafiya sai mu juya abin a matsayin 'yan fashi ko kuma hatsarin mota, kaga mun jefi tsuntsu biyo da dutse d'aya."

Mamaki ya hana Hisham magana kawai kallanta yakeyi.
Kallansa tai tace " ya? Wasan nawa ya had'u?"

Idanunta ya kalla yace " Magajiya kenan, duk duniya Allah bai taba hadani da mai kaifin basira irinki ba, da ace Basirarki a abu mai kyau kike sa ta lalai da ancigaba a gidan nan."
Harara ta makamai tace " mai kake nufi?"
Jinjina ya mata da hannu yace " komai yayi nake nufi."
Tace " Uwata fa?"
Sai daya had'iyi yawo yace " tana gida ba lafiya."
Cikin kulawa tace " da alama sam yaya baka kula da Khadija, inaji zan dawo da ita gabana har tai aure, munyi magana da Mahaifin Saifullahi yace tunda yara sun daidaita zasu kawo kudi."
Hisham yai murmushi yace "Allah ya kaimu."
Kallansa ta kuma yi tace " Ya ake ciki a fada akan maganar auran Abdulmajid da wannan sakaryar?"
Hisham yai tsaki yace " kwana biyu dai anyi shiru da maganar dama Galadima ne uban san kawo maganar da Turaki."
Magajiya tai shiru kafin tace " Gun Abu Turab zani yanzun nan dan in tabbatar da abinda yake dashi."
Hisham ya kalleta yace " da kanki zaki? Ba gwara ki aika yazo ba?"
Murmushun jin dadi tai tace " ai tun yanzu za'a kulla abotar d'a da uwa saboda gudun zargi da zai biyu baya."
Kallanta yai sannan yai kasa dakai.
Mikewa tai ta fita sannan shima ya fito.

KAINUWA....Where stories live. Discover now