Kainuwa....84

6.7K 587 83
                                    

.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*Gaisuwa Gareki Maman Abrar wannan shafin naki ne, Allah yabar zumunci Ameen.......*

*84*

Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli Mairo, kanta ta sadda kasa sannan tai hanyar fita.
Abdulmajid ne ya bita da kallo, sai dataje jikin kofar zata fita sannan ta juyo idanunsa na kanta dan Ji yake kamar kartaje ko ina.

Murmushi tamai sannan taja kofa tai waje Tare da rufo musu.

Tana fita ya maida kallansa gun Turab yace " Waziri fa? Ya aka kare?" dan tun jiya abin nan ke damunshi.
Turab yace " yana gida sai dai Sarki yasa an killaceshi kafin a gama shari'a."

Mairo taje zata gangara ta hango Magajiya na nufo gun.
Gefe ta matsa tare da juya baya har ta wuce, har taje zata sauka ta tafi sai kuma ta fasa.

Turab ya kalleshi yace " Magajiya ta bu'lo da wani sabon al'amari."
Abdulmajid yace " na me kenan?"

Turab zaiyi magana yaji Garzali na sanar da isowarta.
Tura kofar tai ba tare da sallama ba, dama tunda taga Garzali tasan Turab na nan.
Tana shiga ta kalleshi sannan ta kall Abdulmajid.
Murmushi Tai sannan ta karasa ciki.
Kallan Turab tai tace " kana nan ashe?"
Turab ya kalleta sai dai baiyi magana ba.
Girarta ta ja sama sannan ta kallu Abdulmajid tace " zuwa nai in maida kai gida, a kula dakai acan."
Kallanta yai yace " gida?"
Tace " eh, sannan dama inasan inma wata tambaya agaban kanin nan naka, nikam Abdulmajid tsakanin Waziri da Abu Turab wanene ya nemi halaka maka rayuwa?"

Kallan mamaki ya mata yace " ban gane me kike nufi ba?"
Tace " tsakanin Turab da yayana wanene yasa aka kamaka?"
Yace " ni ai ba........"
Katseshi tai da sauri tace "bakaji tambaya ta bace? Tsakanin Turab da Yayana wanene yasa akama ka?"
Turab ya kalla wanda daidai lokacin shima ya kalleshi.
Turab a hankali yamai wani murmushi.
Magajiya tace " kai nake jira."
Yace " Turab ne."
Wata dariya ta saki tace" kaji ko? Ina fatan kasan yanzu amsar da za'a bada a zaman da za'ai, sannan banasan wanda ya nemi kashe min d'a yazo kuma yana neman shiga jikinsa, dan haka karna kara ganinka da Abdulmajid."

Turab ya kalleta idanunsa na kanta ya taku har inda take yana tafa mata, sai dayazo daf da ita yace " Bravo! Kai gaskiya Umma u are indeed a very dangerous woman."
Da yake lokacinta ba makaranta tai ba, sai dai tsabar basira datake dashi ta tabbatar magana ce ya fada mata, tunda lokacin karatun mata ba'a wani daukeshi da wani abu ba.

Kai ta jinjina mai tace " in fadama wani sirri?"
Kallanta yai, tace " abinda kake dashi akaina ba abinda zasumun, kasan dalili? Ta matso daf dashi saitin kunnenaa tace "Saboda kai jinin mahaifinka ne, bazaka taba sanar dashi d'an dayake tunanin nashi ne ba nashi bane."
Sannan ta kalleshi tace " kasan dalili?saboda kana tsoron halin da zai shiga."

Turab kam jiyake zuciyarsa kamae zata fashe saboda takaici, daurewa yai ya kalleta yace " haka kike tunani?to in har haka kike tunani kin bada ni, domin in har irin wannan d'an karamin abun zai firgitashi to ba shakka bai dace da mulki ba."

Ya juya yai waje.

Dunkule hannunta tai ta matse a jikin zaninta, ji take kamar ta jawo yaran can ta shake shi.
Shikansa yana fita ya saku wata ajiyar zuciya sannan ya dan cije labbansa, yai gaba.

Kallan Abdulmajid tai wanda ganin yanda suke magana yasa ya runtse idanunsa saboda takaici, waje tai a zuciye Ta tambayi inda likitansa yake.

A hankali ya bud'e idanunsa, hawaye ne suka zubo mai dan ba shakka shikam yasan duk abinda ke faruwa duk saboda shi ne.

KAINUWA....Where stories live. Discover now