Kainuwa...56

7K 526 54
                                    

*KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*56*

Turab na zaune a cikin mota yai shiru yana tunani, me ya samu Khadija?

A can kuwa Hisham na shiga da ita cikin gida ya rike hannayenta duka biyu yace "Khadija, menene? Me kikaji?"
Kallansa tai tsananin tsoronsa taji ya shigeta, kai ta girgiza batace komai ba, kara jijiga ta yai yace " wanene ni?"
A hankali tace " Abba ne."
Yace " me kike kokarin sanar ma Abu Turab?"
Kai ta girgiza da sauri tace "bakomai."
Idanu ya kankance yana san gano abunda take b'oyewa, mahaifiyarta ce tazo gun tace " Khadija? Lafiya inata kiranki shiru?"
Kwace hannunta tai ta tafi gun Uwarta da gudu.
Hisham cikin zargi ya ke kallanta, Ummanta ta riketa tace "lafiya Khadija?"
Tattaro nutsuwarta tai sannan ta samun kanta da cewa " Bakomai Umma faduwa nai a waje."
Umma ta kama hannunta cikin kulawa sukai ciki.
Hisham ya bisu da kallon zargi sai dai bashida tabbas akan abinda yake zargi, sannan yasan Khadija da ace taji maganar da sukai da matarsa dazu da ciki zata shigo taji me suke nufi bawai waje zatai ba.

*****
Sun isa gida, Turab ya fito sannan ya nufi hanyar b'angarensa.
Abdulmajid ya hango yana tahowa shima da alama shima fita zaiyi, tsaya wai cak yana kallansa sannan yana maimaita kalamun Jakadiya, da kuma Khadija, da alama duk maganarsu a karkashinta dai maganace wacce ta shafi Abdulmajid, to amma me suke nufi? Sam hankalinsa bai kawo ba d'an sarki bane dan shi a ganinsa duk mugunta da makircin magajiya bazata taba tunanin yin wani abu mai kama da haka ba.

Abdulmajid ne ya iso inda yake kallan banza yamai yai gaba abinsa.
Turab ya bishi da kallo sannan yai gaba.

Har ya je zai shiga b'angarensa sai ya juya ya nufi bangaren Hajiya.
Yaje shiga yai kicibis damai kula da ita, sam bata san ya taho ba haka shima.
Bigetan dayai ne kufin dake hannunta ya fad'i kasa.

Turab ya kalleta yace " sannu....."
Ganin yanda ta shiga saurin dauke kofin da tayar sam tama manta da bigeta akai, tana d'aukewa tai hanhar fita, kasa ya tsuguna ya d'au yar karamar ledar data fad'o daga jikinta yana kokarin mata magana akan ta yarda abu sai gani yai ba kowa agun.
Mamaki ya kamashi ina tai? Kallan maganin yai sannan ya shinshina maganin, a aljihunsa ya saka sannan ya shiga ciki.
Sam jikinta ba sauki sai ma karuwa da yakeyi, kusa da ita yaje sannan ya riko hannunta yace " Hajiya nine Abu Turab."
A hankali ta bud'e idanunta ta kalleshi cikin karfin hali ta sakarmai murmushi.
Cikin kulawa da tausayawa yace" Hajiya kinganni shiru ko? Tafiya nai sannan abubuwa sunyi yawa dana dawo, ya jikin?"
Idanu ta lumshe sannan ta bud'e, kallan d'aki yai sannan yace " kin gaji da kwanciya ko?."

Tunani tai yanzu ne lokacin daya kamata ta yunkura ta fadama Turab abinda ta sani.
Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana, kallanta yai yace " akwai abinda kikesan fad'amin?"
Kai ta d'aga da sauri alamar eh.
Matsowa yai da kansa kusa da bakinta yace "menene Hajiya?abu kikeso?"

Daurewa take sosai da kyar ta iya cewa "Maga...."
Yace "magani?"
Kai ta girgiza alamar a'a yace "Magajiya?"
Kai ta d'aga da sauri alamar eh.
Cikin mamaki ya kalleta yace " wani abun ta miki?"

Da kyar ta kara daurewa tace "Abb duu........"
Yace " Abdulmajid?"
Kai ta jijiga alamar a'a yai shiru yana tunani can a ransa yace Abdussamad?
Kallanta yai yace " Abba?"
Kai ta girgiza da sauri yace " me ya faru?"
Kokarin magana take sai dai ina ta kasa, ganin yanda take shan wahala yasa yace " Hajiya daina magana."

Yawo ne yashiga zubowa mai kumfa, cikin tausayawa ya mike da sauri yana neman mai kula da ita.
Yarinyar nan ya gani a waje tana ta dube dube cikin b'acin rai yace "bakiji ina kiranki ba?"
Tahowa tai gunsa, yace " Hajiya jikinta ya motsa nemo mai magani."
Ya fada tare da komawa ciki ya d'agata yana goge mata, sai far fari take da idanunta, mai bada magani tana zuwa ta shiga mata jike jike tana bata, sai dayaga ta samu bacci sannan ya mike cikin tausaya mata.

KAINUWA....Where stories live. Discover now