Kainuwa.....86

6.8K 674 152
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*86*

Kansa yainta girgizawa saboda gaba d'aya hankalinsa na neman gushewa, Bilkisu idanunta ne suka kada ta taso daga inda suke sannan tazo gaban Mai Martaba ta tsugunna, tare da ajiye agoggon akan tebirin gabansa, tace " Tuba nake Ranka ya dade amma zaka iya gane agoggon nan?"

Magajiya ce tai saurin katseta tace " Bilkisu wani irin banzan tarbiyya ce wannan? Bakiga magana muke akan wannan dake gaban mu ba?" ta fada tare da nuna wannan namijin da aka rike.

Bilkisu ta kalleta sannan ta sunkuyar dakai bayan ta juyo bangaren Sarki tace " Tuba nake ranka ya dade amma dan Allah ka bani amsar tambayar nan."
A kasan ranta kuwa addu'a kawai take akan Allah yasa abin ya sakeshi kafin ta gama maganar nan, dan tana tambayar ne dan neman karin lokaci dan ya wartsake.
Magajiya zata sake magana sarki ya katseta tare da kallan agoggon yace " Agoggon menene?"
Bilkisu tace " dazu aka aiko ma Yarima akan kaine ka bada a kawo mai."
Sarki yace " ni kuma?"
Bilkisu tace " haka ne Takawa, yarinyar ta kawo akan kaine ka bada a kawoma Yarima."

Sarki ya daga agoggon sannan yace " menene dalilin aika agoggon nan da sunana bayan bani na bada ba?"
Bilkisu ta kalli magajiya kadan sannan ta kalli Turab wanda yake ta kokarin bud'e idanunsa da kyar tace " ni kaina shine abinda ban sani ba."
Magajiya tace " to yanzu menene? Abinda ya kawomu shine abinda ya kamata muyi ba wai wani zancen agoggo ba wanda bai damemu ba, da a aikamai da agoggo da kar a aika menene namu?"

Galadima yace " Takawa ni wannan mutumin nake san sanin wanene? Da matsayinsa."
Magajiya ta kalli Bilkisu tace " Gimbiya dawo ki zauna ko?"

Bilkisu ta mike tare da kallan Turab.
Sam hankalin Khadija ya kasa kwanciya ganin halin da yake ciki, idanunta duk sun ciciko da kwalla.

Basira kam gaba d'aya ta rasa ina zata sa kanta, Magajiya ta kalli mutumin tace " kai ka nutsu a gaban Sarki kake, sannan wannan da kake neman yima magana mata ce a gun Sarki ka kiyayi kanka kafin a kamaka."
Mutumin yasa dariya yace " mata?"
Galadima yace " kai! Meye tsakaninka da matar Sarki?"

Kallan Basira yai yace " Basira in sanar dasu?"

Kallansa Basira tai idanuwanta sun cika da tsoro, Abdulmajid ne ya kalli Turab ganin har yanzu ba a hayyacinsa yake ba kawai ya fara tari kamar irin ya kware din nan sosai.

Da sauri Magajiya tace a kawo ruwa.
Nan aka kawomai ruwa, da yake hannunsa ba kwari sai yai kamar irin rikewa ya kasa kawai ya juye ruwan a kan Abu Turab.

A firgice Turab ya mike tare da rike kansa.
Magajiya tace " meye hakan kuma?"
Turab ya kalleta sannan ya kalli mutumin nan, sai a yanzu maganar take kara dawo mai daya bayan d'ayan.

Lokacin shi kuma mutumin yana kara cewa " Basira in fada?"
Turab ne ya taho da sauri basu ankara ba ya kai mai naushi.

Karfinsa ya sake sosai dan har saida gefen leb'ansa ya fashe.
Dif d'akin yai da wuta saboda mamaki.
Turab ya kalleshi sannan cikin murya mai sauti yace "Ka fad'i me?"

A lokaci d'aya mutane biyar sukace Alhamdulila Turab is back (nasan kun sansu....Lol)
Magajiya kam takaici ya kamata, Turab ya kallesu sannan ya kalli mai shari'a yace " a shaida da tambaya, mutane nawa ne ba'a yarda da amsarsu?"

Kallansa yai yace " da mahaukaci da......"
Turab ya katseshi yace " wannan hankali gareshi?"
Kowa ya kalli mutumin.
Turab ya kalli Sarki yace " Takawa kayan jikinsa kawai nakeso a kalla, wannan mutumin hankali gareshi?"

KAINUWA....Where stories live. Discover now