Kainuwa.....59

6.2K 460 39
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*59*

Magajiya sam ta rasa yanda zatai, ganin ba mafita yasa ta nufi gun Sarki.
Yayi mamakin jin zuwanta bayan ta shigo ta zauna sannan ta gaidashi.
Kallanta yai tare da amsawa yace " Lafiya dai ko?" ya fada tare da d'aukan ruwan dake gabansa a kofi dan sha.
Fuskarta a sake kai kace cikin farin ciki take tace " dama maganar auren Turab ne, ina tunanin ya kamata in fara had'a lefe....."
Furzo da ruwan bakinsa yai tare da kwarewa, kallanta yai cikin tsananin mamaki yace " me? Me kika ce?"
Dariya tai na salo tace " me? Kana tunanin lokaci baiyi ba?"

Ido ya kura kura mata yace "Magajiya!"
Kallansa tai bata amsa ba, yace " kinsan me kike anan kuwa? Kin tabbatar a hankalinki kike ko kuwa wani tugun muguntar kika shiryo?"

Sansanyan murmushi ta sakar mai tace " ko d'aya na dai fahimci cewa aikinane wannan, sannan waye Turab? D'anka ne fa wanda daga shi baka kara samun wani ba, ta ya za'ai yara kwaya biyu ace mun kasa kula dasu? A wata masarautar sai kaga 'ya'yan sarki sunfi 30 amma mu a namu haryanzu biyu Allah ya bamu, me zaisa mu zauna muna samun sab'ani akan su?"

Wata banzar dariya yai dan ko magajiya zata dafa Al-qur'ani bayajin zai yadda da wad'annan kalaman nata, ya tabbatar da abinda take shiryawa.
Kallanta yai yace " yanzu me ake bukata?"
Nan ta fara mai bayani, yace zai bada kudi ayi komai cikin girmamawa da matsayi.

Tana fitowa yabi bayanta da kallo yana tunani, me ke faruwa? Ya tabbata Turab ko mai zai ce mata bazata taba yarda da zancen nan ba balle ma tasan sirrin mahaifiyarsa, me zai sa ta amince? Ya tabbatar akwai wani shirri da take yi.

*********

Turab zaune agun hutawar daya saba zama ya saka ledar maganin nan a gaba a hannunsa yana kallo cilla maganin yai sama kad'an sannan ya cafe yace " kai kuma aikin me kakeyi?"
Mikewa yai dan dole ne ya binciko maganin menene wannan.
Bangarensa ya nufa, yana shiga Garzali ya taso ya gaidashi sannan ya sanar dashi nemansa da mahaifiyarsa takeyi.
Mikamai maganin yai yace " so nake ka bincikomin maganin menene wannan yanzu, sannan ya zama sirri kar ka tambaya a gidan nan, kaje wajen gari"
Garzali yace " to" sannan yai waje.

Bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, ta sa an shiryamai abinci, Turab ya zauna sannan ya gaisheta.
Kallansa tai cikin kulawa daga dawowarsa daga kano har ya d'an fada, Lantana ta kalla tace " Lantana zubamai abincin."
Turab ya kalli Lantana sannan yace " barshi zan zuba da kaina."
Nan ya jawo plate ya d'ebi fankaso guda biyu ya zuba miyar taushe wanda yaji kaza.
Hannunsa ya wanke sannan ya fara ci, sai da ya gama yasha zubo sannan ta kalleshi tace " ya kukai da Magajiyan?"
Murmushi yai mata sannan yace " karki damu Umma, sirrin nan sai dai ta tafi dashi har kabarinta badai ta sanarma wani ba."

Basira tace "me kake nufi? Kasan halin Magajiya fa?"
Yace " Nasani Umma sanin ne ma ya sani fad'in haka, sirrinki datake tunanin amfani dashi wajen hanani auren Bilkisu da kuma sa Mai Martaba yin murabus wannan sirrin ba wani abu bane akan sirrinta da nake rike dashi, ke dai kawai ki kula da lafiyar wannan shine kadai abinda nake nema daga gareki."

Kallansa tai cikin jin dadi da gamsuwa tace " maganar Mairo fa?"

Yana murmushi yace " Umman Mairo, wai ni Umma daga ni da alama ba wanda kikeso sai Mairo ko?"
Tace " Turab kenan, kasan yarinyar nan itace ta taimakeni har nakejin zaman gidan nan bai zaman min takura ba?itace ke d'ebe mana kewa daga ni har lantana, jinta nake kamar 'yata."

KAINUWA....Where stories live. Discover now