Kainuwa......6

6.9K 537 12
                                    

KAINUWA
......... _Dashen Allah
(A Historical Fiction)

HASKE WRITERS ASSOCIATION

Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂

_Where are u My Dear BillynAbdul? Here is ur special page, tnx for the care Tawan. Allah ya bar zumunci ya kareki daga sharrin masu sharri (Ameen)_

*6*

Suna fita Kanwar Mamanta wato Aunty Lami ta matso kusa da ita tare da cewa " Magajiya nikam waccan wacece?"

Ta fad'a tare da nuna inda Basira ta zauna, murmushi Magajiya tai tace "Ahhh Basira? Kema ta burgeki ne? Bansan meyasa ba amma yarinyar ta shiga raina."

Aunty Lami tai d'an shiru tana tunanin ta inda zata fara, can tace " amma dai ba matar Sarku bace ba ko?".
Had'e rai Magajiya tai tace " wace irin tambaya ce wannan? Baki ga kayan jikinta bane? Ko akwai masu sa kayan Sarki bayan matansa?"

Aunty Lami ta dafa kai, kanta na kasa tace "amma dai ba ciki ne da ita ba ko?"

Kallanta Magajiya tai cikin halin ko in kula ta girgiza kai cikin takaici sannan tace " da alama tsufa ya fara miki illa."

Lami ta d'ago ta kalli Magajiya tace " Magajiya wlh ba haka bane lalai ki binciki 'yar nan, kina me har ciki ya zauna a jikinta haka? Da alama ma cikin nan ya kai wata hudu in bai fi bama."

Kanta ta juya ba tare da ta bata amsa ba dan ta kula nema take kawai ta kona mata rai.

Lami ta kara matsowa tace " wlh Allah da gaske nake, Magajiya kinsan dai da yanda nake, indai naga mace da ciki ko wata d'aya ne sai na gane."

Tasan da wannan sarai sai dai tayaya zatace ciki bayan yarinyar haryanzu Sarki bai fara........

Tunaninta ne ya tsaya ta tuno sanda ita kanta waccan satin taga yanda tai haske har take tsokanarta akan lalai gidan sarauta ya amsheta ganin yanda take kyau haka.

Zumbur Magajiya ta mike cikin firgici ta shiga kwallama wata baiwarta kira, nan ta karaso da sauri.

Baiwar ta zube a kasa, Magajiya tace " jiku shirya zani b'angaren Basira."

Mamaki me ya kama baiwar dan tasan Magajiya bata zuwa b'angaren kowa hatta bangaren Mahaifiyar Sarki sai ta shafa watanni bata ko leka ba.

Basira kam tana dawowa daga gun Magajiya ta hau amai dan abincin dataci acan sam kawai dai ta tura ne amma bawai dan ranta yaso ba, kwanciya tai akan gado dan wani irin jiri takeji.

Mai kula da ita tana kusa da ita tana tambayarta akan ta kira mata mai magani na gidan?

Kai Basira ta jijiga zatai magana sai jin kirarin isowar Magajiya tayi ana yi a kofar ta.

Da sauri ta mike ta d'an gyara fuskarta sannan ta fito.

Magajiya ta gani a zaune tayi zama irin wanda ta saba, tun da ta taho Magajiya da Lami suka kura mata ido har kafarta ce ta hard'e ta kusa fad'uwa.

Da kyar ta karaso, Magajiya ta kalleta cikin dabara tace " ya akai? Bakyajin dadi ne?"

Kai ta girgiza alamar a'a, baiwar dake kula da ita ta matso ta zube a kasa tace " Magajiya dan Allah a kira mai bada magani ta duba Uwar gijiyata wlh ba lafiya ce ta isheta ba."

Gaban Magajiya ne yai wani wawan fad'uwa amma dayake isashiyace sai ta maze cikin gadara tace " je ki kirata."

Da sauri ta mike tai waje, Magajiya ta kalli Basira tace " na d'auke ki kamar kanwata ashe ke ba haka bane?"

KAINUWA....Where stories live. Discover now