Kainuwa....74

6.9K 578 64
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*74*

Turab gidan Umma ya wuce inda take, yana isa ya tadda ta shiryamai abinci, nan yaci sannan ya kwanta akan kujerar falo.
Fitowa tai daga d'aki ta kalleshi tace " Turab meye hakan? Ta ya zakaci abinci ka kwanta?"
Mikewa zaune yai yace "Wlh Umma kaina kemin ciwo."
Zama tai gefensa tace " Ba dole kanka yai ciwo ba, tun da ka tafi d'aurin aure har yanzu banaji ka samu isasshen hutu na awa biyu cikake, ni na kasa gane me kake tayi a waje haka, gashi ni kace in zauna anan."
Turab ya kalli falon sannan yace "Umma ni dama ki dawo nan da zama."
Kallansa tai tace "akwai abinda kake b'oyemin ko?"
Turab yai kasa dakai yace " Ni Umma haryanzu Abba bai fad'amiki inda Hajiya dasu Lantana suke ba?"

Umma tace " Bai fad'amin ba, sai dai inaji kamar fa har yanzu jikin Hajiya ba sauki."
Turab yace "dama nayi tunanin haka, dan da ta warke da ta sanar dashi wani abu."
Basira ta kalleshi tace " me kenan?"
Kai Turab ya girgiza sannan yace " In kawo miki masu aiki daga can? Naga waccan kamar aikin zai mata yawa."

Tace " karka damu, ni ma zaman haka kawai damuna yakeyi, yanzu kai haka zaka zauna har a kawo Amaryar?"
Turab yace " name?"
Tace " ko ma dai menene, ka samu ka huta sosai kafin suzo, kar suzo suganka a haka."
Murmushi yai yace " a haka kamar ya?"
Tace " oho dai nidai na fad'ama in ba so kake su juya da ita suce dama Ashe Angon ba shida jini a jika."

Dariya ya saka sosai, yace " lalai Umma, kawai kice kinaso in huta amma wannan sharhin babu shi."
Tace " haka kace?"
Yace " hmm, ni kam Umma akwai abinda nakesan sanar dake."
Tace " name kenan?"
Yace " Umma so nake idan komai ya kammala in d'aukeki da Bilkisu muje kauyen da na taso."

Umma ta kalleshi cikin jin dadi, tace " Ni kaina inasan zuwa sai dai ina tunanin me zance ma Sarki."
Yace " ki jira in gama abinda nakeyi, sannan ki kara min addu'a akan Allah ya bani ikon gurfanar da masu laifi, ya kuma kareni daga sharrinsu, sannan karya bani ikon cutar da wasu saboda wani buri nawa."

Basira cikin kulawa take kallansa tace " Insha Allahu Allah na tare dakai, sannan muma bazamu daina maka addu'a ba."
Haka sukai ta dan hira sama sama kafin daga baya ya kwanta.

Bacci sosai ne ya d'aukeshi wanda shi kansa bai san jikinshi ya gaji haka ba.

Bai tashi ba sai karfe biyu na rana.

*********

A can gida kuwa Magajiya ce zaune a kuryar d'aki ita da Hisham ta kalleshi tace " Yaya Yaran can yasan komai."
Hisham yace " name kenan?"
Magajiya tace " yasan Abdulmajid ba d'ana bane."

Hisham yai kasa dakai wato shiyasa ya ce mai haka? Sanda ya koreshi daga asibiti?"
Magajiya ta kalli Hisham tace " yaya duk yanda za'ai inaso ka tabbatar baka bari an san nice na sa a kama Turab ba, inaso ka yarda akan kaine kai komai, ni zan san yanda zanyi karyai magana akan Abdulmajid."

Tsananin mamaki ne ya kama Hisham ya kalleta yace " ban gane ba?"
Tace " inaso ka ce kaine kasa a kama Turab in Sarki ya tambayeka, ni zansan yanda zanyi kar a hukuntaka."

Tsananin mamaki yama hanashi magana sai kallanta kawaj da yakeyi.
Magajiya tace " Sannan inaso a maida Khadija Kano, duk sauran matsalar daga baya ni zan san yanda zanyi, kai dai kai wannan abun guda biyu."

Ta mike ba tare da ta jira amsarsa ba tace " bari naje na kara shiryawa asibiti zan koma, dan bazan iya barin D'ana a can ba."

Hisham yabi bayanta kawai da kallo Baki a bud'e.

KAINUWA....Where stories live. Discover now