Kainuwa....78

6.7K 629 51
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*78*

Hankalin Hisham yayi tsananin tashi yana fita jiyai jiri na neman d'aukansa sai daya dafa bango.
Daga nesa ya hango Khadija a zaune a jikin bango tana bin mutane da kallo, tsananin tausayinta ne ya kara ratsashi, shi dai bai ga ranar da wannan buri nasa ya masa ba, ina amfani gaba d'aya ya tarwatsa rayuwar 'ya'yansa?

Kusa da ita yaje yace "Khadija "
Kallansa tai sai dai ba magana, yace " tashi muje."
Mikewa tajeyi da yake batada karfi tai kamar zata fadi, da sauri yasa hannu ya rikota yace "yi a hankali."
Hannunta ta fizge sannan tai gaba.
Kallabta yai jiki a sanyaye suka shiga mota, ya ja sukai gida.
Har suka isa ba wanda yai magana a cikin motar, tana shiga gida ta wuce d'aki ta sauko da akwatinta ta shiga had'a kayanta.
Umma ce ta shigo cikin kulawa tace "Khadija ya jikin Yari......"
Ganin tana had'a kaya yasa maganarta ta tsaya, kallanta tai tace " Khadija me kenan?"
D'agowa tai ta kalleta sai dai bazata iya cewa komai ba dan ta tabbata tana magana kuka ne zai zo mata, kurama Umma ido tai a ranta tace " me yasa kikai haka Umma? Me yasa baki hana Abba aikata munanan aiyukan nan ba?"
Kallanta Umma tai tace " Khadija lafiya?"

Khadija ta maida kanta kan kayan ta cigaba da shiryawa, ganin batada niyyar magana yasa ta fito.
Hisham ta tarar a d'aki ya baza uban tagumi, ko sallamar da tai bai amsa ba, tace " Baban Khadija me ke faruwa?"
Kallanta yai shima sororo, tace " ba shiru zakai ba me ke faruwa naga Khadija duk ta canza sannan tana ta faman hada kaya? Sannan ni bakacemin komai game da ciwon Yarima ba kadai cemib kawai bayajin dadi ne......"
Ya isheni haka nan, ki barni da abinda ke damuna dan Allah, haba! Kinsan ya nakeji a zuciyata a wannan lokacin? Komai na neman rugujewa a rayuwata, d'an da nake tunkaho zai ramamin rashin mutunci da cin zarafin da Magajiya tamib yanzu ya rikide yace shi ba wani abu tsakanina dashi, itace uwarsa, sannan Khadija ko kallona basan yi take ba ke kuma zakizo ki sani a gaba kamar wanda ya amshi bashinki?"

Umma tace " ban gane me kake nuf......"
"ba sai kin gane ba, dama ina kanki zai yi aiki? Kwakwalwace dama kamar ta kifi?"

Umma ta juya jiki a sanyaye tai waje, dakin Khadija ta koma ta tsaya kawai tana kallan ikon Allah.
Khadija kam dama tun jiya idanunta biyu taji sanda Turab yace ta koma kano, sannan dama itama bataji zata iya cigaba da zama a wannan garin, Umma ta kalla tanasan mata magana sai dai ta kasa.
Umma idanunta duk sun ciko dan itakam kalaman Hisham sun kona mata rai, inda sabi yaci ace ta saba amma duk sanda ya mata sai ta dingajin ba dadi.

Hanyar band'aki ta nufa bayan ta dau zanin wanka, ta daure tace " kano zan koma."
Ta shige ban d'akin, kallan kofar Umma tai jiki a sanyaye sannan ta mike hartaje zata shiga d'akinsu kuma ta fasa saboda takaici, juyawa tai ta koma d'akin khadija ta zauna.

**********

A bangaren Basira kuwa su Gimbiya anata kunyar suruka, Umma sosai ta yaba da hankalinta, nan tasa aka kawo mata abincin safe jin Turab yace bataci abinci ba, duk da bataso ci ba sai da Umma tasata taci, sun dade kafin Garzali ya turo a sanar da Turab akan zata fita.
Abinda kawai aka ce kenan shiyasa Basira bata fahimcesu ba, Gimbiya kuwa kallansa tai sai dai bata tambayeshi ba, ya kalleta yace " in barki anan ko in maidake can kafin in dawo?"
Tace " ina nan."
Yace " ok, ba dadewa zanyi ba."
Umma ta kallesu tai murmushin jin dadi.
Turab ya juya ya fita, Garzali ya tarar a waje yace " ta fito?"
Yace " yanzun nan."

Turab yace " muje, ka tura a sanar mai?"
Garzali yace " eh Ranka ya dade."

Mota suka shiga suka tafi asibitin, suna kallan motarta daga gaba su kuma suna baya, har suka isa.
Magajiya ta fito ta nufi d'akin da aka kwantar da Abdulmajid.
Turab yana kallanta ta shiga shikuma ya tsaya a bakin kofa.

Tana shiga aka ajiye kayayyakin data kawo, kallan danta tai cikin jin dadi ta matso tace " Abdulmajid? Idanunka biyu?"
Kallanta yai sai dai baice komai ba.
Magajiya ta zauna kusa dashi cikin jin dadi tace " na sani ai, nasan d'ana ta ina magajin sarki zai kwanta kamar bara numfashi?"

Abdulmajid ya murmusa yace " Umma kiyi hakuri na saki damuwa."
Kanta ta girgiza tace " wa ke wannan zancen? Ai farfad'owarka shine komai nawa."

Kallanta yai sannan yace " Umma kinsan Kawu yanada hannu akan abinda aka min?"
Idanu ta zaro sannan tasa hannu a kirji tace " mene?kanaso kace shiya ja maka wannan abun?"
Turab ya murmusa yace " GOOD JOB ABDUL"

Abdulmajid yai kasa dakai cikin rashin jin dadi, Magajiya tace " karka damu ba yayana ba ko Sarki ne ya kuskura ya tab'amin kai bazan taba yafemai ba."
Abdulmajid ya kalleta yace " na sani dama........"
Turo kofar da akai ne yasa shi yin shiru, Turab ne ya shigo tare da sallama.
Bata juyaba amma tanajin sallamarsa sai da gabanta ya fadi, me ya kawoshi?
Turab ya matso yana cewa "Umma ashe kin garzayo."
Juyowa tai ta kalleshi tace " Au Turab kaine?"
Yace "ni ne, kinsan dolene nazo duba Abdulmajid tunda ni aka je halakawa tsautsayi.........."
Katsesh tai da sauri cikin tsoro tace " ina amaryar? Badai barinta kai ba?"

Yace " ya zanyi? Dolece ta sani zuwa ai, naje gunki akan zamu gun Mai Martaba dan yin wata magana ashe ke kina nan?"
Idanunta ne suka fito, duk yanda taso b'oye tsoronta sai da ya nuna tace " ban gane ba?"
Turab ya matso yace " magana ce wacce ya dace ayi gani gaki ga Abdulmajid sannan ga Waziri."
A rikice ta d'ago ta kalleshi sannan ta kalli Abdulmajid tace "Turab wai kwanan nan meke damunka ne? Wuce muje gida mayi maganar a can."

Murmushi yai sannan yace " Bakyaso muyi a nan?"
Hararsa tai tace " muje ko?"
Ta na kokarin mikewa Zagi ya sanar da isowar Mai Martaba.
Kallan Turab tai dan tabbas tasan yasan da zuwansa, murmushi ya mata sannan ya d'an d'aga gira kadan ya juya kai.

Sarki ne ya fara shigowa bayansa kuma Waziri ne ya shigo.

Abdulmajid ya kalli Turab dan baisan me yake shirin aikatawa Ba.

Sarki ya nemi fadawa daau fita dan zai duba d'ansa.
Nan kowa yai waje, kallan Abdulmajid yai cikin tausayawa yace " Ya jikin naka?"
Abdulmajid ya dan sunkuyar dakai yace"Barka da war haka Takawa."

Kallansa sarki yai sannan ya kalli Turab wanda ya rusuna tare da gaidashi, Magajiya ma tace " Barkanka da war haka."
Sarki ya kalli Turab bayan ya zauna yace " me kakeyi anan kabar yar mutane ita kadai, ba kayi dubiyar ba?"
Yace " yanzu nake kokarin tafiya dama inasan zuwa gunka ne nida Umma."
Magajiya ta kalleshi sai dai kafin tai magana yace " Dama wani abu nake san......"
Katseshi magajiya tai da sauri tace "Ya kamata ka koma gida ko? Ba dadi ango daga aure ace yana waje."
Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham wanda yai tsuru tsuru yace " Magana ce akan Abdulmajid."
Yanda gaban Magajiya ya ke faduwa zata iya cewa wannan shine rana ta farko da takejin faduwar gaba haka ba kakkautawa dan tabbas tasan so yake ya sanar da tsakaninta da Abdulmajid......
Meye mafita?
Kafin kwakwalwarta tai aiki muryar Turab taji yace "Umma maganar da mukace zamuyi da Abba akan abinda ya samu Abdulmajid, ina ganin dolene ga Waziri anan wanda nake tunanin yafi kowa sanin abinda ke faruwa."

Wata irin ajiyar zuciya ta saki wanda sai da kowa ya kalleta.
Kallan Hisham tai sannan ta kalli Turab a ranta tace " tanan ka b'ulo?"
Hisham kam gaba d'aya ya rasa abinda ke mai dadi, ga Abdulmajid yace karya kuskura ya aminta akan shine sila.
Magajiya ta kalli Turab sannan ta kalli Sarki tace " haka ne Turab sai dai ina ganin abari yaji sauki tukunna kafin ai wannan maganar."

Turab ya kalleta yace " haka ne amma bakya tunanin kafin nan wanda ya aikata laifi ya kamata shima ya fuskanci, ba dai saboda zargin da akema yayanki bane yasa kike......"
Wani mugun murmushi tai tace " Kana tunanin in har Waziri nada hannu a ciki zan nemi birne laifinsa?"

Turab zaiyi magana sarki yace " ya isa haka, ina kuma tunanin tunda naji maganar na kuma sam mai ya faru yanzu dolene ayi bincike a fada, gunda alkalai suke."
Hisham! Kaine ka aikata?"
Hisham ya kalli Abdulmajid sannan ya kalli Magajiya tunowa yai da Khadija wacce ta fito da akwatinta a gida tana jira ta tafi aka aiko yazo shine yace ta jira ya dawo.

Ina zai sa kansa?
Magajiya tsoro take kar magana ta shiga fada dan tabbas in ta shiga daga bincike sai ance meye dalilinsa na aikata hakan, daga nan kuma tana tsoron kalaman da zasu fito daga bakin Hisham in yaji ana tsananta bincike a kansa.

***********


Turab ne ya kalli Magajiya wacce fuskarta yau ta bayyana da shakka karara, murmushi taga ya sakar mata a ransa yace " are u scared?"
"In kika tsorata tun yanzu the game will not be fun."
Idanun Turab kawai take kallo..........

*TURAB*

KAINUWA....Where stories live. Discover now