Kainuwa....88

5.8K 469 13
                                    

*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*Nayi mistake wancan page din zan saka 87 na kara sa 86*

*88*

Gidan ya cika taf ana ta fama zuwa gaisuwa, Turab jefi jefi yake kallan Mahaifinsa wanda yake ta amsar gaisuwa daga manya manyan mutane, bayan anyi sallar la'asar ne Sarki Ya shiga d'akinsa tare da bada umarnin a kira masa Turab.

Ya dade sosai baiyi magana ba kafin yace " wanene mahaifin Abdulmajid?"
Turab ya kalleshi a sanyaye yace " Abba!"
Sarki yai saurin cewa " su waye iyayensa?"
Turab yace " d'an gidan Waziri ne."
Kallansa Sarki yai yace " waziri?"
Turab yai kasa da kansa.
Idanu ya dan runtse kafin yace " Tun yaushe kasan maganar nan?"
Turab ya d'ago yace " sanda na fahimci abinda sukama Hajiya, daga nan ne abubuwa dayawa suka fara bayyana."

Shiru ne ya ratsa kafin Sarki yace " Allah kana ganin abinda ya sameni, kaine ka bani mulkin nan ba ni na ba kaina ba, saboda mulki an bani d'an da ba nawa ba a Matsayin nawa, sannan an halakamin matan da zasu haifar min, an kuma halakamun nawa jikin dan kar na haifa, sai dai duk da haka bazanyi fishi ba saboda ka bani wannan d'an da ke gabana, Allah ina rokanka daka karemin wannan yaran daga sharrin duk mai sharri ka kuma bashi ikon rike mulki da taimakon talakawa, ka bashi ikon yin hukunci na gaskiya ba san rai ba, ka karemin shi daga had'uwa da wanda zai nufeshi da sharri, Allah ina rokonka wannan yaran............."

Kasa karasawa yai saboda muryarsa da yaji ta fara rawa.
Duk dauriyar zuciya irin ta Turab sai da hawaye suka zubo masa,kallan Mahaifinsa yake cikin tsananin tausayawa, lalai yau Allah ne kadai yasan yanda bawan Allahn nan yake ji a ransa.
Sarki ya kalleshi yace " Abu Turab."
Nutsuwa Turab yai tare da tattara hankalinsa kan mahaifinsa dan ya fahimci magana mai mahimmanci yake san yi.
Sarki ya cigaba " zan d'auki ragowar mata na uku zamu koma can wajen gari inda nai katan gidana, inaso daga anyi sadakar uku inyi murabus in baka mulkina sannan in tattara inbar gidan nan."
Turab yace " Abba akan me zakayi murabus?"
Sarki ya girgiza kai yace " kana tunanin bayan faruwar wannan al'amarin zan iya cigaba da zama akan mulkin nan?"
" to me kayi? Duk ai laifin ba naka bane na Umma Magajiya ne."
Sarki ya girgiza kai yace " Me kakeso ince? A matsayin na sarkin garin zazzau wanda ya kasa kula da matarsa? Ko a matsayina na sarkin garin wanda matarsa tafi karfinsa?"

Turab ya motsa baki yana sanyin magana, sarki yace " na gama yanke hukuncina sannan umarnine daga Sarki bawai mahaifinka ba."
Turab yai kasa dakai.
Sarki yace " sannan Magajiya, Hisham da Matarsa, inaso kowa kamai hukunci dai dai da laifinsa, sannan kada ka kuskura ka sassautama d'aya daga cikinsu, wannan ma umarni ne."
Turab ya kalleshi yace " Matar Waziri?"
Sarki yace " kwarai, a matsayinta na uwa, akan me zata amince da abinda mijinta da kanwarsa suka tsara?banda itama tana san jininta yahau mulki?"
Turab ya had'iyi wani abu tunowa dayai mahaifiyar Khadija ce.
Sarki ya cigaba " sannan duk wanda suke da hannu akan al'amarin nan, da al'amarin Hajiya inaso ka hukunta kowa, shima umarni ne."
Turab yace " to Ranka ya dade."
Sarki yace " Abdulmajid......."
Sai kuma yai shiru dan baisan me zai ce ba, Turab ya kalleshi yace " Abba, me zai hana mu bar maganar matsayin Abdulmajid a junan mu?"
Kallansa Sarki yai yace " mene?"

Turab yace " Abba wace rayuwa Abdulmajid zaiyi in har akasan asalin abinda ya faru dashi?"
Sarki yai shiru.
Turab yace " Abba idan muka duba wannan lamari wanda akafi cuta ba kowa bane sai Abdulmajid, gaba d'aya shine aka ruguzawa rayuwa, sannan shine wanda za'afi tausayama."
Sarki yace " Abdulmajid ni kaina bazanso akan laifin da banasa ba ya shiga garari na rayuwa ba, amma kana tunanin hakan zai yiwu?"
Turab yace " a lokacin da akai maganar nan akwai mutane dayawa, sannan shi sirri duk yanda akaso da b'oyeshi in har akwai mutanen da suka sani to fa ba wani abu da za'a iya yi, ina tunanin mai zai hana tunda yanada ilimi sannan yanada babbayar hanya na matsayinsa na d'an Sarki a nemar masa aiki babba na gomnati yabar garin nan, yanda baya kusa ma balle gulma a dameshi, sannan yanada matsayin da ko asiri ya tuno ba abinda zai sameshi."

KAINUWA....Where stories live. Discover now