Kainuwa.....75

6.5K 578 50
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*75*

D'akin da Abdulmajid yake ta koma, tana shiga ta taradda Mairo dake tsaye tana jikin kofa da alama nemanta take.

Yanda ta ganta yasa tasan ba a hayyacinta take ba, Mairo ta ja hannunta ta shiga da ita ciki sannan ta zubo ruwa a kofi ta mika mata, tace " naga kina bukatar kad'aicewa ni bari na wuce."
Khadija bata tanka mata ba haka kuma bata sha ruwan ba sai daj yana rike a hannunta.

Tashi tai taje kusa da Abdulmajid tana kallansa, hawayene kawai yake zubo mata, ganin kukan na neman kamata tai ban d'aki da gudu.

Tana gama kukanta ta fara wanke fuskarta, taje zata bud'e kofa ta fito taji muryar Hisham na cewa Khadija? Da alama shigowa yai nemanta, bayan kofar bandakin ta labe da sauri, shi kuma jin shiru yasa ya d'an bud'e ban daki, da yake a rikice yake bai yi tunanin zata iya b'oyewa ba, kawai sai yai tunanin bata ciki.

Juyowa yai zai fita, Magajiya ce ta shigo, ko ta kanta baiyi ba ya fara kokarin wucewa, ba abinda ta tsana irin a ganta ai kamar ba'a ganta ba, a xuciye tace " Waziri meye hakan?baka ganni bane?"
Yace "na ganki, sai dai abinda ke gabana yasa idanuna suka rufe."
Ganin yana neman fita a xuciye tace " Yaya Tsaya!"
Tsayawa yai sannan ya kalleta yace " bakiji nace idanuna sun rufe ba? Alama ce ta ba lafiya ai."
Tace " wannan ba damuwa ta bace, damuwar ka ce, sai dai inaso in sanar ma inma ka nuna baka ganni bane saboda abinda na fadama na cewa ka tabbatar kace kaine sanadin komai, kake neman yadda ni to kada ma ka soma, ka fi kowa sanin nice yar uwarka kadai a duniya nice sirrinka kuma nice reshenka."

Ran Hisham yakai makura yace " reshen da bai dade ni da komai ba sai wahala? Sanar dani me wannan reshen yamin a rayuwa?"

Magajiya tace "mene? Ni kake fadama haka yaya? Ni kake tambaya me na maka? Duk daula da jin dadin da kake zaune a ciki waye sanadi? Kana tunanin karfinka da matsayinka ne yasa?"
Cikin takaici yace " daular banza daular wofi, daular data sa 'ya'yana suka tarwatse? Daular da ta ke rinjayata nake aikata abinda bashi bane? Daular da tasani kisan kai?"

Jikin Khadija ne ya kaure da rawa, batasan sanda ta tsugunna a bandaki ba, kisan kai?
Abdulmajid kam gaba d'aya jiyai gab'obin jikinsa sun daina aiki.

Magajiya ce ta sa dariya tace " ashe kasan da wannan, na d'auka ka manta da mumuman abinda ka aikata."

Hisham fuskarsa ta canza sosai yace " kina tunanin duk abinda nake miki kyaleki nake ko dan ina tsoranki? Dama ina jurewa ne saboda d'ana, yanzu kuwa abinda nake jurewa dominsa na kwance ba lafiya, kina tunanin akwai abinda zai tsayar dani?"

Kallansa tai tace " me zaka iya yi in baka jure ba? Sanar da abinda muka aikata? In haka ne kaine a ruwa dan kai kasan ni da kaina ban taba kaahe mutum ba haka kuma bantaba sawa da bakina a kashe wani ba."

Hisham kallan tsananin mamaki kawai yake mata, yace " mene?"
Tace " ni na saka kaje kashe Turab sanda aka haifeshi?ko nice na saka ka sama gidansu wuta ka kashe yayan mahaifiyarsa da matarsa?"

Abdulmajid ji yai kansa na wani irin juyawa, yanasan yai kara yace musu khadija na bandaki sai dai inaa, wani irin juyawa kansa yakeyi wanda gaba d'aya bakinsa ma ya kasa bud'uwa.

Hisham ya sa hannayensa biyu ya shake ma Magajiya wuya, kallansa tai tace "wani kisan kake san yi? A gaban d'an ka?"

Kallan Abdulmajid yai sannan ya saketa, nuna ta yai da yatsa sai dai baice komai ba sai idanunsa da fuskarsa da suka canza sosai.

KAINUWA....Where stories live. Discover now