Kainuwa....41

6K 452 21
                                    

.🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*_Wannan Shafin sadaukarwa ce gareku Aminan arziki, BillynAbdul, Billy Badaru da Ummu Basheer Allah yabar zumunci da aminta (Ameen)_*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*41*

Yau tun safe ake hidimar yin walimar da Magajiya ta shirya, barin ma bangaren Basira wanda aketa hada hadar girke girke, katon d'akin da suke taro na lokaci zuwa lokaci tasa aka gyara, an mai kwalliya sosai, kowa an waremai gurin zamansa.

Abu Turab kam yana can gun hutawar mai martaba wanda ya saba zama, yarasa meyasa yakejin hankalinsa bai kwanta da wannan walimar ba sai dai ya rasa ta ina matsalar take, kalaman Magajiya ne suke ta mai yawo a zuciyarsa, ya tabbata akwai abinda ta shirya a wannan taron.

Ganin bashida amsa da hujjar dazai kama yasa ya mike, ya nufi bangaren Mahaifiyarsa.

Tana tsaye a kitchen tana kula da abincin da ake tayi, Mairo ma aiki take tukuru, murmushi yai na jin dadin yanda take taimakon mahaifiyarsa.

Basira ce ta juyo ta kalleshi sannan ta kalli Mairo tace " Mairo bari na shiga ciki."
Tace " To Umma" kallan Abu Turab tai tace " Yaya Ina Wuni? "
Yace " Mairo sannu da aiki."

Bata amsa ba sai murmusawa datai.
Bayan Basira yabi, Suna shiga ciki ta kalleshi tace " Dazu na tura a kiramin Mairo, sai datazo hankalina ya kwanta har nake shigowa ciki."

Kallanta yai yace " Umma kinaji da Mairo, itama haka."
Tace " Abu Turab in fadama gaskiya babban burina a duniyarnan a wannan lokacin bai wuce in ganka cikin farinciki ba, sannan banaji akwai mai saka wannan farin cikin daya wuce ta."

Kasa yai da kansa baice komai ba, ta kalleshi tace " komai da lafiya ko?"
D'agowa yai ya kalleta cikin wani yanayi yace " Umma sam hankalina ya kasa kwanciya, inaji a jikina akwai abinda zai faru a gun taron nan sai dai na rasa menene."

Kallansa tai cikin kulawa tace " Turab nasan me kake tsoro sai dai inaso ka sa aranka ba abinda zai faru in shaAllah, dana menene abin jin? Bai wuce ta zuba mana wani abun a abincin mu ba, to ninake yin abincin kaga ba wani abu da zata iya yi."

Jitai yace " shine abinda ke damuna Umma, yin girki a nan bangaren."
Kai ta girgiza tace " Abu Turab kenan, insha Allah ba abinda zai faru."

Shiru yai baice komai ba, sai dai shikam abin na damunsa menene dalilin barin mahaifiyarsa ta d'au nauyin girke girke?"
Basira ce ta katseshi tace " ka tashi kaje ka shirya nima shirya wa zanyi tunda ankusa kamala komai, sannan Mairo da Lantana suna gun."

Mikewa yai ya fito jiki a sanyaye.
Sai dayazo saitin kitchen sannan ya kalli kitchen din aiki kawai akeyi, Mairo ce ta fito tazo jikin kofa tace " Yaya lafiya?"

Yace " Mairo dan zo."
Takowa tai har zuwa inda yake, ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma taji yace " shikenan."

Kallan mamaki tamai sai dai batace komai ba, juyawa yai zai wuce sai kuma taga ya tsaya ya kalleta yace " Nagode Mairo."

Nan ma kallan mamaki tamai, sai dai bata iya cewa komai ba.
Abu Turab ya fita zuwa bangarensa.

Wanka yai sannan ya shirya cikin wata had'adan yadinsa d'inkin yamai kyau sosai, yasa hula sannan yai sallar la'asar.

Ya dade yana addu'oi kafin ya mike ya fito.
Su Garzali dama suna tsaye suna jiransa.

*************

KAINUWA....Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt