Kainuwa....3

7.7K 572 14
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


_Dan Allah wanda yamin magana ban mai reply ba yai hakuri jiya whatsapp d'ina ya samu matsala sai dana sake downloading sai dai sam yaki backup name messages d'ina_

*Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂*

*3*

Kafin su fito daga masallaci bayan an daura auren mutane har sun cika gaban masallacin, labari har ya kai musu cewa ga wani gara can da baisan me yakeyi ba ya auri Basira.

Sarki na kokarin fitowa wannan Bawan nasa ya sha gabansa ya rusuna tare da sanar dashi halin da ake ciki.

Jikin Amadu ne yai mugun sanyi, jiyai Abdulsamad yace " Ku fara fita in yaso ni sai in fito daga baya."

Amadu yace " ai mai martaba bakasan gidan ba."

Yace ba komai zan biyo ku a baya ne nima ai.

Jin hakan yasa suka fara fita, nan fa mutane suka saki baki suna kallan bawan, kowa da gulmar dake fada aransa, wasu cewa suke ai dole ya nemo ko ma waye ya bata da kuma alama ma fakiri ne, wasu kuma suce da alama sadaka aka bashi yaji banza shi yasa bazai iya bari ba.

Haka dai kowa da abinda yake tunani, sudai sukai gaba, Mai Martaba na baya cikin mutane yana kuma jin duk abinda kowa ke fada, jikinsa ne yai mugun sanyi lalai ba shakka yayi babban taimakon na auran yarinyar nan dan kuwa da alama ba mai auranta a garin nan.

Sai da mutane sukaga sun isa gida sannan kowa ya watse, shi kuma Sarki Abdulsamad ya shiga ciki.

Bayan sun zauna ne matar Amadu ta kawo musu fura mai sanyi tare da dambu na tsakin massara yasha gyada, Abdulsamad ya dan ci kad'an kafin ya kalli Amadu yace " Amadu ba zan kai Basira gidana ba yanzu."

Gaban Amadu ne ya fadi yace " kana dana sani ko? Na auranta? Ni kai........"

Katseshi Abdulsamad yai yace " ina tsorace mata a bubuwa guda uku shiyasa bazan kaita yanzu ba."

Yadan ja numfashi na manyan mutane kafin yace " in har taje gidan nan a haka zatasha bakar wahala ba tare kuma da sanina ba, ko Magajiya bazata barta haka ba, ganin jiya akai sunan d'anta ace yau na kawo mata? Sannan na saki yarinya jiya ashe wani nake san sakeyi? Sannan ban sanar dasu zanyi auren ba ma sam.
Kaga wad'annan dalilan sune zai sa su wahalar da Basira, gata ita kuma ko harkar gidan sarauta bata sani ba bare ta nemi kwatar kanta."

Shiru Amadu yai kafin yace " Gaskiya ne ni kaga sam banyi wannan nazarin ba nidai dadina Basira ta auri wanda nasan ko bani da rai zai kular min da ita."

Sarki ya d'an murmusa kadan kafin yace " Zan maka kwatancen gidana dake cikin gari, zan kuma sanar ma ma'aikatan gidan in yaso kai zuwa gobe sai ka taho da ita ka kaita can, zan tura mata bayin da zasu dinga kula da ita da koya mata abubuwan daya dace, in yaso zuwa ko sati biyu ne sai ta dawo."

Amadu ya shiga godiya, nan Sarki ya mike yace zai wuce.

Amadu ya shiga kwallama Basira kira, da sauri Sarki yace " ya isa haka, bance ka kirata ba ai, ina sauri ne in tazo naje na ganta."

Amadu ya amsa da to, sannan yamai sallama yai waje.

Yana fita ita kuma matar Amadu wacce ta taso Basira da kyar tanata sharar baccinta suka fito, ganin ba kowa a gun yasa tace " Malam ina mijin?"

Basira ya kalla yace " Basira gobe zan kaiki shi yayi gaba."

Matar tace " a ina aka tabayin haka? Yaya shine zai kai yarinya?"

KAINUWA....Where stories live. Discover now