Kainuwa....39

6.4K 431 25
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*39*

Yana fita Abu Turab ya kalleta tare da daure fuska yace " Mairo, Abdulmajid d'in ne Bunsuru?"

Tace "laa yaushe nace haka yaya? Nifa zancen da nake daban."
Girman idanunsa ya rage yace " fad'amin tsakaninki dashi."
Tace " ni meye tsakanina dashi kuwa? Nema kawai yake ya takuramin da kuma san ya wulakantani."

Shiru yai sannan can yace " amma kamar yana sanki."
Dariya tad'anyi, sannan tace " kai ka yarda yaya? Wannan ne yake so na? Banaji yasan ma menene soyayya abu d'aya ya sani shi...."
Sai kuma tai shiru, kallanta yai yace " me ya sani?"
A ranta tace " neman mata mana, amma a fili tace bakomai."
Ganin batasan fada yasa yace " ki dai bishi a hankali kinsan halinsa sarai."
Baki ta tabe batace komai ba.
Ta dade sosai a asibitin dan sai da su Basira sukazo sannan suka tafi tare da ita, Zuciyar Basira fal da farincikin ganin yanda Mairo take kula da Abu Turab.

*************

Magajiya ce ta shirya tsaf tasa aka mata girke girke kala kala, kwalliya sosai tai tasa aka jera mata kaya a cikin mota, tana kokarin fitowa Khadija ta shigo.
Bayan sun gaisa Khadija tace " Umma Babba bacci ne ya d'aukeni sai dana tashi Umma tacemin kina kirana."
Magajiya ta kalleta tace " fita zanyi ki jirani inje asibiti in dawo."
Tanajin zancen asibiti tai saurin cewa " zanje Umma Babba inyaso mayi maganar a hanya."
Kallanta tai tace " ba dai san ganin Abu Turab d'in ne yasa kikesan zuwa ba ko?"
Dasauri tace "a'a Umma."
Muje.
Nan suka fito tare.
Masu kula da bangarenta ta kalla tace ku sanar da mutane tafiyata duba Turab kunsan me nake nufi ai, sukace mun gane ranki ya dade.

Tayi hakan ne dan asan abinda takaimai da kuma nunama jama'a tana san yaran.
Sun shiga mota, Magajiya ta kalli Khadija cikin yanayin bugat ciki tace " Ashe Saifullahi yazo?"
Khadija tace " eh yazo jiya."
"Yace zai dawo?"

Khadija tai shiru dan batasan me zatace ba, Magajiya ta tsuke fuska tace " Badai wulakantashi kikai ba ko?"

Khadija ta kalleta jiki a sanyaye tace " Umma ni na kasa gane dalilin had'in auran nan....."

Wani mugun kallo ta mata wanda yasa tai shiru bata iya karasa fadar abinda zata fada ba.
Magajiya tace " Khadija kina tunanin zamu cutar dake ne? Yaran nan d'an gidan manya ne sannan shi kad'ai ne namiji agun iyayensa, ga kudi ga matsayi auranku dashi zai taimaka ma Yayanki Abdulmajid zai kuma taimakeki."

Mamaki ma ya hanata magana, au wad'an nan sune dalilin dayakesa ayi aure? Matsayi?kudi?"

Magajiya ta dafata tace " na yarda dake dan haka karki bani kunya, kinfi kowa sanin Abu Turab bazai taba auranki ba ko matan duniya sun kare dan ko shi ya yarda ni da mahaifinki bazamu taba yarda ba, in ma kina tunanin wani shirme a ranki to kiyi maza ki cire wannan ki maida hankalinki kan Abu Turab."

Khadija tai kasa dakai kawai batace komai ba.

Sun isa asibiti nan aka kwashi kaya aka fara shiga dasu.
Abu Turab na kwance lokacin bacci ne ya fara d'aukansa, Garzali ne ya shigo ya sanar dashi isowar su Magajiya.

Idanunsa na rufe dama saboda dazu Galadima da Barde suka tafi.
Tashi yai ya zauna, ta shigo cikin isarta da yanayin tafiyarta, tana kallansa ta saki wani murmushi, ba shakka yaran nan dan rainin hankali ne harda wani rufe ido?
Shiga tai ta zauna, khadija tana tsaye a jikin kofa bata karaso ba.
Magajiya ta kalleta tace " dan bamu guri Khadija d'a da uwa zasuyi magana, in na gama sai ki dubashi."
To kawai tace tai waje.

Magajiya ta kalleshi tace " Turab bazaka kunce daurin ka gaida mahaifiyarka da kyau ba?"

Abu Turab yace " ai na gaidake ,sannan nida banda lafiya an min aikin ido ta ina zan ganki?"
Murmusa wa tai tace "ahhh na tuna ashe fa makaho ne wanda akamai gyaran ido."

Abu Turab yace " naji dadi da kika tuna."

Shiru sukai kafin can tace "Mahaifinka ya tura mutane yau sunkai kayan godiya da amsawar da masarautar kano ta basu na auranka."

Batajira amsarsa ba tacigaba " Kaifa kana tunanin kaci galaba ko?za kuma ka auri Bilkisu ko?"
Tad'an juya kai sannan tace " sai dai kuma inaso ka sani sai har in an gama shafa fatiha na d'aura auranku sannan zan yarda kaci galaba akan Bilkisu, abinda nazo in fadama kenan."

Murmushi ya saki yace " na d'auka kinzo ne akan mutane susan kinzo duba d'anki? Ashe zuwa kikai kimin kashedi."

Kallansa tai tace " ai dole ne uwa tazo duba danta."
Yace " hmm gaskiya kam
"

Mikewa tai tace " zan koma, ina fatan makaho ya dawo gida a matsayin cikaken ido hakan ne zaisa wasan yafi dadi, muga tsohub hannu da sabon hannu."

Kai ya jinjina yace " kuma fa hakane."
Juyawa tai tai waje.

Khadija ce ta ke kokarin shigowa yanaji Magajiya na ce mata wuce muje ba sai kin shiga ba.
Khadija tace " Umma ba dade wa zanyi ba dan Allah."

Wuce muje ko? Ko kin taba gani an duba mai lafiya?
Zata sake magana ta mata wani kalli, juyawa tai idanunta sun ciciko.

Komawa yai shima ya kwanta, tunda ta tafi jiya duk yanda yaso ya cire zancen Saif a ransa ya kasa, waye shi? Menene matsayinsa a gunta? Sai dayai yaki sosai da tunanin kafin ya samu ya kawar da shi a ransa.

Khadija kam harta shiga mota bata ce komai ba, Magajiya duk da ganin Khadija a haka yasa taji ba dadi sai dai inaaa, bazata yarda da yanda Khadija ke nuna tsantsar damuwarta akan yaron ba.

**********

Yau ya cika sati d'aya kenan da zuwan Turab Asibiti, yau ne kuma ranar da zai koma, tsaf suka shirya komai, Mai Martaba da kansa yazo dan tafiya da dansa, su Hisham da su Barde duk sunyo rakiya.

Mairo kam kusan kullum sai tazo dan Basira ma wani sa'in ita take aike, Khadija kam ba damar zuwa, tun randa suka tafi, sai dai kome take Abu Turab na ranta, kullum sai ta tashi tamai addu'a da daddare.

*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*

KAINUWA....Where stories live. Discover now