Kainuwa......9

6.6K 483 23
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼*

*9*

Sosai Barde ya ba Sani tukuici sannan ya kamo hanya.

Shikam Hisham tun da suka isa masauki ya kasa zaune ya kasa tsaye can ya gaji ya koma ya zauna tare da bubuga 'yatsarsa a guda d'aya a kasa alamar yana cikin dogon nazari ba shakka dolene ya d'au mataki sai dai ta ina?kuma ta yaya? Ganin yaron ma yasa hankalinsa ya kara tashi matuka, ba shakka in har Mai Martaba yaga yaran nan to fa su tasu ta kare, tunda shi jininsa ne.

In mun tafi a hanya in jefar dasu a tsakiyar daji ne? Abinda ya fara fad'o mai kenan a zuciya, kai ya girgiza da sauri yace in nai haka kuma ai zasu koma gidan a hankali tunda da kafarsu kuma zasu iya samun taimako.

Insa a je gidan a kashe su yau? Kai ya girgiza yace na tabbata in nai haka sai an zargeni tunda dai ina garin.

Idanunsa ne ya kada sosai na bakin ciki, gashi dare yayi bare ya tafo daura gun mai magani.

Ko guba zan....... Kai ya kada da sauri alamar rashin gamsuwa, idanunsa ya rufe cikin bakin ciki, jiyai daga wajen d'akin da yake wasu na hira "wlh jiya ai munga abin mamaki, tas fa wutar nan ta cinye gidan daga mata da mijin har yaranta biyu ba wanda ya tsira."

Zumbur ya mike yace wuta.....Wani murmushi ya saki na gamsuwa da shawarar data zo mai a yanzu.

Turawa yai a kiramai wani bawansa wanda ya sa aka bashi matsayi a gidan sarauta saboda tsabar yardar da yamai, bawa ne wanda baya ko tambayarsa dalili in ya saka shi abu, baya taba musa mai ba kuma ya neman sanin dalilinsa na sashi abun.

Yana zuwa ya jashi cikin kuryar d'aki ya sa bakinsa a saitin kunnensa alamar rad'a ya fara mai bayani wanda ni da nake tsaye a gun ma bansan mai ake cewa ba.

Itakam Basira da Babynta bayan Magrib suna kwance akan gado Lantana na kasa tana ninke kayan data wanke tana ta shirya musu jaka matar Yayanta ta shigo.

Basira na ganinta ta fara kokarin mikewa, da saurin tace " koma ki kwanta."

Itakam Basira mikewa tai ta zauna, kallan Lantana matar tai tace "Lantana d'an bamu guri."

Da sauri Lantana ta mike tai waje.

Kallan Basira tai sannan tace " Basira."

Yanda ta kirata yasa Basira ta tattara hankalinta gaba d'aya kanta.

Ta cigaba " Wani irin zama kukeyi da Yayar wanda yazo?"

Basira tace " zaman mutunci mukeyi."

Ido ta kura mata sannan tace " gaskiya nakeso ki fadamin."

Basira taja numfashi sannan tace " wlh da gaske nake tana kula dani nidin ce zuciyata taki yarda da ita."

Meyasa? Abinda taji ta fada kenan.
Basira tai shiru kafin can tace " gabana fad'uwa yakeyi in na ganta."

Shiru tai sannan tace " ki nutsu kiji mai zance, tun bayan zuwansu hankalina yaki kwanciya da yanda naga yayanta yana kallan yaron nan, kallo ne na tsana tsantsa."

Basira tai murmushi tace " kedai kila baki fahimceshi bane amma......"

Katseta tai da cewa " Basira zaman gidan sarauta ko ba'a fada ba kasan ba wai zama bane wanda kowa zai soka, bare ke da kika haihu, ki kasance mai hakuri sannan kar ki bari ko kad'an a cutar miki da d'anki."

KAINUWA....Where stories live. Discover now