Kainuwa.....57

6.4K 487 41
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*57*

Turab na fita Magajiya ta d'auki kofin da ke gabanta ta jefi madubin dake manne a kilisar.
Mikewa tai cikin tsananin tsoro da fargaba tai cikin d'akinta.
Me ya sani? Me ya sani? Me ya sani?
Wannan kalmar ita kawai take mata yawo a kwakwalwarta gaba daya ta rasa inda zatasa kansa, fitowa tai ta bada umarnin a kira mata Jakadiya cikin gaggawa.
Jakadiya na zaune tasa kwanan abinci agaba sam ta kasa ci akazo aka sanar da ita kiran Magajiya.
Zufa ce ta shiga karyo mata, mikewa tai ta fito.
Haka ta karasa tana ta tsoron abinda zai faru.
Magajiya na zaune a kan gadonta yayi shiru tare da kurama kasa ido.
Ko sallamar Jakadiya bata amsa ba, har Jakadiyar ta zauna tare da gaisheta.
Magajiya bata amsa ba sai dai ta kalleta cikin wani yanayi na zargi, sai kuma ta murmusa tace " Jakadiya ba tin yau ba nasan tabbas sai gulna da tsautsau bakinki yasa kin sanar ma Turab sirrin Abdulmajid."
Jakadiya ta zaro ido sannan ta tuno kalaman Turab a yayin da ya mike zai fita bayan ya gama mata fada " Kada ki kuskura ki nunama Magajiya munyi maganar nan dake, duk yanda taso ta bugi cikinki ki tabbatar baki bar wata hanya ba dazai sa ta fahimta, nagode da sanar dani da kikai."
Ya juya ya fita, tunowa datai da kalamansa yasa tai saurin zubewa tace " Gimbiya Magajiya ta yaya zakimin wannan shaidar? Bayan shekaru sama da ashirin ina rike da wannan sirrin? Sai yanzu ne zan tona? Inci ribar me?"
Magajiya ta kalleta tace " Amma ai kwanaki kin min birga akan sirrina da kike rike dashi sannan banida tabbas ke d'in yanzu a bangarena kike duba da abinda kikamin."
Magajiya ta daure tace " Gimbiya bani bace, me nene ma zaisa in fadamai?"
Ganin yanda Jakadiya tai yasa ta gamsu akan ba ita bace, ta kalleta tace " bani guri."
Fita Jakadiya tai, tana zuwa waje ta saki wani ajiyar zuciya.
Magajiya kam tana fita ta dafa kanga cikin tashin hankalu tace " ba wannan bane, tunda duk gidan Jakadiya ce kawai tasan wannan sirrin, tunowa tai da Hajiya, ba dai Hajiya ce ta fad'i dayan sirrin ba?"
Mikewa tai da sauri ta fito, ta sanar ma Bayinta akan zuwa bangaren Hajiya.

Tana shiga wannan baiwar ta taho gunta da gudu ta gaisheta.
Magajiya ta kalleta bata amsa mata ba tai ciki.
Mai kuka da ita wacce tafi kusanci da Magajiya ce ta kalli Baiwar tace " kina zubawa?"
Cikin tsoro tace eh, dan bazata iya cewa ta batar da maganin ba dan ta tabbata inhar ta fada to lalai kwananta ya kare.
Magajiya na shiga ciki ta rufe kofa.
Kallan d'akin tai a wulakance sannan ta toshe haccinta wai wari.
Zama tai daga nesa da Hajiya sannan ta kalleta cikin jin dadin yanda take shan jiki ba damar magana tace " Hajiya? Kin ganeni?"

Kallanta Hajiya tai, tana ganin Magajiya ta shiga yunkuri tanasan magana ta kuma kasa, Magajiya tace " Lalai Hajiya kiji da jikinki har kike wani yunkurin magana? Da nadauka ko kinsamu sauki ne harkinyi tsautsayin yin magana amma yanzu naga ba haka ba, bakya tunanin ya kamata ki sallama komai na duniya ki jira mutuwa tazo ta daukeki?"

Hajiya yunkuri take sosai, ganin ba dama yasa tai shiru sai hawaye da yake ziraro mata ta gefen ido, tunowa tai da abinda ta gani.

{
" Wasika aka ba da akawo mata tashin safiyar yau, amsar wasikar tai ta bud'e, kana kallan rubutun kaga rubutu ne na 'yan koyo, sai dai da yake bata iya karantawa ba yasa ta ajiye wasikar a tunaninta ba mai amfani bace.
Sai dai me? Kwana hudu kenan ana aiko mata da wannan wasikar sannan yaro ne yake kawowa kuma daga ya bada yake sa gudu yai waje, yau abin ya fara damunga dan da alama magana mai mahimmanci ake san sanar da ita.
Sawa tai a kira mata Rabi'a, bayan tazo sun gama gaisawa ta d'auko wasikar ta bata tace " Karantamin."
Rabi'a ta amsa tare da bud'e wa.
Na farko an rubuta "Hajiya d'anki na cikin matsala."
Na biyu " Hajiya ki yafemin sai dai ba yanda zanyi dolene na cigaba da zuba maganin nan inba haka ba Magajiya halakani zatai."
Na uku "Hajiya ki taimaken ki d'au mataki ko na samu zunubina ya tsaya anan."
Na hudu " Hajiya kiyi wani abu dan Allah."

Hajiya ta amshi takardar a taorace tace "Rabi'a kin tabbatar da abinda aka rubuta kenan?"
Rabi'a tace "Hajiya wlh abinda akace kenan amma me hakan yake nufi? Magajiya tana ba sarki magani? Akan me?"

Hajiya tace " jeki gida sannan maganar nan ta zama sirri tsakaninmu koda wani abu zai sameni kimin alkawarin bazaki taba fadan wata kalma ba."
Rabi'a tace "Na miki alkawari, nan ta mata sallama ta fita da tsananin mamaki, bazata taba iya ma Hajiya musu ba."

Tana fita Hajiya ta kona takardar sannan tai shiru tana tunani, ba wanda ta yarda dashi bare suyi maganar dashi, sannan batasan wacece tayo mata wasikar ba, gashi ita ta tsufa ba wani abu da zata iya yi.

Abu d'aya ne ya dace tai shine taje gun Magajiya dan nuna mata ba tsoronta ake ba sannan ga fadamata inhar bata daina ba zata sanarma Sarki.

Yau da safe tasa aka kira mata Magajiya, tun safe aka sanar da ita amma sai yamma liss sannan tazo.
Hajiya na zaune da charbi, zama tai akan kujera sannan tace" Hajiya kim wuni lafiya?"
Hajiya cikin takaici ta kalleta tace " me kike bawa d'ana?"
Magajiya ta kalleta cikin mamaki tace "me nake ba d'anki kamar ya kenan?"
Hajiya tace "Kamar yanda kikaji haka yake, wani tuggun kike dubgawa Abdussamad, nasan dai ba maganin mutuwa kike bashi ba tunda zamansa a mulki shine zamanki kema a mulki, sanar dani me kike masa?"
Dama Magajiya na tsananin jin haushin Hajiya dan tunda aka aureta tasan ba santa takeyi ba, fuska ta canza ta d'aure fuska tace " koma me nake bashi ai mijinane sannan bakida ikon shiga tsakanin mata da miji."
Ta mike zata fita, Hajiga abin ya bata mamaki tace " waye ya haifa miki har kika aura? Sannan ni dama tunda na fara ganinki wlh nasan ke ba alheri bace a gareshi ba kuma matar zama bace ta amana, ko kiyi gaggawar daina abinda kike bashi ko kuma wlh in sanar dashi, zakiyi mamaki inkika ganki a gidan yayanki da takardar saki, ba'a saki a gidan sarauta bari sakin uwargida wacce take sarauniya sai dai ina sanar miki za'a fara akanki."

Wata banzan dariya Magajiya tai tace " Me? Ni za'a saka?"
Hajiya ta kalleta sai dai yanda taga Magajiya tayi yasa tsoro ya d'arsu mata dana sani ya kamata me yasa bata fadama d'anta ba ta sanar ma Magajiya?"

Magajiya tazo kusa da ita ta sakar mata murmushi tace " ina jiran lokacin da za'a bani takarda, ki kuma tabbatar an bani, sannan maganar magani maganin hana d'aukan ciki ne ki tabbatar kin sanar dashi haka."
Ta juya ta fita, tana kallan Hajiya duk ta rikice jikinta ya d'auki rawa.
Bayan Magrib tanashan ruwa shikenan ta kasance ba lafiya tun daga wannan rana har yau ba baki ba zama bare tafiya."
}

Magajiya ta mike tazo saitin kunnen Hajiya tace " Kijira d'ana ya hau mulki in har kinada rai ni zan taimaka a fitar dake daga gidanan akaiki can bayan gari ki zauna kyafi jin dadin zaman duniyar, in kuma kinaso in hada da jikanki da kuma uwarsa Basira ku zauna tare acan."
Ta mike tai waje.
Tsayuwa tai a wajen gidan, me turab ya sani? Bataji akwai wanni babban sirri dazai tsoratata da ya wuce wad'an nan biyu, sauran duk sai dai tasa a aikata amma badai ita dakanta ba, inma zancen kashe yayan Basira ne ai ba ita bace tai Hisham ne.

Dolene ta nemi Turab ta kuma bihi cikinsa da jin sirrin da ya sani.

Turab zauna akan kujera yana d'an kada dan yatsansa d'aya tunani yakeyi wace hanya ce mafi sauki da kuma bakin ciki da zai sa Magajiya ta fita hayyacinta in taji Yayanta Hisham yaci amanar ta? Ya tabbata Hisham da Magajiya kowa amfani yake da dan uwansa.
Ita tana amfani dashi dan cikar burinta, shi kuma yana amfani da ita dan samun matsayin da zai wuceta nan gaba, murmushi yai yace " Badai tana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki komai na burinta ya cika ba?"

Mikewa yai ya fito waje.
Hango Abdulmajid yai a zaune yana shan iska jiyai tausayinsa ya dan darsu mai, ya zaiji in yaji wannan sirrin? Yauce rana ta farko dayaji tausayin Abdulmajid ya kamashi.

Ya zaiyi ya sa Magajiya da Hisham su tunama junansu asiri da kansu?
Khadija!
Shiru yai jin sunan daya zo mai, tabbas itace a tsakanin mutanen biyu, ita da Abdulmajid, sai dai me? Zuciyarsa zata iya jure amfani da ita?

Juyawa yai ya koma ciki tare da furzar da iska mai zafi.......

*TURAB*

KAINUWA....Where stories live. Discover now