Kainuwa....60

6.4K 493 23
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*60*

Abdulmajid ya kara kallan Magajiya yace " Umma wai meke faruwa?"
Tsawa yaji ta dakamai tace " Fita ka bani guri."
Tsananin mamaki ne ma ya hanashi d'auke ido daga kanta, me yai? Yauce ranar daya tabaji tamai tsawa haka balle ma akan wani Abu Turab?
Mikewa yai rai a b'ace yai waje.
Ko bi ta kansa batai ba ta sa kafa tayi ball da wannan kofin, mikewa tai ta nufi falonta.

Turab kam number Bilkisu ya danna, ta dade kafin a d'aga, gaisheshi akai sannan akace wanene?"
Turab yace " Ina Gimbiya?"
Daga can akace bari a sanar mata, waz'ace?" yace "Abu Turab."
Da sauri mai maganar ta gaisheshi sannan ta ajiye kan wayar a gefe tai cikin d'aki da sauri.
Gimbiya na Kwance rike da wani littafi tana karantawa.
Bayan yarinyar ta nemi izini ta shigo ta tsugunna sannan tace "Gimbiya, yarima ne ya kira waya."

Mikewa tai zaune da sauri tace " Turab?"
Yarinyar tace " eh Gimbiya."

Da sauri ta juya zata sauko, sai kuma ta koma ta zauna tace jekinkice ina zuwa.
Yarinyar ta amsa da to sannan ta mike.

Bilkisu sai da ta d'an dade a zaune sannan ta sauko a hankali ta fito.

Sallamar duk masu kula da ita wad'anda ke falon tai sannan ta d'auki wayar, cikin kasalaliyar murya tace " Barkanka da Warhaka."
Turab wanda yasan dolene ya jira saboda mulki, yai murmushi sannan yace " na d'au lokaci kafin na kira Gimbiya, ina fatan za'amin afuwa."

"Hmmm za'a duba uzurunka sai a maka."
Turab ya kalli kofa dan yasan tabbas Magagiya zata leko dan ganin me yake yi.
Gefen fuskarsa ya d'am shafa sannan yace " Abubuwa ne wad'anda nikaina banyi tsamanni ba suka dinga bulbulowa wad'anda suka rike tunanina."
Tace " Hmm yanzu fa? Ka warware komai?"
Yai shiru, hakan yasa tace " Karka damu nasan zaka iya, koma menene, kardai kacemin baka yarda da kanka ba?"

Turab ya kalle gefen kofa inda ya hango inuwar Magajiya, yiyai kamar bai ganta ba, murmushi yai sannan ya gyara zamansa irin mai jin shaukin nan yace " Kuma fa haka ne, ya kamata in zama mutum na farko mai yadda da kansa."
Tace " A koda yaushe ka dinga tunawa ina tare da kai akan komai, duk da ayanzu bazan iya taimaka maka ba, bazan kuma iya kula da kai ba sai dai inaso kasa a ranka akwai wacce take tare da kai a koda yaushe."

Har zuwarshi sai da yaji wani sanyi ba shakka Bilkisu macece wacce ta san kanta ya tabbata zasu zauna lafiya, sannan yana ji a jikinsa ita alheri ce a gareshi.
Jiyai tace " kayi shiru? Ba dai kalamai na......"
Katseta yai da sauri yace " wannan layin nawa ne bance ki fada ba."
Tace " layin me?"
Yace " Kalamanki sun ratsani na kuma ji dadi, ba haka zaki ce ba?"

Bata san sanda tai dariya ba, tace " mene? Haka nace ma?"
Yace " sosai ma."
Gani inuwar Magajiya yai ta juya.
Fuska ta rufe kamar yana ganinta, Turab yace " zan kiraki zuwa ko zuwa anjima ko zuwa gobe."
Tace " Karka damu dani, yanzu ma da mukai magana ya isa, duk sanda ka samu sarari ka kirani."
Yace " Nagode, ki gaida Munnira."
Bai jira ta amsa da to ba ma ya ajiye kan wayar sannan ya mike.

Magajiya kam ta gama kuluwa da alama ma soyayya suke da yarinyar, itakam duk duniya ba wanda ta tsana yanzu irin wannan dan banzan yaran, ko ganinsa batasan yi, wai kamar ita ace ta zauna yaro yana raina mata hankali? Dolene ta nemi abinda zatai amfani dashi ko da yake ai ta shirya da auransa hmmm tai kwafa tace a ranar aure ka zai kasance jana'izar ka.
Ta na kokarin shiga d'akinta yace " Umma me kike anan?"

Juyowa tai fuskarta a had'e sai kuma ta saki fuska tace " Na d'auka ka tafi ai, ashe kana ciki?"

Turab yace " na d'auka zakizo ku gaisa da sirikarki, ko zaki koma in kira miki ita?"
Idanunta ne suka canza har fuskarta sai data nuna bacin ranta, daurewa tai ta saki yake tace " Meye abin azarbabi bayan nice shugabar kai lefe?"

Kai ya jinjina sannan ya dawo gabanta, fuskarsa a hade tare da kallanta.
Kallansa tai tace " ya akai kuma?"

Wani banzan murmushi yai yace " maganinki da kika sa a dinga sama Hajiya ina tunanin sai kinsa a nemo wani."

Idanunta ne sukai rawa alamar mara gaskiya tace " me kake fada?"
Yace " ba abinda nake fada ina dai sanar dakeni duk wanda ya maida Hajiya haka wallahi wannan rantsuwa ce nai bazan taba kyaleshi ba, sai na sa anmai hukunci daidai da abinda ya aikata, ko da kuwa Umma tace Basira ta aikata hakan, duk da nasan bazata taba zalintar d'an adam ba kamar wasu."

Magajiya ta kalleshi sannan ta saki wanj banzan murmushi na rainin hankali tace " Ko nima zan tayaka d'aukan hukuncin, sai dai ka tabbatar kana da karfi na hukunta mai laifin? Ba wai karfi na jiki nake nufi ba."
Turab ya kalli kwayar idanunta yace " Ahhh to wa ya sani?" sannan ya murmusa yace " kece kika sa aka fara game d'in, sai dai ni nake da ikon tsayar dashi, sannan inaso ki tabbatar idanunki na nan a bud'e har sanda zan tsayar da wasan, zakiga inda mara karfi yake kaskantar da masu karfi."

Magajiya tama kasa magana kallansa kawai takeyi.
Turab ya juya ya fara tafiya, har yayi nisa ya juyo yace " Ahh ki gaida Khadija banaji zan iya zuwa yau ba, ko da yake bata sani ba."

Kallansa tai cikin takaici tace " Kana tunanin ita Khadijan yarda zatai dakai?"

Wata dariya ya saki yace " Khadijan? Kin tabbatar Khadijan da kika sani kike fad'a? Ahh Umma ya zakiyi? Dan Khadija ba sai na tambayeta ba dan nasan abinda ke ranta."
Ya juya.
Jiyai tace " Lalai na yarda yarinta na damunka kanka kuma na rawa, ya zakayi to? Dan kuwa an kusa sa ranarta da Saifullahi."

Bai san me yasa ba amma sai dayaji wani abu ya taba zuciyarsa.
Sai da ya daure ya juyo fuskarsa d'auke da murmushin da yake iya lab'ansa yace " ai mace sai anyi aurenta an shafa fatiha ake tabbatar da mijinta."
Ya juya ya fita.

Agogon dake manne a bangon gun tasa hannu ta fizgo sannan ta bugashi a kasa, kanta ta dafe sannan ta shiga d'akinta, da karfi ta bugo kofar.
Ji take kamar ta saki kara.

**********

Turab na fita ya dafe kansa, ba shakka matarnan bala'ice, wacce mutum zai dinga neman tsari da ita (irinsu sai a karshe zakaji suna cewa sharrin shaid'an ne)

Khadija ya hango daga nesa, tafe take kamar mara laka a jiki, da alama batajin dadi.
Me ya sameta?
Juyawa yai da sauri dan bama yasan zuciyarsa ta nemi yin rawa saboda ita.

Ganin ya juya zai wuce yasa ta tsaya cak, idanunta ne suka ciciko dan taga da alama goje mata yake sanyi, ita kanta bataso shigowa ba sai dai dolene ta fadama Magajiya akan bazata auri Saif ba, ita dai su barta ta karashi rayuwarta a haka, inta tunan mumunan abunda suka aikata ji take baxata iya kallan wata zuri'ar da sunan mutum na gari ba.

Ko me ya tuna sai kuma ya juyo, kallan kallo sukayi daga nesa.
Juyawa yai a hankali ya fara tafiya.

Bata san tana binsa ta baya ba, ji take ganinsa kamar yanasa taji abinda ke tokare a ranta na raguwa.

Yasan tana binsa sai dai ya rasa dalilinsa na nuna mata bai sani ba, sannan ya rasa dalilinsa nayin tafiya a hankali cikin saibi.
Har ya isa bangaren Hajiya.
Yarinyar nan ya gani tana shara, kallanta yai yace " ajiye tsintsiyar ki kuma biyoni."

Gabanta ne ya fadi ta kalleshi tace "Yarima laifi nai?"

Wani mugun kallo ya mata, da sauri tai kasa da kai tace "Tuba nake Yarima."
Ajiye tsintsiyar tai tabi bayansa.

B'angaren sa ya nufa da ita, suna shiga cikin falo ya d'aga hannu cikin zafin rai zai kai mata mari, idanunta ta runtse dan ta gama sadaukarwa.

Saura kiris ya mareta sai kuma ya tsaya cikin tsananin b'acin rai.

A hankali ta bud'e idanunta ta tsugunna da sauri tace " Tuba nake ranka ya dade."

*TURAB*

KAINUWA....Where stories live. Discover now