Kainuwa.....66

7.4K 554 78
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼*

_Haly(Mom Farhan) Allah ya kara lafiya yasa kaffara ne....Wish u quick recovery_

*66*

Abu Turab idanunsa ya bud'e a hankali ya shiga kallan d'akinsa kafin a hankali ya furzar da wata yar karamar iska daga bakinsa.
Sannan yasa hannu ya dafa gadon ya mike ya zauna, idanunsa ya rufe ya shiga karanto addu'oin safiya, kafin ya sauko daga kan gado.

Yau saura sati 3 bikinsa, dayake gidan maza ne ba wani abu special ake aikatawa ba, an dai kammala ginin bangaren da zasu zauna da gimbiya.

Saukowa yai daga kan gadon sannan ya nufi bandaki dan kama ruwa da yin alwala.

Bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yai ta tilawar al-qur'ani har sai da gari yai haske, wannan al'adar haka yake yinta dan koyar wace ta ma'aiki S.A.W.
Sai wajen karfe goma yaci abincin safe sannan ya fito.
B'angaren Mahaifiyarsa yaje sukai 'yar hira kafin ya fito.
Yana kokarin komawa bangarensa ya hango Baiwar da take kula da bangaren Abdulmajid wanda ya shine ya sakata a bangaren dan kawomai rahoto akan Hisham.
Karasowa tai cikin hanzari sannan ta gaisheshi, tana yi tana kalle kalle.
Turab ya kalleta yace " lafiya da safen nan?"
Tace "banga d'an aike bane, dama Waziri ne ya zo yanzun nan, sannan rike yake da lefa katuwa, da ya shiga ciki na amshi laidar sai naga kula ce sannan ga kamshin abinci nan."
Turab yace " yayi kyau, koma bakin aikin ki."
Tace "Yarima Abdulmajid ya......"
Dakatar da ita yai yace " na tambayeki rayuwar Abdulmajid? Ko kuwa a sanda na baki aikin nan nace ki dinga kawon zancensa? A iya sanina ce miki nai kawai in Waziri yazo ki sanar dani."
Tace " Tuba nake ranka ya dade."

Turab ya sallameta sannan shikuma ya shiga ciki.
A bakin kofa ya tadda Garzali da alama fita zaiyi.
Turab ya kalleshi yace " in zaka fita ka biya bangaren Sarki gub Jakadiya."
Garzali ya kalleshi yace " Jakadiya?"
Turab yace " ka sanar da ita Hisham na bangaren Abdulmajid."
Garzali cikin rashin fahimta yace " to." dan bazai iya tambayarsa dakili ba.

Garzali ya garzaya yaba Jakadiya sako.
Ita kanta kallab Garzalin tai tace " abinda yace kawai ka fadamin kenan?"
"iya kacinsa kenan."
Ya juya.

Jakadiya tai shiru tana kara maimaita kalmar kafin daga baya ta fito.
Bangaren Magajiya ta nufa, Magajiya na karyawa ta shigo.
Sama sama ta amsa gaisuwarta tanayi kamar bataso.
Sannan tace " me ya kawoki?"
Jakadiya ta miko mata leda tace " maganine aka kawo na gyaran fata."
Magajiya ta kalli maganin dake cikin farar leda sannan ta kalleta tace " ni ce miki akai ko wani kare da doki ya bani magani amsa nake?"

Jakadiya tace "badai haryanzu baki hakura ba?haba Hajiya Magajiya, matar sarki, uwar sarki, kakar sarki."

Magajiya ta wani juya kai sannan tace " Me ya kawo ki? Dan na tabbata ba wannan bane kadai abinda ya kawoki."
Jakadiya ta dan shafi fuska sannan ta matso tace " hmm dama na kasa fahimtar wani abu ne, Na rasa me yasa nake ganin Waziri yanzu yana zirya bangaren yarima Abdulmajid."
Magajiya ta kalleta tace " ban gane ba.."
Jakadiya tace " Tuba nake Ranki ya dade amma nifa hankali ya kasa kwanciya da zuwansa."

Ruwan da ta gama sha ragowar cikin kofun tai kamar zata zubo mata har ta rufe idonta ta d'auka ita zata zuba ma.
Magajiya ta ajiye cup din sannan ta kalleta tace " najiki inaso kuma ki fita."
Jakadiya ta had'iyi yawu sannan ta mike tai waje.
Magajiya tai shiru tana tunani, dama kwanaki Turab ya sanar da ita ya ganshi amma shi ha musa, sannan an fada mata rannan an ganshi, sannan yau Jakadiya ta fada mata, me Hisham yake tunani? Tamai magana akan kai Khadija Kano ma ya mata burus sannan yanzu ya fara kewayewa yana zuwa gun D'anta?

KAINUWA....Where stories live. Discover now